Wane Irin Mutumi ne Kake Son Ka Zama?
WANI shugaban ’yan sanda a wani birni da ke ƙasar Philippines ya tambayi wata majagaba, “Me kika yi wa wannan mutumin ne da ya sa ya canja halinsa?” Sa’ad da yake nuna tarin takardun da ke kan teburinsa, ya daɗa: “Kin san cewa waɗannan tarin bayanai ne na shari’o’in da aka yi masa a dā? Kin rage mana ɗaya daga cikin matsalolin da muke da su a wannan birnin.” Wannan mutumin mashayi ne a dā da ke yawan jan rigima. Menene ya motsa shi ya yi irin waɗannan canje-canje masu yawa a rayuwarsa? Hurarren saƙon da ke cikin Kalmar Allah ne, Littafi Mai Tsarki.
Yawancin mutane sun bi shawarar manzo Bulus da ta ce ‘su tuɓe, ga zance irin zamansu na dā, tsofon mutum, su yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah.’ (Afis. 4:22-24) Ko da muna bukatar mu yi canje-canje masu yawa ko a’a, yafa sabon hali sashe ne na rungumar Kiristanci.
Amma fa, yin canje-canje da kuma samun cin gaba har mu cancanci yin baftisma mafari ne kawai. A lokacin da muke gabatar da kanmu don mu yi baftisma, muna kama ne da icen da aka sassaƙa. Idan ka ga icen za ka san abin da ake son a yi da shi, amma fa, da sauran aiki. Masassaƙin yana bukatar ya daɗa yi wa icen kwalliya don ya yi kyau. A lokacin da muka yi baftisma, muna da ainihin halayen da ake bukata don zama bawan Allah. Amma fa, muna bukatar mu ƙara kyautata sabon halinmu. Muna bukatar mu ci gaba da kyautata shi ta wajen yin gyare-gyare.
Bulus ya ga cewa yana bukatar ya yi gyare-gyare. Ya ce: “In na so yin abin da ke daidai, sai in ga mugunta tare da ni.” (Rom. 7:21, Littafi Mai Tsarki) Bulus ya san ko shi wanene da kuma abin da yake son ya zama. Mu kuma fa? Muna bukatar mu tambayi kanmu: ‘Menene ke tare da ni? Wane irin mutumi ne ni? Kuma wane irin mutumi nake son na zama?’
Menene Ke “Tare da Ni”?
Sa’ad da muka yi wa tsohon gini gyaran fuska, yi wa gidan fenti ba zai magance matsalolin ba idan azarar ta riga ta ruɓe. Idan ba mu gyara wuraren da suka lalace ba, hakan zai jawo matsala ne a nan gaba. Hakazalika, nuna cewa muna da aminci bai isa ba kawai. Dole ne mu bincika halinmu sosai kuma mu fahimci matsalolin da muke bukatar mu magance. Idan ba haka ba, tsofaffin halaye suna iya sake ɓullowa. Saboda haka, bincika kai sosai ya zama dole. (2 Kor. 13:5) Muna bukatar mu gane halaye marar kyau da muke da su kuma mu kawar da su. Don mu cim ma haka, Jehobah ya yi mana tanadin taimako.
Bulus ya rubuta: “Gama maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa rarraban rai da ruhu, da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma, tana kuwa da hamzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” (Ibran. 4:12) Saƙon da ke cikin rubutacciyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, yana iya shafan rayuwarmu sosai. Yana shiga cikinmu sosai, a alamance, har cikin ɓargon da ke can cikin ƙasusuwanmu. Yana bayyana tunaninmu da manufofinmu, yana nuna ainihin ko wane irin mutumi ne mu, ba yadda muka bayyana ba a gaban mutane ko kuma yadda muka ɗauki kanmu. Hakika, Kalmar Allah tana taimaka mana mu fahimci matsalolinmu!
Sa’ad da muka gyara tsohon gini, ba canja abubuwan da suka lalace ba ne ba kawai zai magance matsalolin gabaki ɗaya. Sanin ainihin tushen matsalolin zai taimaka mana mu ɗauki matakan da suka dace don hana matsalolin sake aukuwa. Hakazalika, sanin halayenmu marar kyau da kuma gane ainihin abubuwan da suka jawo su zai taimaka mana mu bi da kasawarmu yadda ya kamata. Abubuwa da yawa suna shafan halayenmu. Wasu a cikinsu su ne matsayinmu da kuma abin hannu da muke da shi, inda muka girma, al’adarmu, iyayenmu, abokanmu, da kuma addininmu. Shirye-shirye da wasannin da muke kallo a talabijin, da kuma wasu hanyoyin yin nishaɗi suna shafanmu sosai. Sanin abubuwan da za su ɓata halinmu zai taimake mu mu rage hakan.
Bayan mun bincika kanmu, muna iya cewa, ‘Ba laifi na ba ne, haka Allah ya halicce ni.’ Wannan tunani ne marar kyau. Sa’ad da yake magana game da waɗanda suke ikilisiyar Koranti da a dā mazinata ne, masu kwana da maza, mashaya, da sauransu, Bulus ya ce: “Waɗansu ma a cikinku dā haka ku ke: amma aka wanke ku, . . . cikin Ruhun Allahnmu.” (1 Kor. 6:9-11) Tare da taimakon ruhu mai tsarki na Jehobah, mu ma za mu iya yin nasara wajen yin canje-canje da suka dace.
Yi la’akari da labarin wani mutumi mai suna Marcos,a wanda ke zaune a ƙasar Philippines. Sa’ad da yake bayani game da irin yanayin da ya girma, Marcos ya ce: “Iyaye na suna yawan yin gardama. Shi ya sa na bijire musu tun ina ɗan shekara 19.” Marcos ya zama mugun ɗan caca, ɓarawo, har da yin fashi da makami. Akwai ma lokacin da shi da wasu suke son su je su yi fashin jirgin sama, amma hakan bai yiwu ba. Marcos ya ci gaba da mugayen halinsa har bayan ya yi aure. Daga baya, ya rasa dukan abin da ya ke da shi wajen yin caca. Ba da daɗewa ba, Marcos ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah suke yi da matarsa. Da farko, ya yi tunanin cewa bai cancanci zama Mashaidi ba. Amma, ta wajen yin amfani da abubuwan da yake koya da kuma halartan taro, hakan ya taimaka wa Marcos ya yi watsi da halayensa na dā. A yanzu ya riga ya yi baftisma kuma yana koya wa mutane a kowane lokaci yadda su ma za su canja halinsu.
Me Kake Son Ka Zama?
Waɗanne canje-canje ne muke bukatar mu yi don mu kyautata halayenmu na Kirista? Bulus ya shawarci Kiristoci: “Ku kawasda dukan waɗannan; fushi, hasala, ƙeta, tsegumi, alfasha daga cikin bakinku: kada ku yi ma juna ƙarya; da shi ke kun tuɓe tsofon mutum tare da ayukansa.” Manzon ya ci gaba da cewa: ‘Ku yafa kuma sabon mutum, wanda a ke sabonta shi zuwa ilimi bisa ga surar mahaliccinsa.’—Kol. 3:8-10.
Ainihin makasudinmu shi ne, mu kawar da tsohon halinmu kuma mu sanya sabon hali. Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu cim ma hakan? Bulus ya ce: “Ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa; kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowanne mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku, hakanan kuma sai ku yi: gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kol. 3:12-14) Yin iya ƙoƙarinmu don mu nuna waɗannan halayen zai taimaka mana mu sami “tagomashi a wurin Ubangiji duk da mutane.” (1 Sam. 2:26) Sa’ad da yake duniya, Yesu ya yi fice wajen nuna halaye masu kyau. Ta wajen yin nazari da kuma yin koyi da misalinsa, za mu iya zama kamar Kristi a matsayin “masu-koyi da Allah.”—Afis. 5:1, 2.
Wata hanya kuma da za mu iya gane canje-canje da wataƙila muke bukatar mu yi ita ce, yin nazarin halayen mutanen da ke cikin Littafi Mai Tsarki, ta wajen yin la’akari da halayensu masu kyau da marar kyau. Alal misali, yi la’akari da Yusufu, ɗan Yakubu uban iyali. Duk da cewa an zalunce shi, Yusufu ya ci gaba da nuna ra’ayi da halaye masu kyau. (Far. 45:1-15) Akasin haka, Absalom ɗan Sarki Dauda ya yi kamar ya damu sosai da mutane kuma an yaba masa domin halinsa mai kyau. Amma gaskiyar ita ce, shi maci amana ne kuma mai kisan kai. (2 Sam. 13:28, 29; 14:25; 15:1-12) Nuna hali mai kyau a munafunce da kuma kyaun siffa ba su ne ainihin abin da ke sa mutum ya kasance da hali mai kyau ba.
Za Mu Iya Yin Nasara
Don mu kyautata halayenmu kuma mu sami tagomashin Allah, muna bukatar mu mai da hankali ga zuciyarmu. (1 Bit. 3:3, 4) Yin canje-canje a halayenmu na bukatar sanin ainihin halayenmu marar kyau da kuma abubuwan da ke jawo su, mu kuma koyi halaye masu kyau. Za mu iya yin nasara a ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na kyautata halayenmu kuwa?
Ƙwarai kuwa, tare da taimakon Jehobah za mu iya yin canje-canje da suka dace. Za mu iya yin addu’a kamar mai zabura: “Daga cikina ka halitta zuciya mai-tsabta, ya Allah; ka sabonta daidaitacen ruhu daga cikina.” (Zab. 51:10) Muna iya roƙon Allah ya ba mu ruhunsa don ya motsa mu, mu kyautata muradinmu na son yin rayuwar da ta jitu sosai da nufinsa. Hakika, za mu iya yin nasara wajen samun tagomashin Jehobah sosai!
[Hasiya]
a Ba ainihin sunansa ba ne.
[Hoto a shafi na 4]
Fenti ne kawai ya kamata a yi wa gidan da guguwa ta lalata?
[Hoto a shafi na 5]
Halinka ya zama kamar na Kristi ne?