TALIFIN NAZARI NA 8
Gargaɗin da Kake Bayarwa Yana Ƙarfafa Mutane?
“Turare da man ƙanshi sukan farantar da rai, amma farin cikin abokantaka daga shawara mai kyau ne.”—K. MAG. 27:9.
WAƘA TA 102 “Mu Taimaki Marasa Ƙarfi”
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1-2. Mene ne wani ɗan’uwa ya koya game da yi wa mutane gargaɗi?
SHEKARU da yawa da suka shige, wasu dattawa biyu sun ziyarci wata ’yar’uwa da ba ta yawan halartan taro don su ƙarfafa ta. Ɗaya daga cikin dattawan ya nuna wa ’yar’uwar nassosin da suka tattauna abin da ya sa halartan taro ke da muhimmanci. Ya ɗauka cewa sun ƙarfafa ’yar’uwar, amma da za su tafi, sai ’yar’uwar ta ce, “Da alama ba ku fahimci matsalolin da nake fuskanta ba.” Dattawan sun yi mata gargaɗi ba tare da sanin matsalolin da take fuskanta da yanayinta ba. A sakamakon haka, abin da suka faɗa bai ƙarfafa ta ba.
2 Dattijon da ya karanta mata nassosin ya tuna abin da ya faru kuma ya ce: “A lokacin, na ɗauka ’yar’uwar tana yi mana rashin kunya ne. Amma da na yi tunanin abin da ya faru, na ga cewa ban mai da hankali ga tambayoyin da ya kamata in yi mata ba, tambayoyi kamar ‘Waɗanne matsaloli ne kike fuskanta?’ ‘Ta yaya zan iya taimaka miki?’ A maimakon haka, na yi ta karanta mata nassosi ne kawai.” Dattijon ya koyi darasi daga abin da ya faru. A yau, shi dattijo ne mai taimako da kuma tausayi.
3. Su waye ne za su iya ba da gargaɗi a ikilisiya?
3 A matsayin makiyaya, dattawa suna da hakkin yi wa ’yan’uwa a ikilisiya gargaɗi. Amma akwai wasu lokuta da ’yan’uwa a ikilisiya ma suke bukatar su yi wa juna gargaɗi. Alal misali, wata ’yar’uwa ko kuma ɗan’uwa zai iya ba abokinsa gargaɗi daga Littafi Mai Tsarki. (Zab. 141:5, New World Translation; K. Mag. 25:12) Ko kuma ’yan’uwa mata da suka manyanta za su iya “horar da mata masu ƙuruciya” kamar yadda aka ambata a Titus 2:3-5. A wasu lokuta, iyaye ma za su bukaci su yi wa yaransu gyara. Wannan talifin yana magana ne game da yadda dattawa za su iya ba da gargaɗi. Amma dukanmu za mu iya amfana daga abin da za a tattauna game da yin gargaɗi a hanyar da za ta faranta ran masu saurara kuma ta sa su bi shi.—K. Mag. 27:9.
4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
4 A wannan talifin, za mu tattauna tambayoyi huɗu game da yin gargaɗi: (1) Me ya sa muke so mu yi gargaɗin? (2) Lallai ne sai mun yi gargaɗin? (3) Waye ne ya kamata ya yi gargaɗin? (4) Ta yaya za ka yi gargaɗi a hanyar da za ta ƙarfafa mutum?
ME YA SA MUKE SO MU YI GARGAƊIN?
5. Ta yaya kasancewa da ra’ayin da ya dace zai taimaka wa dattijo ya yi gargaɗi a hanyar da ta dace? (1 Korintiyawa 13:4, 7)
5 Dattawa suna ƙaunar ’yan’uwansu. A wasu lokuta, suna nuna wannan ƙaunar ta wajen ba da gargaɗi ga ɗan’uwan da yake dab da ɓata dangantakarsa da Jehobah. (Gal. 6:1) Amma kafin dattijo ya yi wa ɗan’uwan gargaɗi, yana bukatar ya yi tunani a kan abin da manzo Bulus ya faɗa game da ƙauna cewa: “Ƙauna tana da haƙuri da kirki, . . . takan sa haƙuri cikin kowane hali, da bangaskiya cikin kowane hali, da sa zuciya cikin kowane hali, da kuma jimiri cikin kowane hali.” (Karanta 1 Korintiyawa 13:4, 7.) Yin tunani a kan waɗannan ayoyin zai taimaka wa dattijon ya yi wa ɗan’uwa gargaɗi a hanyar da za ta nuna cewa yana ƙaunar sa. Idan wanda aka yi wa gargaɗin ya san cewa dattijon yana ƙaunar sa, hakan zai sa ya yi masa sauƙin bin gargaɗin.—Rom. 12:10.
6. Wane irin misali mai kyau ne manzo Bulus ya kafa?
6 Manzo Bulus ya kafa misali mai kyau a matsayin dattijo. Alal misali, sa’ad da ’yan’uwa a Tasalonika suka bukaci gargaɗi, Bulus ya yi musu hakan ba tare da ɓata lokaci ba. Amma a wasiƙun da Bulus ya tura musu, ya fara da yaba musu domin ayyukan da suke yi, da irin ƙaunar da suke nunawa da kuma yadda suke jimrewa. Ya yi tunanin matsalolin da suke fuskanta kuma ya gaya musu cewa ya san irin fama da suke yi da kuma yadda suke jimre tsanantawa da suke fuskanta. (1 Tas. 1:3; 2 Tas. 1:4) Har ya gaya musu cewa suna kafa misali mai kyau ga wasu Kiristoci. (1 Tas. 1:8, 9) Hakika yadda Bulus ya yaba musu ya sa su farin ciki sosai! Babu shakka Bulus ya nuna cewa yana ƙaunar ’yan’uwansa sosai. Abin da ya taimaka masa ya ba wa ’yan’uwan da ke Tasalonika gargaɗin da ya dace ke nan.—1 Tas. 4:1, 3-5, 11; 2 Tas. 3:11, 12.
7. Me ya sa wasu suke ƙin bin gargaɗi?
7 Mene ne zai faru idan ba mu yi gargaɗi a hanyar da ta dace ba? Wani dattijo da ya manyanta ya ce, “Wasu sukan ƙi gargaɗi ba don gargaɗin bai dace da su ba, amma domin ba a ba da shi a hanyar da ya kamata ba ne.” Mene ne hakan ya koya mana? Zai iya yi wa mutane sauƙi su karɓi gargaɗi idan an yi musu gargaɗin cikin ƙauna maimakon fushi.
LALLAI NE SAI MUN YI GARGAƊIN?
8. Waɗanne tambayoyi ne dattijo yake bukatar ya yi wa kansa kafin ya yi ma wani ɗan’uwa gargaɗi?
8 Kada dattawa su riƙa saurin yin gargaɗi. Kafin dattijo ya yi ma wani ɗan’uwa gargaɗi, yana bukatar ya tambayi kansa: ‘Lallai ne sai na yi wannan gargaɗin? Shin na tabbata abin da ɗan’uwan nan ya yi bai dace ba? Ya taka wata dokar Littafi Mai Tsarki ne? Ko dai bambancin ra’ayi ne kawai?’ Dattawa masu hikima suna guje wa “saurin yin magana.” (K. Mag. 29:20) Idan dattijo bai tabbata ko ɗan’uwa yana bukatar gargaɗi ba, zai iya tambayar wani dattijo dabam ra’ayinsa don ya tantance ko abin da ɗan’uwan yake yi bai dace ba kuma yana bukatar a yi masa gargaɗi.—2 Tim. 3:16, 17.
9. Mene ne muka koya daga manzo Bulus game da ba da shawara a kan suturar da mutum ya saka? (1 Timoti 2:9, 10)
9 Ga wani misali. A ce wani dattijo ya damu da irin ado ko kuma suturar da wani ɗan’uwa yake sakawa, dattijon zai iya tambayar kansa cewa, ‘Shin ina da hujja daga Littafi Mai Tsarki na yin gargaɗi?’ Don kada ya ba da gargaɗi bisa ga na shi ra’ayin, zai iya tambayar ra’ayin wani dattijo ko ɗan’uwa da ya manyanta. Tare za su iya bincika abin da Bulus ya faɗa game da ado da kuma saka sutura. (Karanta 1 Timoti 2:9, 10.) Bulus ya yi magana game da ƙa’idar da ta shafi dukan Kiristoci. Ya ce ya kamata Kirista ya riƙa saka suturar da ta dace, kuma ya tabbata cewa ba ta taka dokar Jehobah ba. Amma Bulus bai lissafta irin suturar da mutum ya kamata ya sa da waɗanda bai kamata ya saka ba. Ya san cewa Kiristoci suna da ’yancin saka abin da suke so muddin bai taka dokar Allah ba. Don haka, kafin dattawa su yi wa mutum gargaɗi don suturar da ya saka, su duba ko suturar ta dace kuma ba ta taka dokar Allah ba.
10. Me ya kamata mu tuna game da zaɓin da wasu suka yi?
10 Muna bukatar mu san cewa Kiristoci biyu da suka manyanta za su iya yin zaɓi da suka bambanta, kuma hakan ba ya nufin cewa ɗaya daga cikin zaɓin bai dace ba. Bai kamata mu tilasta wa ’yan’uwanmu su yi abin da muke ganin shi ne daidai ba.—Rom. 14:10.
WAYE NE YA KAMATA YA YI GARGAƊIN?
11-12. Idan wani ɗan’uwa yana bukatar a yi masa gargaɗi, waɗanne tambayoyi ne dattijo yake bukatar ya yi wa kansa, kuma me ya sa?
11 Idan aka ga wani ɗan’uwa yana bukatar a yi masa gargaɗi, waye ne ya kamata ya yi masa gargaɗin? Kafin dattijo ya yi ma matar aure ko ƙaramin yaro gargaɗi, zai dace dattijon ya tuntuɓi maigidan ’yar’uwar ko kuma mahaifin yaron wanda wataƙila zai so ya yi gargaɗin da kansa.b Ko kuma magidancin ko mahaifin zai so ya kasance a wurin da dattijon yake yin gargaɗin. Kuma kamar yadda aka ambata a sakin layi na 3, akwai lokacin da zai dace ’yar’uwa da ta manyanta ne ta gargaɗi ’yar’uwa matashiya.
12 Akwai wani abu kuma da dattijo yake bukatar ya yi tunani a kai. Dattijo zai iya tambayar kansa, ‘Ni ne ya kamata in yi wannan gargaɗin, ko kuma zai fi dacewa wani dabam ya yi?’ Alal misali, zai yi wa ɗan’uwan da yake ji kamar ba shi da amfani sauƙi ya karɓi gargaɗi daga dattijon da ya yi fama da wannan matsalar, maimakon dattijon da bai taɓa fama da wannan matsalar ba. Dattijon da ya taɓa fama da irin wannan matsalar zai fi nuna tausayi kuma hakan zai sa ya yi wa ɗan’uwan sauƙi ya bi gargaɗin da aka ba shi. Amma duka dattawa suna da hakkin ƙarfafa ’yan’uwansu maza da mata don su yi canje-canje da ta jitu da Littafi Mai Tsarki. Don haka, idan wani ɗan’uwa yana bukatar a yi masa gargaɗi, abin da ya fi muhimmanci shi ne a yi masa gargaɗin.
TA YAYA ZA KA YI GARGAƊI A HANYAR DA ZA TA ƘARFAFA MUTUM?
13-14. Me ya sa yake da kyau dattijo ya saurara da kyau?
13 Ka saurari ɗan’uwan da kyau. Idan dattijo yana shirin yi ma wani ɗan’uwa gargaɗi, zai dace ya tambayi kansa: ‘Mene ne na sani game da yanayin da ɗan’uwana yake ciki? Mene ne yake faruwa da shi? Shin yana fuskantar wasu matsaloli da ban sani ba? Mene ne yake bukata yanzu?’
14 Ƙa’idar da ke Yakub 1:19 ta shafi waɗanda suke yin gargaɗi. Yakub ya ce: “Ya kamata kowa ya kasance mai saurin ji, amma ba mai saurin magana ba ko mai saurin fushi ba.” Dattijo zai iya ɗauka cewa ya san kome da kome game da wani batu, amma da gaske ya san hakan? Karin Magana 18:13 ta ce: “Wanda ya amsa magana tun bai ji [“gaskiyar batun” NWT] ba, wawanci ne da abin kunyarsa.” Zai fi dacewa mu ji gaskiyar batun daga mutumin da kansa. Hakan ya ƙunshi saurarawa da kyau kafin mu faɗi albarkacin baƙinmu. Ka tuna darasin da dattijon da aka ambata a farkon talifin nan ya koya. Dattijon ya gane cewa maimakon ya soma ƙarfafa ’yar’uwar da nassosin da ya shirya kawai, da zai fi dacewa ya yi mata tambayoyi kamar: “Waɗanne matsaloli ne kike fuskanta?” “Ta yaya zan taimaka miki?” Idan dattawa suka yi ƙoƙari su san ainihin abin da ya faru, hakan zai taimaka musu su iya ƙarfafa ’yan’uwansu kuma su taimaka musu.
15. Ta yaya dattawa za su bi ƙa’idar da ke Karin Magana 27:23?
15 Ka san tumakin sosai. Kamar yadda muka tattauna a farkon talifin nan, ba karanta nassosi ko ba da shawara ne kawai gargaɗi ya ƙunsa ba. ’Yan’uwanmu suna bukatar su ga cewa mun damu da su, mun fahimci yadda suke ji kuma muna so mu taimaka musu. (Karanta Karin Magana 27:23.) Zai dace dattawa su yi iya ƙoƙarinsu don su ƙulla abokantaka da ’yan’uwansu maza da mata.
16. Mene ne zai taimaka wa dattawa su yi gargaɗi yadda ya dace?
16 Dattawa ba za su so ’yan’uwansu su ji kamar sai suna so su yi musu gargaɗi ne kawai suke zuwa wurinsu ba. A maimakon haka, ya kamata su riƙa tattaunawa da ’yan’uwansu a kai a kai kuma su nuna sun damu da su sa’ad da suke fuskantar matsaloli. Wani dattijo da ya manyanta ya ce, “Idan ka yi hakan, za ka ƙulla dangantaka mai kyau da ’yan’uwanka. Hakan zai sa ya yi maka sauƙi ka yi gargaɗi idan bukata ta taso.” Ƙari ga haka, zai yi ma wanda aka yi wa gargaɗin sauƙi ya bi gargaɗin da aka yi masa.
17. A wane lokaci ne musamman dattijo yake bukatar ya zama mai haƙuri da kuma kirki?
17 Ka zama mai haƙuri da kuma kirki. Kana bukatar ka zama mai haƙuri da kuma kirki musamman sa’ad da wani ya ƙi gargaɗi da ka ba shi daga Littafi Mai Tsarki. Kada dattijo ya yi fushi idan wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ƙi yin amfani da gargaɗin da aka ba ta nan da nan. Littafi Mai Tsarki ya yi annabci game da Yesu cewa: “Karan da ya yi kusan karyewa, ba zai karya ba, fitilar da ta yi kusan mutuwa kuma, ba zai kashe ta ba.” (Mat. 12:20) Don haka, sa’ad da dattijo yake addu’a, ya roƙi Jehobah ya albarkaci wanda aka yi wa gargaɗin, ya taimake shi ya fahimci dalilin da ya sa aka yi masa hakan, kuma ya yi amfani da abin da aka gaya masa. Ɗan’uwan da aka yi wa gargaɗin zai bukaci lokaci don ya yi tunani a kan abin da aka gaya masa. Idan dattijo yana da haƙuri da kuma kirki, wanda aka yi wa gargaɗin ba zai mai da hankali ga yadda aka yi masa gargaɗin ba, amma zai mai da hankali ga abin da aka faɗa. Hakika a kowane lokaci ya kamata mu ba da shawara bisa ga Kalmar Allah.
18. (a) Mene ne ya kamata mu tuna sa’ad da muke so mu yi ma wani gargaɗi? (b) Kamar yadda aka nuna a hoton da kuma akwatin, mene ne iyayen suke tattaunawa?
18 Ka koyi darasi daga kurakuranka. Da yake mu ajizai ne, ba za mu iya bin dukan shawarwarin da aka tattauna a wannan talifin ba tare da kuskure ba. (Yak. 3:2) Amma idan muka yi kuskure, ya kamata mu koyi darussa daga kurakurenmu. Idan ’yan’uwanmu maza da mata suka ga cewa muna ƙaunar su, zai yi musu sauƙi su gafarta mana idan muka ɓata musu rai ta abin da muka faɗa ko kuma muka yi.—Ka duba akwatin nan “Saƙo ga Iyaye.”
ME MUKA KOYA?
19. Me za mu iya yi don mu faranta ran ’yan’uwanmu?
19 Kamar yadda muka gani, yin gargaɗi ba shi da sauƙi. Mu ajizai ne, kuma waɗanda muke yi ma gargaɗi ma ajizai ne. Ka tuna ƙa’idodin da muka tattauna a wannan talifin. Ka tabbata cewa ƙauna ce ta sa kake so ka ba da gargaɗin. Ƙari ga haka, ka tabbata cewa mutumin yana bukatar gargaɗin kuma kai ne ya kamata ka ba da gargaɗin. Kafin ka yi gargaɗin, ka saurara da kyau kuma ka yi tambayoyin da suka dace don ka fahimci abin da mutumin yake fuskanta. Ka yi ƙoƙari ka fahimci mutumin. Ka bi da ’yan’uwanka a hankali kuma ka ƙulla abokantaka da su. Ka tuna cewa muna so gargaɗin da muka yi ya amfani ’yan’uwa kuma ya ‘farantar da ransu.’—K. Mag. 27:9.
WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya
a Yi wa mutum gargaɗi ba shi da sauƙi. Idan da bukatar yi ma wani gargaɗi, ta yaya za mu yi hakan a hanyar da za ta ƙarfafa shi? Wannan talifin zai taimaka wa dattawa su san yadda za su riƙa yin gargaɗi a hanyar da za ta ƙarfafa masu saurara kuma su bi shi.
b Ka duba talifin nan “Yadda Za Mu Fahimci Shugabanci a Ikilisiya” a fitowar Hasumiyar Tsaro ta Fabrairu 2021.