Ka Ƙarfafa Iyalinka da “Magana Masu-Daɗin Ji”
SA’AD da yake zaune a cikin mota yana jiran matarsa, fushin David sai ƙaruwa yake yi da shigewar kowane minti. Yana ta duban agogonsa. Sa’ad da Diane, wato matarsa, ta fito daga gida, ya kasa riƙe fushinsa.
“Me ya sa kika bar ni a nan ina ta jiranki?” ya yi tsawa. “Kullum sai kin makara! Me ya sa ba za ki gama kwalliyanki da sauri ba a kalla sau ɗaya?”
Diane ta ji haushi sosai. Sai ta fashe da kuka, ta koma cikin gida a guje. Nan da nan David ya gane cewa ya yi kuskure. Fushin da ya yi ya ƙara lalata abubuwa ne kawai. Menene zai yi yanzu? Ya kashe mota, ya yi ajiyar zuci, sai ya bi ta cikin gida.
Wannan labarin ya nuna abin da ke faruwa, ko ba haka ba? Ka taɓa yin da na sani bayan ka faɗi wani abu? Idan muka yi magana kafin mu yi tunani, sau da yawa muna faɗin abubuwan da muke yin nadama. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciyar mai-adalci ta kan yi tunanin abin da za ta amsa.”—Misalai 15:28.
Yana da wuya mu yi tunani sosai kafin mu yi magana, musamman ma idan mun fusata, ko kuma mun tsorata. Musamman da waɗanda suke cikin iyali, a duk lokacin da muke so mu furta yadda muke ji hakan yakan sa mu ga laifin wasu. Hakan kuma zai iya sa mu yi fushi sosai ko kuma ya sa mu soma jayayya.
Me ya kamata mu yi don mu yi nasara? Ta yaya za mu sa kada yadda muke ji ya sha kanmu? Za a iya samun shawara mai kyau daga Sulemanu marubucin Littafi Mai Tsarki.
Ka Yi Tunanin Abin da Za ka Faɗa da Yadda Za ka Faɗe Shi
Kamar yadda Sulemanu marubucin littafin Mai-Wa’azi ya rubuta yadda yake ji game da rayuwa, hakika hakan ya nuna yadda yake ji game da batun. Ya ce: “Na ƙi jinin rai.” A wani lokaci ya ce rayuwa “banza ne.” (Mai-Wa’azi 2:17; 12:8) Duk da haka, ba baƙin cikin Sulemanu ne kawai aka rubuta a cikin Mai-Wa’azi ba. Ya ga cewa bai dace ya yi magana kawai game da abubuwa marasa kyau na rayuwa ba. Da yake kammala littafin, Sulemanu ya nuna cewa ya nemi ‘ya sami magana masu-daɗin ji, da abin da aka rubuta daidai, kalmomin gaskiya ke nan.’ (Mai-Wa’azi 12:10) Wata fassara da aka yi ta ce wai ya yi “ƙoƙari ya bayyana waɗannan abubuwa a hanya da ta fi kyau da kuma yadda ya dace.”—Contemporary English Version.
Sulemanu ya fahimci cewa yana bukatar ya kame kansa. Wato kamar dai, ya ci gaba da tambayar kansa ne: “Abin da na ke son in faɗa gaskiya ne? Idan na faɗi waɗannan kalaman, mutane za su yi ji daɗi ne, kuma su amince da shi?” Ta wajen neman “magana masu daɗin ji,” hakan ya sa ya hana yadda yake ji ya rikita tunaninsa.
Sakamakon haka ba kawai kyakkyawan rubutu ba ne amma tushe ne na hikimar Allah game da ma’anar rayuwa. (2 Timothawus 3:16, 17) Shin salon Sulemanu na tattauna batu mai ban haushi zai taimake mu ne wajen kyautata cuɗanyarmu da waɗanda muke ƙauna? Yi la’akari da wannan misalin.
Ka Koyi Kame Kanka
Alal misali, a ce yaro ya dawo gida daga makaranta yana riƙe da rahoton sakamakon jarabawarsa yana baƙin ciki. Ubansa ya dubi rahoton ya ga inda yaron ya faɗi. A nan take sai uban ya yi fushi, ya tuna dukan lokatai da yaron bai yi aikin da aka ba shi daga makaranta ba. Uban ya ji kamar ya dake shi: “Da ma ai kai rago ne! Idan ka ci gaba haka ba za ka yi nasara a rayuwarka ba!”
Kafin ya ƙyale mugun tunani ya rinjayi irin martani da zai mayar, ya kamata uban ya tambayi kansa, ‘Shin abin da nake tunani gaskiya ne kuma daidai ne?’ Wannan tambayar za ta taimake shi ya bambance tsakanin gaskiya daga yadda yake ji. (Misalai 17:27) Da gaske ne ɗan ba zai yi nasara ba domin bai ci jarabawa ɗaya ba? Rago ne da gaske, ko kuma dai yana barin aikin ne domin wata matsala da ya fuskanta wajen fahimtar wasu abubuwan? Littafi Mai Tsarki ya yi ta nanata muhimmancin ɗaukan batutuwa kamar yadda suke da gaske. (Titus 3:2; Yaƙub 3:17) Domin su ƙarfafa yaro, iyaye suna bukatar su faɗi “kalmomin gaskiya.”
Ka Zaɓi Kalmomi da Suka Dace
Da zarar uban ya zaɓi abin da zai ce, sai ya tambayi kansa, ‘Yaya zan faɗe shi da kalmomi da ɗana zai ji daɗi, kuma ya amince da shi?’ Hakika, zaɓan kalmomi da suka dace ba shi da sauƙi. Amma iyaye suna bukatar su tuna cewa matasa sau da yawa suna iya tunanin cewa idan ba su ci dukan jawabansu ba su yi nasara ba. Suna iya ɗaukan wuri ɗaya da suka kasa ko kuma inda suka raunana su faɗaɗa muhimmancinsa, hakan zai sa su fara ganin cewa ba za su taɓa cin nasara ba. Idan iyaye suka faɗi abin da bai dace ba, hakan zai sa yaron ya tabbata cewa tunaninsa daidai ne. Kolossiyawa 3:21 ta ce: “Ku ubanni, kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna, domin kada ransu ya yi suwu.”
Kalmomi kamar su “koyaushe” da “ba ka taɓa” ba sa nuna ainihin gaskiyar batu. Idan iyaye suka ce, “Ba za ka taɓa zama kome ba,” hakan zai sa yaron ba zai ga kansa da daraja ba. Idan aka yi amfani da irin waɗannan furcin a yanayi da yawa na rayuwa, yaro zai fara ganin kansa ba zai taɓa yin nasara ba a rayuwarsa. Hakika, wannan yana kashe gwiwa kuma ba gaskiya ba ne.
Ko da yaushe ya fi kyau a nanata ɓangare mafi kyau na kowane al’amari. Uba na misalinmu yana iya cewa: “Ɗana, na ga kana baƙin ciki domin inda ka faɗi a jarrabawanka. Na sani cewa kana ƙoƙari ƙwarai a ayyukanka na makaranta. Bari mu tattauna game da inda ka faɗi mu ga yadda za mu magance dukan wata matsala da ka ke fuskanta.” Domin ya fahimci yadda zai taimaki ɗansa da kyau, uban zai iya yin takamammun tambayoyi ya ga ko da wasu matsaloli.
Bi da matsalar ta wannan hanyar mai kyau hakika zai fi yin magana da fushi. “Zantattuka masu-daɗi” in ji Littafi Mai Tsarki, “masu-zaƙi ne ga rai, kuma lafiya ne ga ƙasussuwa.” (Misalai 16:24) Yara, hakika, dukan iyali, sun fi ci gaba cikin yanayi na salama da ƙauna.
“Daga Cikin Yalwar Zuciya”
Ka yi tunanin mutumin da aka ambata daga farkon wannan talifin. Da bai fi ba idan ya ba da lokaci ya zaɓi “magana masu daɗi” na gaskiya maimakon ya huce fushinsa a kan matarsa? Magidanci a irin wannan yanayi ya kamata ya tambayi kansa: ‘Ko da yake matata tana bukatar ta yi gyara wajen shiri a kan lokaci, shin gaskiya ne cewa ko da yaushe ne take makara? Wannan lokacin ya dace kuwa in yi magana a kan wannan? Baƙar magana da fushi za su motsa ta kuwa ta so ta yi gyara?’ Dakatawa mu yi wa kanmu irin waɗannan tambayoyi zai taimake mu mu guji ɓata wa waɗanda muke ƙauna rai ba da sonmu ba.—Misalai 29:11.
Me za mu yi, idan dukan tattaunawarmu ta iyali tana juyawa ta zama jayayya? Ya kamata mu yi tunani sosai, mu yi la’akari da abin da yake sa muke zaɓan kalmominmu. Abin da muka ce, musamman sa’ad da muka yi fushi, zai bayyana irin mutumin da muke da gaske. Yesu ya ce: “Daga cikin yalwar zuciya bakin ya kan yi magana.” (Matta 12:34) Wato, zancenmu sau da yawa yana bayyana tunaninmu, muradinmu, da kuma halayenmu.
Muna ɗaukan rayuwa kamar yadda yake da gaske kuma da bege? To, muryarmu da kuma abin da muke magana a kai zai nuna haka. Mu masu tsattsauran ra’ayi ne da mugun fata da kuma kushe wa mutane? Idan haka muke, za mu kashe wa wasu gwiwa da abin da muka ce ko kuma yadda muka faɗe shi. Ba za mu sani ba cewa tunaninmu ko kuma furcinmu ya zama marar kyau. Za mu gaskata ma cewa ra’ayinmu daidai ne. Amma mu mai da hankali kada mu ruɗi kanmu.—Misalai 14:12.
Abin farin ciki, muna da Kalmar Allah. Littafi Mai Tsarki zai taimake mu mu binciki tunaninmu mu ga waɗanda ba sa bukatar gyara da kuma waɗanda muke bukatar mu gyara. (Ibraniyawa 4:12; Yaƙub 1:25) Ko yaya halinmu yake ko kuma yadda aka rene mu, dukanmu muna iya zaɓan mu canja yadda muke tunani da kuma yadda muke yin abubuwa idan muna son mu yi haka da gaske.—Afisawa 4:23, 24.
Ƙari ga yin amfani da Littafi Mai Tsarki, muna iya yin wani abu don mu bincika yadda muke cuɗanya da wasu. Ka tambayi wasu. Alal misali, ka tambayi matarka ko kuma ɗanka ya gaya maka gaskiya game da yadda ka ke yi a wannan al’amari. Ka yi magana da abokinka mai dattako da ya sanka da kyau. Zai bukaci tawali’u ka yarda da abin da za su ce kuma ka yi gyara da ake bukata.
Ka Yi Tunani Kafin Ka Yi Magana!
A ƙarshe, idan da gaske ba ma so mu baƙanta wa wasu rai da furcinmu, muna bukatar mu yi abin da Misalai 16:23 ta ce: “Zuciyar mai-hikima tana koya ma bakinsa, tana kuwa ƙara ma leɓunansa sani.” Kame kanmu ko da yaushe yana da wuya. Duk da haka, idan muka nemi mu fahimci wasu maimakon mu zarge su ko kuma mu kushe su, zaɓan kalmomi da suka dace mu furta ra’ayinmu zai kasance mana da sauƙi.
Hakika, babu kamili cikinmu. (Yaƙub 3:2) A wasu lokatai, dukanmu muna magana babu tunani. (Misalai 12:18) Amma da taimakon Kalmar Allah za mu iya koyon mu yi tunani kafin mu yi magana kuma mu saka yadda wasu suke ji da kuma abubuwa da suke so gaba da namu. (Filibbiyawa 2:4) Mu ƙuduri anniyar zaɓan “magana masu daɗi” na gaskiya, musamman ma sa’ad da muke magana da waɗanda suke iyalinmu. Ta haka furcinmu ba zai baƙanta wa wasu rai ba, mai makon haka, zai kasance mai warkarwa mai gina waɗanda muke ƙauna.—Romawa 14:19.
[Hoto a shafi na 12]
Ta yaya za ka guje wa faɗan abin da za ka yi nadama daga baya?