Ka Yi Alheri a Furucinka da Ayyukanka
WATA ’yar’uwa mai suna Lisa ta faɗa abin da ya sa ta fara son gaskiya.a Ta ce: “Alherin da ’yan’uwa maza da mata suka yi min ne ya fi ratsa zuciyata.” Wata ’yar’uwa mai suna Anne ma ta ce: “Abin da ya sa na fara son gaskiya shi ne alherin da Shaidun Jehobah suka yi min, ba abin da suka koya min ba.” ’Yan’uwa biyun nan suna jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki yanzu da kuma yin tunani mai zurfi a kansa. Amma abin da ya sa sun fara son gaskiya shi ne alherin da aka yi musu.
Ta yaya za mu yi wa mutane alheri a hanyar da za ta ƙarfafa su? Bari mu tattauna hanyoyi biyu, wato ta furucinmu da kuma ayyukanmu. Sa’an nan za mu tattauna ko su waye ne ya kamata mu yi musu alheri.
YADDA ZA MU YI ALHERI A FURUCINMU
Mace mai alheri da aka yi maganarta a Karin Magana sura 31 tana bin ‘koyarwa ta alheri’ ta furucinta. (K. Mag. 31:26) Wannan ‘koyarwar’ ce take taimaka mata ta san abin da za ta faɗa da yadda za ta faɗe shi. Ya kamata iyaye maza ma su bi wannan koyarwar yayin da suke magana. Yawancin iyaye sun san cewa yin magana da fushi zai iya yin mummunan tasiri a kan yaransu kuma zai iya sa yaran su ƙi jin abin da suka faɗa. Saboda haka, idan iyaye suka yi magana da alheri, zai yi wa yaransu sauƙi su saurare su kuma su yi biyayya da umurnansu.
Ko da kai mahaifi ne ko ba mahaifi ba, ta yaya za ka koyi yadda za ka yi magana da alheri? Abin da ke Karin Magana 31:26 zai taimaka mana mu san yadda za mu yi hakan. Wurin ya ce: ‘Tana magana da hikima.’ Hakan ya ƙunshi yin amfani da kalmomi masu kyau da kuma muryar da ta dace. Yana da kyau mu riƙa tambayar kanmu: ‘Abin da zan faɗa yanzu zai sa mutum fushi ne ko zai kwantar masa da hankali?’ (K. Mag. 15:1) Hakika yana da kyau mu yi tunani kafin mu yi magana.
Wani karin magana kuma ya ce: “Maganar da an yi da rashin tunani tana sa rauni kamar sokin takobi.” (K. Mag. 12:18) Idan muna tunanin yadda kalmominmu da kuma muryarmu za su iya sa mutane ji, za mu ƙoƙarta mu yi magana da kyau. Yin magana bisa ga ‘koyarwa ta alheri’ zai taimaka mana mu guji faɗin abin da zai sa mutane baƙin ciki ko kuma yin magana da faɗa. (Afis. 4:31, 32) A maimakon mu yi wa mutane magana a hanyar da ba kyau, ya kamata mu yi magana a hanyar da za ta kwantar musu da rai. Jehobah ya nuna mana yadda za mu iya yin hakan sa’ad da ya ƙarfafa bawansa Iliya a lokacin da Iliya yake jin tsoro. Jehobah ya yi masa magana ta wurin mala’ika da “ƙaramar murya [da] ta fito a hankali.” (1 Sar. 19:12) Amma ba ta magana ne kaɗai za a iya yin alheri ba. Dole ne mu yi abubuwa da za su nuna cewa mu masu alheri ne. Ta yaya za mu yi hakan?
YI WA MUTANE ALHERI ZAI RATSA ZUCIYARSU
Za mu iya bin misalin Jehobah ta wajen yi wa mutane alheri ta furucinmu da kuma ayyukanmu. (Afis. 4:32; 5:1, 2) Lisa, wadda aka ambata a farkon wannan talifin ta faɗi yadda Shaidun Jehobah suka yi mata alheri. Ta ce: “A lokacin da muka bukaci mu bar gidan da muke zama cikin gaggawa, ’yan’uwa ma’aurata guda biyu sun nemi izini daga wurin aikinsu don su taimaka mana mu kintsa kayanmu. A lokacin, ban ma fara yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah ba!” Wannan alherin da suka yi wa Lisa ya sa ta soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki.
Anne, wadda aka ambata a farkon wannan talifin ma ta nuna godiya don alherin da Shaidun Jehobah suka yi mata. Ta ce: “Domin yadda yanayin duniya yake, yana min wuya in yarda da mutane.” Ta ci gaba da cewa: “A lokacin da na haɗu da Shaidun Jehobah, ban yarda da su ba. Na tambayi kaina cewa, ‘Me ya sa suke damuwa da ni?’ Amma wadda ta yi nazari da ni ta yi min alheri sosai kuma hakan ya sa na soma yarda da ita.” Mene ne sakamakon haka? Anne ta ce: “Daga baya sai na soma tunani sosai a kan abin da nake koya.”
Ka lura cewa alherin da ’yan’uwa suka yi wa Lisa da Anne ya ratsa zuciyarsu sosai kuma hakan ya taimaka musu su soma koya game da Jehobah. Alherin ya sa suka soma yarda da Jehobah da kuma bayinsa.
KU YI KOYI DA ALLAH TA WAJEN YI WA MUTANE ALHERI
Wasu suna iya yin amfani da kalmomi masu daɗin ji kuma su riƙa murmushi domin yadda aka yi renon su ko kuma inda suke zama. Yana da kyau idan mutane suna hakan. Amma idan al’adarmu ko yadda aka yi renonmu ne kaɗai yake sa mu yi magana a hanya mai daɗin ji ko kuma mu riƙa murmushi, hakan ba ya nufin cewa muna koyi da Allah ne.—Ka duba misalin da ke Ayyukan Manzanni 28:2.
Alheri na ƙwarai yana ɗaya daga cikin halayen da ruhu mai tsarki yake haifarwa. (Gal. 5:22, 23) Saboda haka, idan muna so mu yi alheri na ƙwarai, wajibi ne mu bar ruhun Allah ya yi tasiri a kan yadda muke tunani da kuma yin abubuwa. Yin hakan zai nuna cewa muna yin koyi da Jehobah da kuma Yesu. Kamar yadda Yesu ya yi, mu ma muna damuwa da mutane sosai. Saboda haka, muna yin alheri na ƙwarai domin muna ƙaunar Jehobah da kuma mutane. Da haka, irin alherin da muke yi zai zama hali da Allah yake so kuma yake fitowa daga zuciyarmu.
SU WAYE NE SUKA CANCANCI MU YI MUSU ALHERI?
Yana da sauƙi mu yi alheri da godiya ga waɗanda suka yi mana alheri ko kuma waɗanda muka san su. (2 Sam. 2:6; Kol. 3:15) Amma idan muna gani kamar wani bai cancanci mu yi masa alheri ba fa?
Ka yi la’akari da wannan: Jehobah ne ya fi yin alheri ga waɗanda ba su cancanci a yi musu alheri ba, kuma Kalmarsa ta nuna mana muhimmancin nuna wannan halin. An yi amfani da furucin nan “yin alheri ga waɗanda ba su cancanta ba” sau da yawa a cikin Nassosin Helenanci na Kirista. A wace hanya ce Allah yake yi mana alheri?
Jehobah ya yi alheri ga dukan mutane da suka taɓa wanzuwa ta wajen ba su dukan abubuwan da suke bukata don su rayu. (Mat. 5:45) Hakika, Jehobah ya yi wa ’yan Adam alheri tun kafin su san shi. (Afis. 2:4, 5, 8) Manzo Bulus ya rubuto cewa Jehobah ya ba da fansa ga ’yan Adam da “ba su cancanta ba bisa ga alherinsa a yalwace.” (Afis. 1:7) Ƙari ga haka, duk da cewa muna zunubi kuma muna ɓata wa Jehobah rai, yana ci gaba da yi mana ja-goranci da kuma koyar da mu. Umurnansa da kuma kalmominsa suna “ɗiga kamar ruwan sama” da ke saukowa a hankali. (M. Sha. 32:2) Ba zai yiwu mu biya shi don dukan alherin da yake yi mana ba. Kuma gaskiyar ita ce, idan Jehobah bai yi mana alheri ba, ba za mu kasance da begen yin rayuwa har abada ba.—Ka duba abin da ke 1 Bitrus 1:13.
Babu shakka, alherin da Jehobah yake yi hali ne mai kyau da zai sa mu kusace shi kuma mu ma mu yi wa mutane alheri. Saboda haka, maimakon mu zaɓi waɗanda muke so mu yi musu alheri, zai dace mu yi koyi da Jehobah ta wajen yin alheri ga dukan mutane a kowace rana. (1 Tas. 5:15) Idan muna yin alheri a kai a kai, za mu zama kamar wuta da ke ɗumama mutane a lokacin da ake sanyi. Za mu ƙarfafa iyalinmu da ’yan’uwanmu masu bi da abokan aikinmu da ’yan makarantarmu da kuma maƙwabtanmu.
Ka yi tunanin ’yan iyalinka ko ’yan’uwa a ikilisiya da za su amfana idan ka yi musu alheri ta furucinka da kuma ayyukanka. Mai yiwuwa za ka iya taimaka ma wani a ikilisiyarku da ke bukatar taimako da sharan gidansa ko yi masa cefane. Ƙari ga haka, idan kana wa’azi kuma ka ga mutum da yake bukatar taimako, zai dace ka taimaka masa idan zai yiwu.
Bari mu yi koyi da Jehobah kuma mu bar ‘koyarwa ta alheri’ ta yi tasiri a kan furucinmu da kuma ayyukanmu.
a An canja sunayen.