TALIFIN NAZARI NA 15
“Ka Zama Abin Koyi . . . Cikin Magana”
“Ka zama abin koyi ga sauran masu bi, cikin magana.”—1 TIM. 4:12.
WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Wane ne ya ba mu baiwar yin magana?
ALLAHNMU mai ƙauna ne ya ba mu baiwar yin magana. Da zarar Jehobah ya halicci Adamu, Adamu ya iya yin magana da Ubansa na sama. Ban da haka, Allah ya ba shi damar ƙirƙiro sabbin kalmomi. Adamu ya yi amfani da baiwar nan sa’ad da yake ba dabbobi sunaye. (Far. 2:19) Hakika Adamu ya yi farin ciki sosai a lokaci na farko da ya iya magana da kyakkyawar matarsa, wato Hauwa’u!—Far. 2:22, 23.
2. Ta yaya aka yi amfani da baiwar magana a hanya marar kyau a dā da kuma a yanzu?
2 Jim kaɗan bayan hakan, an yi amfani da baiwar yin magana a hanyar da ba ta dace ba. Shaiɗan Iblis ya yi wa Hauwa’u ƙarya kuma hakan ya jawo zunubi da ajizanci. (Far. 3:1-4) Adamu ya yi amfani da harshensa yadda bai kamata ba sa’ad da ya ɗora wa Hauwa’u da kuma Jehobah laifin kuskuren da ya yi. (Far. 3:12) Kayinu ya yi wa Jehobah ƙarya bayan ya kashe ɗan’uwansa Habila. (Far. 4:9) Daga baya, Lamech ya rera wata waƙa da ta nuna cewa yana goyon bayan yadda mutane suka zama masu son faɗa a zamaninsa. (Far. 4:23, 24) Yaya yanayin yake a yau? Mukan ga ’yan siyasa da suke zage-zage a fili. Kuma yawancin fina-finai a yau suna ɗauke da maganganun banza. A makaranta da wuraren aiki, akan yi maganganun banza. Gaskiyar ita ce maganganun banza da ake yi sun nuna yadda duniya ta daɗa muni.
3. Wane haɗari ne ya kamata mu guje wa kuma me za mu tattauna a wannan talifin?
3 In ba mu yi hankali ba, za mu iya sabawa da maganganun banza har mu ma mu soma yin su. Hakika, a matsayinmu na Kiristoci, muna so mu faranta ran Jehobah kuma hakan ya ƙunshi guje wa maganganun banza. Ƙari ga hakan, ya kamata mu yi amfani da baiwar yin magana a hanyar da za ta sa a yabi Jehobah. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya yin hakan (1) sa’ad da muke wa’azi, (2) sa’ad da muke taro, da (3) sa’ad da muke hira da mutane. Amma kafin hakan, bari mu tattauna abin da ya sa furucinmu zai iya sa Jehobah farin ciki ko baƙin ciki.
FURUCINMU ZAI IYA SA JEHOBAH FARIN CIKI KO BAƘIN CIKI
4. Bisa ga abin da ke Malakai 3:16, me ya sa furucinmu zai iya sa Jehobah farin ciki ko baƙin ciki?
4 Karanta Malakai 3:16. Shin, za ka iya tunanin dalilin da zai sa Jehobah ya rubuta sunayen waɗanda maganganunsu suka nuna cewa suna tsoronsa kuma suna bimbini a kan sunansa a cikin “littafin tunawa” da yake da shi? Furucinmu yana nuna abin da ke zuciyarmu. Yesu ya ce: “Abin da yake cikin zuciya, shi yake fitowa a baki.” (Mat. 12:34) Abubuwa da muke faɗa suna nuna yadda muke ƙaunar Jehobah. Kuma Jehobah yana son waɗanda suke ƙaunarsa su more rayuwa a duniya har abada.
5. (a) Wace alaƙa ce ke tsakanin ibadarmu da kuma furucinmu? (b) Kamar yadda aka nuna a hoton da ke shafin nan, mene ne bai kamata mu yi ba?
5 Furucinmu zai iya sa Jehobah ya karɓi ibadarmu ko ya ƙi karɓa. (Yak. 1:26) Waɗanda ba sa ƙaunar Jehobah sukan yi magana da faɗa da kuma fahariya. (2 Tim. 3:1-5) Bai kamata mu zama kamar su ba. Muna so mu faranta wa Jehobah rai ta furucinmu. Amma yaya Jehobah zai ji idan muna magana yadda ya kamata sa’ad da muke taro ko wa’azi, sa’an nan in muka koma gida sai mu juya mu soma magana da faɗa?—1 Bit. 3:7.
6. Wane sakamako mai kyau ne aka samu daga yadda Kimberly ta yi amfani da baiwar yin magana da kyau?
6 Idan muna amfani da baiwar yin magana da kyau, za mu nuna cewa mu bayin Jehobah ne. Za mu taimaki mutane su bambanta “tsakanin wanda yake bauta wa Allah da wanda ba ya bauta masa.” (Mal. 3:18) Abin da ya faru da wata ’yar’uwa mai suna Kimberlyb ke nan. An haɗa ta da wata ’yar ajinta su yi aikin makaranta. Bayan sun gama, abokiyar ajinta ta lura cewa Kimberly ta fita dabam da sauran ’yan makarantarsu. Ta lura cewa Kimberly ba ta gulma, kuma ba ta baƙar magana ko zage-zage. Abin ya burge yarinyar sosai kuma daga baya ta yarda Kimberly ta yi nazari da ita. Hakika, yin magana a hanyar da za ta sa mutane su so su koya game da Jehobah yana sa shi farin ciki sosai!
7. Me kake so ka yi da baiwar da Allah ya ba ka na yin magana?
7 Dukanmu muna so mu yi magana a hanyar da za ta ɗaukaka Jehobah kuma ta sa mu kusaci ’yan’uwanmu. Saboda haka, za mu tattauna wasu hanyoyi da za mu iya “zama abin koyi . . . cikin magana.”
KA KAFA MISALI MAI KYAU YAYIN DA KAKE WA’AZI
8. Wane misali ne Yesu ya bar mana a yadda ya yi amfani da baiwar yin magana sa’ad da yake wa’azi?
8 Idan mutane suka ɓata maka rai, ka yi musu magana cikin alheri kuma ka daraja su. Sa’ad da Yesu yake hidimarsa a duniya, mutane sun ce shi mai yawan ci da kuma buguwa ne, wakilin Iblis ne, ba ya bin dokar Assabaci, kuma yana saɓo. (Mat. 11:19; 26:65; Luk. 11:15; Yoh. 9:16) Duk da haka, Yesu bai yi musu baƙar magana ba. Kamar yadda Yesu ya yi, mu ma bai kamata mu yi ramako idan aka yi mana baƙar magana ba. (1 Bit. 2:21-23) Hakika, yin hakan bai da sauƙi. (Yak. 3:2) Me zai taimaka?
9. Me zai taimaka mana mu guji faɗan abin da bai dace ba sa’ad da muke wa’azi?
9 Idan kana wa’azi kuma mutum ya yi maka baƙar magana, ka yi ƙoƙari kada ka rama da baƙar magana. Wani ɗan’uwa mai suna Sam ya ce: “Nakan yi tunanin yadda mutumin yake bukatar ya koya game da Allah kuma ina tuna cewa zai iya canja halinsa.” A wasu lokuta, mutane sukan yi fushi ne domin mun je wurinsu a lokacin da bai dace da su ba. Idan muka haɗu da wani da ke fushi, za mu iya yin abin da wata ’yar’uwa mai suna Lucia take yi. Za mu iya yin gajeriyar addu’a ga Jehobah ya taimaka mana mu kwantar da hankalinmu, kuma mu guji yin baƙar magana.
10. Bisa ga 1 Timoti 4:13, wane maƙasudi ne ya kamata mu kafa wa kanmu?
10 Ka inganta yadda kake koyarwa. Timoti ƙwararren mai wa’azi ne, duk da haka ya bukaci ya ci gaba da inganta koyarwarsa. (Karanta 1 Timoti 4:13.) Ta yaya za mu inganta koyarwarmu? Dole mu yi shiri da kyau. Muna farin ciki cewa akwai abubuwa da yawa da za su taimake mu mu ƙware a yadda muke koyarwa. Ƙasidar nan, Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa da kuma sashen taro da ake kira Ka Yi Wa’azi da Ƙwazo da ke Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu za su iya taimaka maka. Shin, kana amfani da littattafan nan? Idan muka yi shiri da kyau, tsoro ba zai kama mu sosai ba kuma za mu yi magana da ƙarfin zuciya.
11. Me ya taimaka ma wasu Kiristoci su iya koyarwa da kyau?
11 Za mu kuma iya inganta koyarwarmu ta wajen koya daga ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Sam, wanda aka ambata ɗazu, yakan tambayi kansa abin da yake sa wasu Kiristoci su iya koyarwa. Yakan saurare su yayin da suke koyarwa kuma yana bin misalinsu. Wata ’yar’uwa mai suna Talia takan saurari ’yan’uwa da suka iya jawabi sosai don ta koyi yadda za ta riƙa tattaunawa da mutane a kan batutuwan da ake yawan yin tambaya a kai.
KA KAFA MISALI MAI KYAU A TARO
12. Waɗanne ƙalubale ne wasu suke fuskanta?
12 Dukanmu za mu iya ɗaga muryoyinmu mu rera waƙa a taro kuma mu ba da kalamai masu daɗin ji. (Zab. 22:22) Yakan yi ma wasu wuya su yi waƙa ko su yi kalami a taro. Yanayinka ke nan? Idan haka ne, sanin abin da ya taimaka ma wasu zai taimaka maka.
13. Me zai taimaka maka ka rera waƙa da dukan zuciyarka a taro?
13 Ka rera waƙa da dukan zuciyarka. Ainihin dalilin da ya sa ya kamata mu riƙa rera waƙa a taro shi ne don mu yabi Jehobah. Wata ’yar’uwa mai suna Sara ta ce ita ba mai iya waƙa ba ce sosai. Duk da haka tana so ta yabi Jehobah ta yin waƙa. Saboda haka, yayin da take shirya taro a gida, takan shirya yadda za ta yi waƙa ma. Takan koyi yadda za ta rera waƙar kuma ta lura da alaƙar da ke tsakanin waƙar da abubuwan da za a tattauna a taro. Ta ce: “Idan na yi tunani game da kalmomin waƙar, ba na damuwa da cewa ban iya waƙa ba.”
14. Idan kai mai jin kunya ne, me zai taimake ka ka riƙa yin kalamai a kai a kai?
14 Ka riƙa yin kalamai a kai a kai. A gaskiya, hakan zai iya yi ma wasu wuya. Talia, wadda aka yi ƙaulinta ɗazu ta ce: “Nakan ji tsoro idan ina cikin mutane kuma hakan yakan sa ya yi min wuya in yi kalami a taro. Amma da yake ni mai magana a hankali ce, mutane ba sa saurin ganewa.” Duk da haka, Talia ba ta daina yin kalamai a taro ba. Yayin da take shirya abubuwa da za a tattauna a taro, takan tuna wa kanta cewa ya kamata mutum na farko da zai yi kalami a kan tambaya ya yi gajeren kalami kai tsaye. Ta ce: “Hakan yana nufin cewa idan kalamaina gajeru ne, ban yi laifi ba domin abin da mai gudanar da nazarin yake so ke nan.”
15. Me ya kamata mu tuna game da kalamai da muke yi?
15 Ko Kiristoci da ba sa jin kunya ma sukan yi jinkirin yin kalamai a taro. Me ya sa? Wata ’yar’uwa mai suna Juliet ta ce: “A wasu lokuta, nakan yi jinkirin yin kalami domin nakan ji kamar abin da zan faɗa bai kai kome ba.” Amma ka tuna cewa Jehobah yana so mu yi kalamai iya gwargwadonmu ne.c Yana farin ciki idan muna iya ƙoƙarinmu mu yi kalami a taro ko da muna tsoro.
KA KAFA MISALI MAI KYAU YAYIN DA KAKE TAƊI DA MUTANE
16. Waɗanne irin maganganu ne ya kamata mu guji yi?
16 Ka guji yin ‘zage-zage.’ (Afis. 4:31, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Kamar yadda muka ambata ɗazu, bai kamata Kirista ya yi zage-zage ba. Amma akwai irin maganganun zagi da ba a saurin ganewa da ya kamata mu guje wa. Alal misali, bai kamata mu faɗi abubuwa marasa kyau game da waɗanda suka fito daga wata ƙasa ko waɗanda al’adarsu ta bambanta da tamu ba. Ƙari ga haka, bai kamata mu yi wa kowa baƙar magana ba. Wani ɗan’uwa ya ce: “Akwai lokuta da nakan yi wa mutane maganganu marasa kyau cikin wasa. Amma a gaskiya, hakan yana ɓata wa mutane rai. Idan na yi irin maganganun nan, daga baya, sa’ad da nake tare da matata mu kaɗai, takan ce min abin da na gaya mata ko wasu mutane ba daɗi kuma hakan yana taimaka min sosai.
17. Bisa ga Afisawa 4:29, ta yaya za mu ƙarfafa ’yan’uwa?
17 Ka yi magana a hanyar da za ta ƙarfafa mutane. Ka yi saurin yaba wa mutane maimakon sukar su ko yin gunaguni. (Karanta Afisawa 4:29.) Jehobah ya ba Isra’ilawa abubuwa da yawa da ya kamata su yi godiya a kai. Duk da haka, sun yi ta gunaguni. Idan mu masu yawan gunaguni ne, hakan zai iya shafan wasu ma. Ka tuna cewa rahoto marar kyau da ’yan leƙen asiri goma suka kawo ne ya sa “dukan Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa.” (L. Ƙid. 13:31–14:4) Amma idan muna yaba wa mutane, kowa zai yi farin ciki. Babu shakka, ’yar Jephthah ta sami ƙarfafa ta ci gaba da hidimarta domin yadda ƙawayenta suke yaba mata. (Alƙa. 11:40, New World Translation) Sara, wadda aka ambata ɗazu ta ce: “Idan muna yaba wa ’yan’uwa, za mu sa su san cewa Jehobah da ’yan’uwansu a ikilisiya suna ƙaunar su.” Saboda haka, ka nemi hanyoyin yaba wa ’yan’uwa.
18. Bisa ga Zabura 15:1, 2, me ya sa dole ne mu faɗi gaskiya kuma me hakan ya ƙunsa?
18 Ka riƙa faɗin gaskiya. Ba za mu iya faranta ran Jehobah ba idan muna yin ƙarya. Ya tsani kowace irin ƙarya. (K. Mag. 6:16, 17) Ko da yake mutane da yawa a yau suna ganin kamar ƙarya ba wani abu ba ne, muna guje wa yin ta domin Jehobah ya haramta ta. (Karanta Zabura 15:1, 2.) Bai kamata mu ƙi ba da wasu bayanai don mu ruɗi mutane ba.
19. Mene ne kuma ya kamata mu yi hankali a kai?
19 Ka guji yin gulma. (K. Mag. 25:23; 2 Tas. 3:11) Juliet, da aka ambata a baya, ta faɗi yadda take ji game da gulma. Ta ce: “Jin gulma yakan sa ni sanyin gwiwa kuma yakan sa in daina yarda da wanda yake gulmar domin ban san ko ni ma zai yi gulmata gobe ba.” Idan ka ga hirar da kuke yi tana so ta zama gulma, ka canja batun zuwa hira mai ban ƙarfafa.—Kol. 4:6.
20. Mene ne ka ƙudura cewa za ka yi game da yadda kake magana?
20 Da yake muna rayuwa ne a duniyar da yawancin mutane suna yin maganganu marasa kyau, sai mun dāge kafin mu iya faranta wa Allah rai ta furucinmu. Ka tuna cewa Jehobah ne ya ba mu baiwar yin magana, kuma ya damu da yadda muke amfani da ita. Zai yi mana albarka idan muna iya ƙoƙarinmu mu yi magana a hanyar da za ta yabe shi yayin da muke taro ko wa’azi ko muna taɗi da mutane. Bayan Jehobah ya hallaka wannan muguwar duniya, zai yi mana sauƙi mu riƙa yaba wa Jehobah ta yadda muke magana. (Yahu. 15) Amma kafin lokacin, ka ƙudura cewa za ka faranta wa Jehobah rai ta wurin ‘maganar bakinka.’—Zab. 19:14.
WAƘA TA 121 Mu Riƙa Kame Kanmu
a Jehobah ya ba mu babban kyauta, wato baiwar yin magana. Abin taƙaici, yawancin mutane ba sa amfani da wannan kyautar yadda Jehobah yake so. Me zai taimaka mana mu riƙa faɗin alheri kuma mu faranta ran Jehobah a wannan muguwar duniya? Ta yaya za mu faranta ran Jehobah ta furucinmu a lokacin da muke wa’azi, ko taron ikilisiya ko hira da mutane? Talifin nan zai ba da amsoshin tambayoyin.
b An canja wasu sunayen.
c Don samun ƙarin bayani a kan yadda za mu iya ba da kalami, ka duba talifin nan, “Mu Yabi Jehobah a Cikin Ikilisiya” a Hasumiyar Tsaro ta Janairu 2019.
d BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa yana cacar baki da mutumin da ya je yi ma wa’azi. Wani ɗan’uwa ya yi shiru yayin da ake waƙa a taro. Wata ’yar’uwa tana gulma.