Maris
Asabar, 1 ga Maris
Sa zuciyar nan ba za ta zama abin banza ba ko kaɗan.—Rom. 5:5.
Gaskiya ne cewa sabuwar duniya ba ta zo ba tukuna. Amma ku yi laꞌakari da abubuwan da muke gani yanzu, wato taurari, da bishiyoyi, da dabbobi da kuma mutane. Babu wanda zai yi shakkar cewa akwai abubuwan nan. Ko da yake akwai lokacin da babu su. Yanzu muna ganin su ne domin Jehobah ya halicce su. (Far. 1:1, 26, 27) Haka ma, Allah ya yi alkawari cewa zai yi sabuwar duniya. Zai cika wannan alkawarin. A sabuwar duniya, mutane za su yi rayuwa har abada cikin ƙoshin lafiya. Idan lokacin Jehobah ya yi, za mu ga sabuwar duniyar kuma za ta zama kamar abubuwan da muke gani a yau. (Isha. 65:17; R. Yar. 21:3, 4) Kafin lokacin, ka yi amfani da duk zarafin da kake da shi don ka ƙarfafa bangaskiyarka. Ka daɗa nuna godiya don fansar Yesu Kristi. Ka riƙa tunani a kan ikon Jehobah. Ka shagala a ayyukan ibada. Idan ka yi abubuwan nan, za ka zama ɗaya daga cikin waɗanda “suka yi haƙuri har suka karɓi abin da Allah ya yi alkawari zai ba su.”—Ibran. 6:11, 12. w23.04 31 sakin layi na 18-19
Lahadi, 2 ga Maris
Ba na riga na gaya miki cewa idan kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah ba?—Yoh. 11:40.
Yesu ya ɗaga idanunsa sama kuma ya yi adduꞌa a gaban jamaꞌa. Ya yi hakan ne domin yana so a yabi Jehobah. Sai Yesu ya ce: “Liꞌazaru, fito!” (John 11:43) Sai Liꞌazaru ya fito daga kabarin! Yesu ya yi abin da wasu suke ganin ba zai taɓa yiwuwa ba. Wannan labarin ya ƙara tabbatar mana cewa za a ta da matattu. Ta yaya? Ka tuna da alkawarin da Yesu ya yi wa Marta, ya ce: “Ɗanꞌuwanki zai tashi.” (Yoh. 11:23) Kamar Ubansa, Yesu yana da niyya da kuma ikon cika wannan alkawarin. Hawaye da Yesu ya yi, ya nuna cewa yana marmarin kawo ƙarshen mutuwa da kuma matsaloli da hakan ya jawo. Kuma yadda Liꞌazaru ya fito daga kabarin ƙarin tabbaci ne cewa Yesu yana da ikon ta da matattu. Ƙari ga haka, ka yi tunani a kan tunasarwa da Yesu ya yi wa Marta, wanda aka ambata a nassin yini na yau. Muna da dalilai masu kyau na gaskata cewa alkawarin da Allah ya yi game da tashin matattu zai cika. w23.04 11-12 sakin layi na 15-16
Litinin, 3 ga Maris
Yahweh yana kurkusa ga masu kira gare shi, ga waɗanda suke kira gare shi cikin gaskiya.—Zab. 145:18.
Idan muka fahimci nufin Jehobah da kyau, wataƙila hakan zai sa mu canja abin da muka roƙa. Ya kamata mu tuna cewa Jehobah yana da lokacin da ya adana da zai cika nufinsa. Ɗaya daga cikin nufin Jehobah shi ne ya cire dukan matsalolin da muke fuskanta a yau, kuma hakan ya ƙunshi balaꞌoꞌi, da cututtuka da kuma mutuwa. Jehobah zai yi amfani da Mulkinsa don ya cim ma hakan. (Dan. 2:44; R. Yar. 21:3, 4) Amma kafin lokacin ya zo, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya mulki duniyar nan. (Yoh. 12:31; R. Yar. 12:9) Idan Jehobah yana magance matsalolin da ꞌyan Adam suke fuskanta a yau, abin zai yi kamar Shaiɗan ne yake nasara a mulkinsa. Ko da yake muna bukatar mu jira Jehobah ya cika wasu alkawuransa, Jehobah bai bar mu haka ba, yana taimaka mana ko a yanzu ma. w23.05 8 sakin layi na 4; 9-10 sakin layi na 7-8
Talata, 4 ga Maris
Ku san irin amsar da ya yi kyau ku ba kowa.—Kol. 4:6.
Ta yaya za mu taimaka wa mutane su ma su amfana daga Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? Hanya ta farko ita ce, mu gayyace su. Ya kamata mu gayyaci mutane idan muka fita waꞌazi. Ban da haka, zai dace mu rubuta sunayen wasu da za mu so mu gayyata. Za mu iya haɗa da sunayen danginmu da abokan aikinmu da abokan makarantarmu da dai sauransu. Ko da ba mu da littafin gayyata da aka buga da yawa, za mu iya tura wa mutum mahaɗi, wato link, don ya iya duba gayyatar da naꞌurarsa. Idan muka yi hakan, mai yiwuwa za mu yi mamakin yawan mutane da za su zo taron. (M. Wa. 11:6) Ka tuna cewa idan ka gayyaci mutum zuwa taron nan, mai yiwuwa zai so ya yi maka wasu tambayoyi, musamman idan bai taɓa zuwa taronmu ba. Don haka, zai dace mu yi tunanin tambayoyin da za su iya yi mana da amsar da za mu ba su. Ko waɗanda suka zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu ma, za su iya yi mana wasu tambayoyi. Hakika, kafin ranar taron, a lokacin taron, da kuma bayan taron, zai dace mu yi duk wani abin da za mu iya don mu taimaka wa masu “zuciya ta samun rai na har abada” su amfana daga wannan taron.—A. M. 13:48, NWT. w24.01 12 sakin layi na 13, 15; 13 sakin layi na 16
Laraba, 5 ga Maris
Shin, wane irin abu ne ranku? Ai, abu ne kamar hazo wanda yake bayyana a ɗan lokaci saꞌan nan ya ɓace.—Yak. 4:14.
Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mutane takwas da aka ta da su a nan duniya. Me zai hana ka yin nazari mai zurfi a kan kowanne ɗayansu? Yayin da kake yin hakan, ka nemi darasi da za ka iya koya daga labarin. Ka yi tunani a kan yadda kowanne ɗaya daga cikin labaran ya nuna yadda Allah yake da niyya da kuma ikon ta da matattu. Ka yi tunani a kan tashin matattu mafi muhimmanci, wato na Yesu. Ka tuna cewa akwai ɗaruruwan mutane da suka shaida tashin Yesu daga mutuwa, kuma hakan ya ba mu dalili mai kyau na gaskatawa da alkawarin tashin matattu. (1 Kor. 15:3-6, 20-22) Muna godiya sosai ga Jehobah domin alkawarin da ya yi mana cewa zai ta da matattu! Za mu iya kasance da tabbaci cewa alkawarin nan zai cika domin Jehobah yana da niyya da kuma ikon cika alkawarin. Bari mu ƙudiri niyyar ci-gaba da gaskata da alkawarin tashin matattu. Ta hakan, za mu ƙara kusantar Allah wanda ya yi mana alkawari cewa, ‘Ƙaunatattunku za su tashi!’—Yoh. 11:23. w23.04 8 sakin layi na 2; 12 sakin layi na 17; 13 sakin layi na 20
Alhamis, 6 ga Maris
Ka yi tafiyarka da Allahnka cikin sauƙin kai.—Mik. 6:8.
Za mu nuna cewa mun san kasawarmu idan ba mu da girman kai kuma muka san cewa ba kome ne za mu iya yi ba. Za mu kuma nuna cewa mu masu tawaliꞌu ne idan muna girmama mutane kuma muna ɗaukansu da muhimmanci fiye da kanmu. (Filib. 2:3) Halaye biyun nan kusan ɗaya suke. Mutum mai tawaliꞌu yakan san cewa yana da kasawa. Gideyon mutum ne mai tawaliꞌu wanda ya san kasawarsa. Midiyanawa suna da ƙarfin gaske. Da malaꞌikan Jehobah ya gaya wa Gideyon cewa shi aka zaɓa ya ceci Israꞌilawa daga hannunsu, Gideyon ya ce: “Dangina marar ƙarfi ne a cikin zuriyar Manasse, ni ne kuma mafi ƙanƙanta a cikin gidanmu.” (Alƙa. 6:15) A tunaninsa, ba zai iya yin aikin ba, amma Jehobah ya san cewa zai iya. Da taimakon Jehobah, Gideyon ya kuwa cika aikin nan da aka ba shi. Dattawa suna iya ƙoƙarinsu su nuna halin sauƙin kai da kuma tawaliꞌu a kome da suke yi. (A. M. 20:18, 19) Ba sa takama da baiwarsu ko abubuwan da suka cim ma. Kuma ba sa ganin cewa ba su da amfani don kurakuren da suka taɓa yi. w23.06 3 sakin layi na 4-5
Jumma’a, 7 ga Maris
Zai murƙushe kanka.—Far. 3:15.
Kafin zuriyar ya murƙushe kan Shaiɗan, zai ɗauki fiye da shekaru dubu daga yanzu. (R. Yar. 20:7-10) Amma kafin hakan a faru, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana wasu abubuwa masu muhimmanci da za su faru. Da farko, ƙasashe za su yi shelar “zaman lafiya da salama!” (1 Tas. 5:2, 3) “Sai kawai” a soma ƙunci mai girma. Ƙuncin zai soma da harin da ƙasashen duniya za su kai wa addinan ƙarya. (R. Yar. 17:16) Bayan haka, Yesu zai yi shariꞌa, kuma zai ware awaki daga tumaki. (Mat. 25:31-33, 46) A wannan lokacin, Shaiɗan ba zai yi zaman kashe wando ba, zai ci-gaba da yin gāba da Jehobah domin ya tsani bayin Jehobah sosai. Zai zuga haɗin gwiwar ƙasashe da Littafi Mai Tsarki ya kira Gog na ƙasar Magog su kai wa bayin Jehobah hari. (Ezek. 38:2, 10, 11) A yayin da ake ƙunci mai girma, za a tattara dukan shafaffun Kiristoci zuwa sama domin su haɗa kai da Yesu da malaꞌikunsa su yi yaƙi a Armageddon. Hakan zai kawo ƙarshen ƙunci mai girma. (Mat. 24:31; R. Yar. 16:14, 16) Bayan haka, Yesu zai soma yin sarauta a duniya na shekara dubu.—R. Yar. 20:6. w23.10 20-21 sakin layi na 9-10
Asabar, 8 ga Maris
Ni mai tsoron Yahweh ne tun ina yaro.—1 Sar. 18:12.
A yau, akwai mutane da yawa da suke zama a ƙasashen da gwamnati ta hana aikinmu. Suna daraja waɗanda suke mulki, amma kamar Obadiya, sun ƙi su daina bauta ma Jehobah. (Mat. 22:21) Sun nuna cewa suna tsoron Allah ta yadda suke yi masa biyayya fiye da mutum. (A. M. 5:29) Suna hakan ta wurin ci gaba da yin waꞌazi da kuma yin taro a ɓoye. (Mat. 10:16, 28) Kuma suna yin iya ƙoƙarinsu wajen samar wa ꞌyanꞌuwansu abubuwa da za su sa su ci gaba da yin kusa da Jehobah. Alal misali, akwai wani ɗanꞌuwa mai suna Henri daga wata ƙasa a Afirka inda gwamnati ta taɓa hana aikinmu. A lokacin, Ɗanꞌuwa Henri ya yarda a dinga aikan sa yana kai wa ꞌyanꞌuwa littattafanmu. Ya ce: “Ni mai kunya ne sosai. . . . Jehobah . . . ne ya sa na iya yin ƙarfin zuciya.” Kai ma za ka iya yin ƙarfin zuciya kamar Henri? Tabbas za ka iya, idan kana tsoron Jehobah. w23.06 16 sakin layi na 9, 11
Lahadi, 9 ga Maris
Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya.—Rom. 5:12.
Da Adamu da Hauwaꞌu suka yi tawaye, abin ya zama kamar duniyar nan ba za ta taɓa cika da kamiltattun mutane masu biyayya kamar yadda Jehobah ya nufa ba. Amma Shaiɗan ya hana Jehobah cika nufinsa ne? Mai yiwuwa Shaiɗan ya zata Jehobah zai kasa cika alkawarinsa. Wataƙila ma ya zata cewa Jehobah zai kashe Adamu da Hauwaꞌu kuma ya halicci wasu mutane don su cika duniya. Da hakan zai sa Allah ya cika nufinsa. Sai dai kuma Shaiɗan zai ce, Allah ya yi ƙarya. Me ya sa? Domin kamar yadda Farawa 1:28 ta ce, Jehobah ya gaya wa Adamu da Hauwaꞌu cewa ꞌyaꞌyansu ne za su cika duniya. Mai yiwuwa kuma Shaiɗan ya ɗauka cewa Jehobah zai bar Adamu da Hauwaꞌu su haifi ꞌyaꞌya amma ꞌyaꞌyan ba za su taɓa zama kamiltattu ba. (M. Wa. 7:20; Rom. 3:23) Idan hakan ya faru, ba shakka Shaiɗan zai yi wa Jehobah dariya don ya kasa cika nufinsa. Me ya sa? Domin ba za a samu kamiltattun ꞌyaꞌyan Adamu da za su cika duniya kuma su mai da ita aljanna kamar yadda Allah ya nufa ba. w23.11 6 sakin layi na 15-16
Litinin, 10 ga Maris
Kada ku wuce abin da aka rubuta.—1 Kor. 4:6.
Jehobah yakan gaya mana abin da yake so mu yi dalla-dalla, ta wurin Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa. Bai kamata mu ƙara gishiri a kan umurninsa ba, ko kaɗan. (K. Mag. 3:5-7) Don haka, ba za mu wuce abin da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki ba, ko mu kafa ma ꞌyanꞌuwa dokoki a kan abin da Jehobah bai ce ba. Shaiɗan yana amfani da “yaudarar wofi” da kuma “alꞌadun duniyar nan” don ya ruɗi mutane kuma ya raba kansu. (Kol. 2:8, Mai Makamantu[n] Ayoyi) A ƙarni na farko, waɗannan alꞌadun sun haɗa da ilimin duniya da ke bisa ga raꞌayin mutane da kuma koyarwar mutane da ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. Da raꞌayin nan cewa dole ne Kiristoci su bi dokar Musa. Dukan abubuwan nan yaudara ne domin sun ɗauke hankalin mutane, sun hana su mai da hankali ga Jehobah, wanda shi ne Tushen hikima ta gaske. A yau, Shaiɗan yana amfani da kafofin yaɗa labarai da na sada zumunta don ya yaɗa jita-jita da kuma labaran ƙarya da shugabannin gwamnati suke ƙullawa. w23.07 16 sakin layi na 11-12
Talata, 11 ga Maris
Ya Yahweh, ina misalin girman ayyukanka? Tunaninka da zurfi suke ƙwarai!—Zab. 92:5.
Ba shakka, yadda Jehobah ya warware wannan matsalar ya ba Shaiɗan mamaki. Jehobah ya bar Adamu da Hauwaꞌu su haifi ꞌyaꞌya. Ta hakan, ya cika alkawarin da ya yi musu kuma ya nuna cewa ba ya ƙarya. Jehobah ya nuna cewa in har ya ce zai yi wani abu, ba abin da ya isa ya hana shi. Ya buɗe hanyar cika nufinsa ta wurin tanadar da wani zuriya wanda zai ceci ꞌyaꞌyan Adamu da Hauwaꞌu masu aminci. Wannan zuriyar zai ba da ransa don ya ceci ꞌyan Adam. (Far. 3:15; 22:18) Hakika, hakan ya ba Shaiɗan mamaki. Me ya sa? Domin ƙauna da rashin son kai ne suka sa Jehobah da Yesu suka yi tanadin wannan fansar. (Mat. 20:28; Yoh. 3:16) Shaiɗan ba haka yake ba, shi mai son kai ne. Wane amfani ne wannan fansar za ta kawo? A ƙarshen Sarautar Yesu na Shekara Dubu, ꞌyaꞌyan Adamu da Hauwaꞌu kamiltattu masu biyayya su ne za su kasance a duniyar nan, kuma za su mai da ita aljanna kamar yadda Jehobah ya so tun farko. w23.11 6 sakin layi na 17
Laraba, 12 ga Maris
Allah zai hukunta.—Ibran. 13:4.
Mu bi dokar Jehobah game da rai da jini. Me ya sa bai kamata mu yi wasa da jini ba? Domin Jehobah ya ce jini yana wakiltar rai, wanda kyauta ne mai daraja da ya ba mu. (L. Fir. 17:14) Da Jehobah ya ba wa mutane izini su ci dabbobi, ya ce kada su ci jinin. (Far. 9:4) Ya sa an ambata hakan a dokar da ya ba wa Israꞌilawa ta hannun Musa. (L. Fir. 17:10) Ya kuma umurci hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko su gaya wa dukan Kiristoci su ‘kiyaye kansu daga . . . jini.’ (A. M. 15:28, 29) Muna bin wannan dokar sosai idan muna zaɓan irin jinyar da za a yi mana. Mu kuma guji yin lalata, kamar yadda Jehobah ya umurta. Manzo Bulus ya shawarce mu cewa mu “kashe halin shaꞌawace-shaꞌawacen duniya,” wato mu yi duk wani abin da ya kamata don mu guji halaye marasa kyau. Don haka, za mu guji kallo ko kuma yin duk wani abin da zai kai ga yin lalata.—Kol. 3:5; Ayu. 31:1. w23.07 15 sakin layi na 5-6
Alhamis, 13 ga Maris
A ƙarshe, . . . ya faɗa mata asirinsa duka.—Alƙa. 16:17.
Mai yiwuwa son da Samson yake yi wa Delila ne ya sa ya kasa ganin makircin da take ƙullawa. Ko ma mene ne ya sa, mun dai san cewa Delila ta yi ta matsa masa ya gaya mata sirrin ƙarfinsa, har sai da ya gaya mata. Abin baƙin ciki, Samson ya sa kansa a cikin yanayin da ƙarshenta, ya rasa ƙarfinsa kuma ya ɓata wa Jehobah rai. (Alƙa. 16:16-20) Samson ya sha wuya sosai domin ya yarda da Delila maimakon ya dogara ga Jehobah. Filistiyawa sun kama shi kuma sun ƙwaƙule masa idanu. Sun sa shi a kurkuku a birnin Gaza. A wurin, sun mai da shi bawa mai yi musu niƙa. A-kwana-a-tashi, sai suka kawo shi inda suke yin wani biki, suka yi hadaya ga allahnsu mai suna Dagon, don suna ganin shi ne ya sa suka iya kama Samson. Sai suka kawo shi daga kurkuku “ya yi musu wasa” don su yi masa dariya.—Alƙa. 16:21-25. w23.09 5-6 sakin layi na 13-14
Jumma’a, 14 ga Maris
Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne.—Rom. 12:17.
Ƙila abokin aikinmu ko ɗan makarantarmu ya tambaye mu wani abu game da imaninmu. Idan hakan ya faru, zai dace mu yi iya ƙoƙarinmu mu kāre imaninmu, amma mu daraja mutumin. (1 Bit. 3:15) Mu yi amfani da tambaya don mu san abin da yake a zuciyarsa. Ko da mene ne ya sa mutum ya tā da wani batu, zai dace mu amsa masa cikin natsuwa kuma da alheri. Idan muka amsa masa da kyau, hakan zai iya sa ya canja raꞌayinsa. Misali, idan wani abokin aikinmu ya tambaye mu abin da ya sa ba ma bikin zagayowar ranar haifuwa (birthday), ka dakata ka yi tunani. Shin, mutumin yana ganin kamar ba a barin mu mu yi wani abin jin daɗi gabaki ɗaya ne? Mai yiwuwa abin da kawai yake bukata shi ne mu gode masa don yadda ya nuna cewa ya damu da abokan aikinsa. Ƙila hakan zai sa hankalinsa ya kwanta, kuma ya so jin abin da za mu gaya masa daga Littafi Mai Tsarki game da bikin ranar haifuwa. w23.09 17 sakin layi na 10-11
Asabar, 15 ga Maris
Ku lura domin kada koyarwar ƙarya ta masu mugunta ta kwashi hankalinku, har ku faɗi daga tabbatacciyar tsayawarku.—2 Bit. 3:17.
Muna da babbar damar yi wa dukan mutane waꞌazi. Manzo Bitrus ya ce mu yi “marmarin zuwan” ranar Jehobah. (2 Bit. 3:11, 12) Ta yaya za mu yi hakan? A kowace rana, za mu iya yin tunanin abubuwa masu ban shaꞌawa da za su faru a sabuwar duniya. Ka yi tunanin yadda za ka ji idan kana shaƙar iska mai tsabta, kana cin abinci mai gina jiki, kana marabtar waɗanda kake ƙauna da aka ta da su daga mutuwa, kuma kana koya wa mutanen da suka yi rayuwa a dā yadda annabcin Littafi Mai Tsarki ya cika. Idan kana irin wannan tunanin, zai taimake ka ka ci-gaba da yin marmarin zuwan ranar, kuma ba za ka yi shakkar cewa ƙarshen ya yi kusa ba. Idan ‘mun riga mun san da waɗannan’ abubuwa, masu koyarwar ƙarya ba za su ‘kwashi hankalinmu’ ba. w23.09 27 sakin layi na 5-6
Lahadi, 16 ga Maris
Saboda Ubangiji ku yi wa iyayenku biyayya, domin wannan shi ne daidai.—Afis. 6:1.
Matasa da yawa a yau, “marasa biyayya ga iyayensu” ne, kuma hakan zai iya shafan matasan da suke bauta wa Jehobah. (2 Tim. 3:1, 2) Amma me ya sa suke rashin biyayya? Wasu suna ganin iyayensu munafukai ne, domin iyayen ba sa yin abin da suke gaya musu. Wasu kuma suna ganin abin da iyayensu suke gaya musu tsohon yayi ne, don haka, ba shi da amfani, ko kuma yana takura musu. Idan kai matashi ne, ka taɓa jin hakan? Yana yi wa matasa da yawa wuya su bi umurnin Jehobah da ke nassin yini na yau. Mene ne zai taimaka maka ka yi hakan? Yesu ne ya fi kafa misali mai kyau a wannan batun, kuma za ka iya yin koyi da shi. (1 Bit. 2:21-24) Shi ba ya kuskure, amma iyayensa ajizai ne. Duk da haka, Yesu ya daraja iyayensa ko a lokacin da suka yi kuskure ko ba su fahimce shi ba.—Fit. 20:12. w23.10 7 sakin layi na 4-5
Litinin, 17 ga Maris
An kawar da Koyarwar ta dā a gefe ke nan saboda rashin ikonta da rashin amfaninta.—Ibran. 7:18.
Manzo Bulus ya bayyana musu cewa hadayun da Dokar ta ce su riƙa yi ba za su iya wanke zunubansu gabaki ɗaya ba. Saboda haka, an ajiye wannan Dokar a “gefe.” Sai Bulus ya soma koya musu wasu abubuwa masu wuyar fahimta. Ya tuna wa ꞌyanꞌuwan wata mafita mafi kyau da Allah ya shirya ta wurin hadayar Yesu Kristi, kuma wannan shi ne zai taimaka musu su yi “kusa da Allah.” (Ibran. 7:19) Bulus ya bayyana musu yadda ibadar da suke yi yanzu ya fi ibadar da suke yi a dā. Ayyukan ibada da Yahudawa suke yi bisa ga Dokar Musu “kamar hoto ne kawai na abin da zai zo, amma Almasihu shi ne ainihin abin.” (Kol. 2:17) Hoton abu ba shi ne ainihin abin ba. Haka ma ayyukan ibada da Yahudawa suke yi yana wakiltar abubuwan da za su faru a nan gaba ne. Muna bukatar mu fahimci shirye-shiryen da Jehobah ya yi mana don a gafarta mana zunubanmu. Hakan zai sa mu iya bauta masa yadda yake so. w23.10 25 sakin layi na 4-5
Talata, 18 ga Maris
A kwanakin ƙarshe kuma sarkin kudu za ya yi kokuwa da shi: sarkin arewa kuma za ya tasa masa da gāba kamar guguwa.—Dan. 11:40, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
Littafin Daniyel sura 11 ta yi zancen sarakuna ko kuma masu mulki guda biyu da suka yi ta kokuwa da juna a kan mulkin duniya. Da muka gwada abin da ke annabcin nan da sauran annabce-annabcen da ke Littafi Mai Tsarki, mun ga cewa a yau Rasha da ƙasashen da ke goyon bayanta su ne “sarkin arewa,” saꞌan nan Mulkin Burtaniya da Amurka shi ne “sarkin kudu.” “Sarkin arewa” yana tsananta wa mutanen Allah da suke a ƙarƙashinsa sosai. An yi ma wasu Shaidun Jehobah dūka kuma an kai su kurkuku saboda imaninsu. Amma maimakon tsanantawa da sarkin yake musu ta sa ꞌyanꞌuwanmu su ja da baya, ta ma ƙara musu bangaskiya ne. Me ya sa? Domin ꞌyanꞌuwanmu sun san cewa wannan tsanantawa da ake yi wa mutanen Allah yana cika annabcin da Daniyel ya yi ne. (Dan. 11:41) Mu ma idan muka san hakan, zai ƙara ba mu bege kuma zai sa mu ƙudiri niyyar riƙe amincinmu. w23.08 11 sakin layi na 15-16
Laraba, 19 ga Maris
Duk wanda ya taɓa mutanena ya taɓa ƙwayar idona ne.—Zak. 2:8.
Saboda ƙaunar da Jehobah yake yi mana, da zarar wani abu ya same mu, shi ma yakan ji shi a ransa kuma yana so ya kāre mu. Shi ya sa kowannenmu zai iya roƙon Jehobah cewa: ‘Ka kiyaye ni kamar ƙwayar idonka.’ (Zab. 17:8) Ƙwayar ido yana saurin jin zafi, kuma ba ma wasa da shi. Don haka, da Jehobah ya ce mu kamar ƙwayar idonsa ne, yana nufin cewa, duk wanda ya taɓa mu ya taɓa abin da Jehobah ba ya wasa da shi. Jehobah yana so ka san cewa yana ƙaunar ka. Amma ya san cewa wani lokaci saboda abin da ya taɓa faruwa da mu, za mu iya ganin kamar ba zai iya ƙaunar mu ba. Mai yiwuwa kuma, kana cikin wani hali a yanzu da ke sa ya yi maka wuya ka gaskata cewa Jehobah yana ƙaunar ka. Me zai taimaka maka? Wani abin da zai tabbatar maka cewa Jehobah yana ƙaunar ka shi ne idan ka ga yadda Jehobah ya bayyana ƙaunarsa ga Yesu, da shafaffun Kiristoci da kuma dukanmu. w24.01 27 sakin layi na 6-7
Alhamis, 20 ga Maris
Hannun Allahnmu yana tare da mu, ya kuma cece mu daga hannun abokan gābanmu.—Ezra 8:31.
Ezra ya ga yadda Jehobah ya taimaka wa mutanensa saꞌad da suke fuskantar matsaloli. Da alama Ezra yana Babila a shekara ta 484 kafin haihuwar Yesu saꞌad da Sarki Ahasuerus ya ba da umurni cewa a kashe dukan Yahudawa da ke Daular Fashiya. (Esta 3:7, 13-15) Hakan ya sa ran Ezra da sauran Yahudawan cikin haɗari. Da suka ji game da umurnin, sun damu sosai har suka kasa cin abinci. Sun yi kuka kuma sun roƙi Jehobah ya taimaka musu. (Esta 4:3) Ka yi tunanin yadda Ezra da ꞌyanꞌuwansa Yahudawa suka ji saꞌad da aka kashe waɗanda suke so su kakkashe Yahudawan. (Esta 9:1, 2) Abin da ya faru da Ezra a wannan mawuyacin yanayin, ya ba shi ƙarfin fuskantar matsalolin da za su taso daga baya, kuma ba mamaki hakan ya ƙara tabbatar masa cewa Jehobah zai iya kāre bayinsa. w23.11 17 sakin layi na 12-13
Jumma’a, 21 ga Maris
Allah ya ce da shi mai adalci, ba ta dalilin ayyukan da . . . ya yi ba.—Rom. 4:6.
Manzo Bulus yana magana ne game da “ayyukan Koyarwar Musa,” wato dokar da aka ba wa Musa a Dutsen Sinai. (Rom. 3:21, 28) A zamanin Bulus, wasu Kiristoci Yahudawa suna ganin cewa suna bukatar su ci-gaba da bin Dokar Musa. Saboda haka, Bulus ya yi amfani da misalin Ibrahim don ya nuna cewa ba dole ne mutum ya bi “ayyukan Koyarwar Musa” kafin Allah ya yarda da shi ba. A maimako, bangaskiya ce muke bukata. Sanin wannan yana da ban ƙarfafa, don ya nuna cewa za mu iya samun dangantaka mai kyau da Allah. Idan muka ba da gaskiya ga Allah da kuma Yesu, za mu sami amincewar Allah. Amma “ayyukan” da aka ambata a Yakub sura 2, ba “ayyukan Koyarwar Musa” da Bulus ya yi magana a kai ba ne. Yakub yana magana ne game da ayyukan da Kiristoci suke yi a rayuwarsu na yau da kullum. (Yak. 2:24) Ayyukan nan suna nuna ko Kirista ya gaskata da Allah da gaske ko aꞌa. w23.12 3 sakin layi na 8; 4-5 sakin layi na 10-11
Asabar, 22 ga Maris
Miji shi ne kan matarsa.—Afis. 5:23.
Idan kina so ki yi aure, ki yi tunani sosai a kan wanda za ki aura. Ki tuna cewa, bayan kin yi aure, za ki riƙa bin ja-gorancin maigidanki. (Rom. 7:2; Afis. 5:33) Don haka, ki yi wa kanki tambayoyin nan: ‘Shi Kirista ne da ya manyanta? Bautar Jehobah ce abu mafi muhimmanci a rayuwarsa? Yana yanke shawarwari masu kyau? Yana yarda da kurakuransa? Yana daraja mata? Shin zai iya taimaka min in kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, ya yi min tanadi, kuma ya zama abokina?’ Gaskiyar ita ce, idan kina so ki auri mijin kirki dole ne ke ma ki yi shirin zama macen kirki. Macen kirki za ta zama “mai taimako” ga maigidanta. (Far. 2:18) Kuma da yake tana ƙaunar Jehobah, za ta yi iya ƙoƙarinta don ta sa mutane su ga halaye masu kyau na maigidanta. (K. Mag. 31:11, 12; 1 Tim. 3:11) Za ki iya shirya yin hakan ta wurin ƙara ƙaunar Jehobah, da kuma taimaka wa mutane a iyalinki da kuma a ikilisiya. w23.12 22-23 sakin layi na 18-19
Lahadi, 23 ga Maris
In waninku yana bukatar hikima, sai ya roƙi Allah.—Yak. 1:5.
Jehobah ya yi alkawari zai ba mu hikima da za ta taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. Muna bukatar hikimar Allah musamman ma saꞌad da za mu yanke shawarwarin da za su shafi rayuwarmu Yana kuma ba mu ƙarfin jimrewa. Kamar yadda Jehobah ya yi wa manzo Bulus, haka ma zai iya ba mu ƙarfin jimre matsalolin da muke fuskanta. (Filib. 4:13) Wani abin da yake amfani da shi shi ne ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci. A dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya yi adduꞌa sosai. Ya roƙi Jehobah kada ya bar mutane su ɗauke shi a matsayin mai saɓo kuma su hukunta shi saboda hakan. Maimakon Jehobah ya yi hakan, ya aika wani malaꞌika wurin Yesu don ya ƙarfafa shi. (Luk. 22:42, 43) Mu ma Jehobah zai iya sa ꞌyanꞌuwanmu su kira mu ko su ziyarce mu don su ƙarfafa mu. Dukanmu za mu iya neman zarafin gaya wa ꞌyanꞌuwanmu “kalmar ƙarfafawa.”—K. Mag. 12:25. w23.05 10-11 sakin layi na 9-11
Litinin, 24 ga Maris
Ku ƙarfafa juna, ku yi ta gina juna.—1 Tas. 5:11.
Idan wanɗanda suka daɗe ba su zo taro ba suka zo Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, za su iya jin tsoro don ba su san abin da ꞌyanꞌuwa za su faɗa ba. Don haka, kada ka yi musu tambayoyin da za su kunyantar da su, ko kuma ka faɗi abin da zai sa su baƙin ciki. Su ꞌyanꞌuwanmu ne kuma muna farin cikin sake bauta wa Jehobah tare da su. (Zab. 119:176; A. M. 20:35) Muna godiya domin Yesu ya umurce mu mu tuna da mutuwarsa kowace shekara kuma mun san muhimmancin yin hakan. Idan muka halarci taron, za mu amfana kuma mutane ma za su amfana a hanyoyi da yawa. (Isha. 48:17, 18) Zai sa mu ƙara ƙaunar Jehobah da kuma Yesu. Zai nuna cewa muna godiya don abin da suka yi mana. Zai kyautata dangantaka da ke tsakaninmu da ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci. Za mu kuma taimaka ma mutane su san yadda su ma za su amfana daga fansar Yesu Kristi. Bari dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi shiri don Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekara, wato ranar da ta fi muhimmanci a shekara! w24.01 14 sakin layi na 18-19
Talata, 25 ga Maris
Ni ne Yahweh . . . wanda yake nuna muku hanyar da za ku bi.—Isha. 48:17.
Ta yaya Jehobah yake mana ja-goranci? Da farko, yana yin hakan ta Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. Ban da haka, yana amfani da ꞌyan Adam don ya yi mana ja-goranci. Alal misali, yana amfani da “bawan nan mai aminci, mai hikima” don ya tanada mana abubuwan da za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau. (Mat. 24:45) Akwai wasu mutane kuma da Jehobah yake amfani da su don ya yi mana ja-goranci. Alal misali, masu kula da daꞌira da dattawa a ikilisiya suna ƙarfafa mu kuma suna ba mu shawarwari da za su taimaka mana saꞌad da muke yanayi mai wuya. Muna godiya sosai don yadda Jehobah yake mana ja-goranci a wannan lokaci mai wuya. Shawarwari da muke samu suna taimaka mana mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, kuma mu sami rai na har abada. Amma a wasu lokuta yana iya mana wuya mu bi ja-gorancin Jehobah, musamman ma in ya yi hakan ta wurin ꞌyan Adam. A wasu lokuta, muna bukatar mu ƙara gaskata cewa Jehobah ne yake yi mana ja-goranci ta wurin ꞌyanꞌuwan nan. Kuma za mu amfana idan muka bi ja-gorancin. w24.02 20 sakin layi na 2-3
Laraba, 26 ga Maris
Kada ku nuna ƙaunarku ta wurin surutun baki kawai, amma ku nuna ƙaunarku ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.—1 Yoh. 3:18.
Idan muna nazarin Kalmar Allah sosai, hakan zai taimaka mana mu ƙara ƙaunar sa. Yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka yi ƙoƙari ka ga abin da nassin yake koya maka game da Jehobah. Ka yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Ta yaya nassin nan ya nuna cewa Jehobah yana ƙauna ta? Ta yaya hakan ya nuna cewa Jehobah ya cancanci in bauta masa?’ Wani abu kuma da zai sa mu ƙara ƙaunar Jehobah shi ne, yin adduꞌa ga Jehobah a kullum da bayyana masa yadda muke ji. (Zab. 25:4, 5) Jehobah zai amsa adduꞌarmu. (1 Yoh. 3:21, 22) Ya kamata yadda kuke ƙaunar mutane ma ya ci gaba da ƙaruwa. Bayan Bulus ya yi wasu shekaru da zama Kirista, ya haɗu da wani matashi mai kirki, mai suna Timoti. Timoti, yana ƙaunar Jehobah da mutane. Bayan wasu shekaru, Bulus ya gaya wa Filibiyawa cewa: “Ba ni da wani kamar [Timoti] wanda ya damu da ku sosai.” (Filib. 2:20) Bulus ya ga cewa Timoti yana ƙaunar mutane sosai. Ba mamaki, ikilisiyoyin da Timoti ya ziyarta sun dinga marmarin zuwansa.—1 Kor. 4:17. w23.07 9 sakin layi na 7-10
Alhamis, 27 ga Maris
Sam sam ba zan yar da kai ba.—Ibran. 13:5.
Musa ya mutu kafin Israꞌilawa su shiga Ƙasar Alkawari. Bayan da wannan mutum mai aminci ya mutu, shin Jehobah ya daina taimaka wa mutanensa ne? Aꞌa. Jehobah ya yi musu tanadi muddin sun riƙe amincinsu gare shi. Kafin Musa ya mutu, Jehobah ya gaya masa ya naɗa Joshua ya ja-gorance su. Musa ya riga ya yi shekaru da yawa yana horar da Joshua. (Fit. 33:11; M. Sha. 34:9) Ƙari ga haka, akwai wasu mutane da suke ja-goranci. Wasu cikinsu shugabanni ne a kan dubu-dubu, wasu a kan ɗari-ɗari, wasu a kan hamsin-hamsin, wasu kuma a kan goma-goma. (M. Sha. 1:15) Jehobah ya tanada wa mutanensa abin da suke bukata. Haka ma yake a zamanin Iliya. Iliya ya yi shekaru da yawa yana taimaka wa Israꞌilawa su riƙa yin bauta ta gaskiya. Sai Jehobah ya ba shi wata hidima dabam a Kudancin Israꞌila, wato Yahuda. (2 Sar. 2:1; 2 Tar. 21:12) Shin hakan na nufin cewa Jehobah ya yasar da waɗanda suke bauta masa da aminci a ƙabilu goma na Israꞌila ne? Aꞌa, domin Iliya ya yi shekaru da yawa yana horar da Elisha. Jehobah ya ci-gaba da cika nufinsa da kuma taimaka wa bayinsa masu aminci. w24.02 5 sakin layi na 12
Jumma’a, 28 ga Maris
Ku yi zaman mutanen haske.—Afis. 5:8.
ꞌYanꞌuwan da ke Afisa sun koyi gaskiyar da ke Kalmar Allah kuma suna bin ta, ta zama musu haske. (Zab. 119:105) ꞌYanꞌuwan nan da ke Afisa sun daina bin koyarwar addinin ƙarya da yin lalata. Yanzu sun zama masu yin koyi da Allah kuma suna iya ƙoƙarinsu su bauta masa kuma su faranta masa rai. (Afis. 5:1) Kafin mu san gaskiya, mu ma a cikin duhu muke a batun addini da kuma lalata. Wasunmu mun yi bukukuwan addinan ƙarya da kuma lalata. Amma, da muka fahimci ƙaꞌidodin Jehobah, sai muka canja rayuwarmu kuma muka soma yin rayuwa yadda za ta gamshe shi. Matakin nan da muka ɗauka ya amfane mu sosai. (Isha. 48:17) Amma da sauran aiki. Muna bukatar mu ci-gaba da kiyaye kanmu daga wannan duhun da muka bari kuma mu yi “zaman mutanen haske.” w24.03 21 sakin layi na 6-7
Asabar, 29 ga Maris
Duk inda muka kai, mu ci gaba daga nan.—Filib. 3:16.
Mai yiwuwa kana bukatar ka yi wasu canje-canje a rayuwarka don ka iya bin ƙaꞌidodin Jehobah. Ko kuma kana bukatar ƙarin lokaci don ka ƙarfafa bangaskiyarka. (Kol. 2:6, 7) Wasu ɗalibai sukan fi wasu saurin kusantar Jehobah, kuma shekarun da matasa sukan kai kafin su yi alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma ba ɗaya ba ne. Don haka, ka yi ƙoƙari ka san inda kake bukatar yin gyara kuma ka yi gyaran. Kada ka gwada kanka da kowa. (Gal. 6:4, 5) Ko da ka ga cewa ba ka yi shirin yin alkawarin bauta wa Jehobah yanzu ba, ka ci-gaba da yin wannan burin. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yi duk wani gyaran da kake bukata. (Filib. 2:13) Kuma ka kasance da tabbacin cewa Jehobah zai ji adduꞌarka ya kuma taimake ka.—1 Yoh. 5:14. w24.03 5 sakin layi na 9-10
Lahadi, 30 ga Maris
Ku maza, . . . ku yi zamanku da matanku tare da tunani.—1 Bit. 3:7.
Akwai lokacin da ran Saratu ya ɓace kuma ta gaya wa maigidanta yadda take ji, har ma ta ce laifinsa ne. Ibrahim ya san cewa Saratu tana masa ladabi kuma ta saba tallafa masa. Ya saurare ta kuma ya yi ƙoƙarin magance matsalar. (Far. 16:5, 6) Me wannan ya koya mana? Magidanta, kuna da ikon tsai da shawarwari a madadin iyalinku. (1 Kor. 11:3) Amma fa, zai fi dacewa ka tattauna da matarka kuma ka saurare ta da kyau kafin ka yanke shawara, musamman ma idan abin zai shafe ta. (1 Kor. 13:4, 5) Akwai lokacin da Ibrahim ya samu baƙi babu zato, kuma ya so ya yi musu karamci. Sai ya ce wa Saratu ta bar abin da take yi kuma ta je ta yi musu abin da za su ci. (Far. 18:6) Nan da nan Saratu ta yi abin da Ibrahim ya ce. Mata, za ku iya yin koyi da Saratu ta wajen bin umurnin mazajenku. Idan kuna hakan, za ku kyautata zamanku.—1 Bit. 3:5, 6. w23.05 24-25 sakin layi na 16-17
Litinin, 31 ga Maris
Hikimar da ta fito daga wurin Allah . . . mai son yin biyayya ce.—Yak. 3:17, New World Translation.
Da Gideyon ya zama alƙali, ya bukaci halin biyayya da kuma ƙarfin zuciya sosai. Domin an ba shi aiki mai wuya, wato cewa ya rushe bagadin Baal na babansa. (Alƙa. 6:25, 26) Daga baya, da Gideyon ya tattara sojojinsa, sai aka gaya masa ya rage yawan sojojin har sau biyu. (Alƙa. 7:2-7) A ƙarshe, an umurce shi ya kai wa maƙiyansa hari da tsakar dare. (Alƙa. 7:9-11) Ya kamata dattawa su zama masu “sauƙin kai,” wato masu saurin yin biyayya. Dattijon da yake da sauƙin kai yakan yi biyayya da umurnin da ƙungiyar Jehobah ta bayar da kuma wanda ya karanta daga Littafi Mai Tsarki. Ta haka, yana kafa misali mai kyau ma sauran ꞌyanꞌuwa. Duk da haka, a wasu lokuta zai iya masa wuya ya yi biyayya. Alal misali, zai iya masa wuya idan ana ba shi umurnai da yawa ko ana canja umurnan a-kai-a-kai. A wasu lokuta ma, zai iya yin shakkar ko umurnin da aka ba shi ya dace. Ƙari ga haka, za a iya ce ya yi aikin da zai sa hukumomi su kama shi ko su tsare shi. Ta yaya dattawa za su yi biyayya kamar Gideyon a yanayoyin nan? Ka saurari umurnin da aka ba ka da kyau kuma ka yi daidai abin da aka ce. w23.06 4-5 sakin layi na 9-11