TALIFIN NAZARI NA 2
“Ku Yarda Allah Ya Canja Ku Ya Sabunta Tunaninku da Hankalinku”
“Ku yarda Allah ya canja ku ya sabunta tunaninku da hankalinku. Ta haka za ku iya tabbatar da abin da yake nufin Allah, wato abin da yake mai kyau, abin karɓa ga Allah, da kuma abin da yake cikakke.”—ROM. 12:2.
WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1-2. Mene ne ya zama dole mu ci gaba da yi bayan mun yi baftisma? Ka bayyana.
SAU nawa ne kake share gidanka? Wataƙila kafin ka ƙaura ka share gidan da kyau. Amma mene ne zai faru idan ba ka sake share shi ba? Zai yi datti da sauri. Don gidanka ya kasance da tsabta, kana bukatar ka riƙa sharewa kowane lokaci.
2 Haka ma, dole ne mu ci gaba da kyautata halayenmu da yadda muke tunani. Kafin mu yi baftisma mukan yi iya ƙoƙarinmu mu yi canje-canje da ya kamata mu yi a rayuwarmu domin “mu tsabtace kanmu daga dukan abin da zai sa jiki da zuciyarmu ya ƙazantu.” (2 Kor. 7:1) Yanzu, dole ne mu bi gargaɗin da manzo Bulus ya bayar cewa: ‘Ku ci gaba da sabunta.’ (Afis. 4:23, New World Translation) Me ya sa ya kamata mu ci gaba da sabunta halayenmu? Domin halayen mutanen duniya a yau zai iya sa mu kasance da rashin tsabta a gaban Jehobah. Dole ne mu ci gaba da canja halayenmu da yadda muke tunani da kuma abubuwan da muke shaꞌawarsu kafin mu iya faranta wa Jehobah rai.
KU CI GABA DA “SABUNTA TUNANINKU DA HANKALINKU”
3. Mene ne “sabunta tunaninku da hankalinku” yake nufi? (Romawa 12:2)
3 Mene ne ya kamata mu yi don mu sabunta tunaninmu da kuma hankalinmu? (Karanta Romawa 12:2.) Kalmar Helenanci da aka fassara zuwa “sabunta tunaninku da hankalinku” tana iya nufin “ku yi wa tunaninku kwaskwarima.” Hakan ba ya nufin mu yi wasu ayyuka masu kyau kawai. A maimakon haka, dole ne mu bincika halayenmu kuma mu yi canje-canje da za su sa mu yi iyakacin ƙoƙarinmu wajen bin ƙaꞌidodin Jehobah. Kuma ya kamata mu ci gaba da yin hakan.
4. Ta yaya za mu guji barin duniyar nan ta shafe tunaninmu da hankalinmu?
4 Idan mun zama kamiltattu, za mu iya faranta wa Jehobah rai a dukan ayyukanmu. Kafin lokacin, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu faranta wa Jehobah rai. A Romawa 12:2, Bulus ya ce muna bukatar mu sabunta tunaninmu da hankalinmu don mu san abin da Allah yake so mu yi. Maimakon mu bi halin muguwar duniyar nan, dole ne mu soma bincika kanmu don mu san yadda muke barin tunanin Jehobah ya shafi maƙasudinmu da shawarwarin da muke yankewa.
5. Waɗanne tambayoyi ne za mu yi wa kanmu da za su nuna cewa muna tunanin zuwan ranar Jehobah? (Ka duba hoton.)
5 Ka yi laꞌakari da wani misali. Jehobah yana so mu yi ‘marmarin zuwan ranarsa.’ (2 Bit. 3:12) Ka tambayi kanka: ‘Salon rayuwata tana nuna na fahimci cewa ƙarshen wannan zamanin ya yi kusa sosai? Shawarwarina game da zuwa jamiꞌa ko kuma aikina suna nuna cewa bauta wa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwata? Ina da bangaskiya cewa Jehobah zai kula da ni da iyalina, ko kuma ina yawan damuwa game da abin duniya?’ Ka yi tunanin yadda Jehobah yake farin ciki yayin da yake ganin cewa muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi rayuwa da ta jitu da nufinsa.—Mat. 6:25-27, 33; Filib. 4:12, 13.
6. Mene ne ya kamata mu ci gaba da yi?
6 Ya kamata mu bincika tunaninmu a kai a kai kuma mu yi canje-canjen da suka dace. Bulus ya gaya wa Korintiyawa cewa: “Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku.” (2 Kor. 13:5) Ba halartan taro ko yin waꞌazi ne kawai za mu riƙa yi ba idan muna so mu kasance da “bangaskiya.” Ya shafi abubuwan da muke tunani a kai, da abubuwan da muke shaꞌawarsu, da kuma dalilin da ya sa muke yin abubuwa. Don haka, ya kamata mu ci gaba da sabunta tunaninmu da hankalinmu ta wajen karanta Kalmar Allah, da yin tunani yadda Allah yake yi, da kuma yin abubuwan da ya kamata mu yi don mu faranta wa Allah rai.—1 Kor. 2:14-16.
‘KU ƊAUKI SABON HALI’
7. Kamar yadda Afisawa 4:31, 32 suka nuna, mene ne kuma muke bukatar mu yi, kuma me ya sa hakan zai iya ya yi mana wuya?
7 Karanta Afisawa 4:31, 32. Ban da yin canje-canje a tunaninmu, muna bukatar mu ‘ɗauki sabon hali.’ (Afis. 4:24) Yin hakan zai bukace mu mu yi ƙoƙari sosai. Alal misali, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kawar da halayen banza, kamar ɗacin rai da haushi da fushi. Me ya sa hakan zai iya ya yi mana wuya? Domin kawar da wasu halayen banza bai da sauƙi. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa wasu suna da “saurin fushi” da “zafin kai.” (K. Mag. 29:22) Kamar yadda labarin da ke gaba zai nuna mana, ya kamata wanda yake da irin waɗannan halayen banza ya ci gaba da yin canje-canje sosai bayan ya yi baftisma.
8-9. Ta yaya labarin Stephen ya nuna mana dalilin da ya sa ya kamata mu kawar da halinmu na dā?
8 Ya yi ma wani ɗanꞌuwa mai suna Stephen wuya ya rage fushi. Stephen ya ce: “Har bayan na yi baftisma ma, na ci gaba da yin ƙoƙari don in rage fushi. Alal misali, na taɓa bin wani ɓarawo da ya saci rediyo a motata saꞌad da nake waꞌazi. Da ya ga cewa na yi kusa da shi, sai ya yar da rediyon ya gudu. Saꞌad da na gaya ma waɗanda nake waꞌazi tare da su abin da ya faru, sai wani dattijo a cikinsu ya tambaye ni ya ce: ‘Stephen da a ce ka kama shi da me za ka yi masa?’ Tambayar ta sa na gano cewa ina bukatar in daɗa ƙoƙari don in zauna lafiya da kowa.”b
9 Kamar yadda muka gani a labarin Stephen, za mu iya nuna halayen banza farat ɗaya ko bayan muna ganin kamar mun riga mun daina halin. Idan hakan ya faru, kada ka yi sanyin gwiwa ko kuma ka yi tunani cewa kai ba Kirista na ƙwarai ba ne. Manzo Bulus ma ya amince da batun saꞌad da ya ce: “Ya zama mini ƙa’ida cewa idan ina so in yi nagarta, sai in ga mugunta tare da ni.” (Rom. 7:21-23) Da yake dukan Kiristoci ajizai ne, suna da wasu halaye marasa kyau da suke nunawa a wasu lokuta kamar yadda ƙura da datti suna sake taruwa a gidanmu. Ya kamata mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu kasance da tsabta. Ta yaya za mu yi hakan?
10. Mene ne ya kamata mu yi don mu daina halaye marasa kyau? (1 Yohanna 5:14, 15)
10 Ka yi adduꞌa ga Jehobah ya taimaka maka ka canja halinka na dā, kuma ka kasance da tabbaci cewa zai amsa maka kuma ya taimaka maka. (Karanta 1 Yohanna 5:14, 15.) Ko da yake Jehobah ba zai kawar da munanan halayenka ta wajen muꞌujiza ba, zai taimaka maka ka ci gaba da ƙoƙari don ka daina halayen. (1 Bit. 5:10) Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka, kuma ka yi ƙoƙari ka daina yin abubuwan da za su sa ka nuna tsohon halin. Alal misali, ka mai da hankali da irin fina-finai da kake kalla, da shirye-shiryen talabijin, ko kuma karanta labarai da suke ɗaukaka halayen banzan da kake ƙoƙarin dainawa. Kuma kada ka ci gaba da mai da hankali a kan shaꞌawoyin banza.—Filib. 4:8; Kol. 3:2.
11. Waɗanne matakai ne za mu iya ɗaukawa don mu ci gaba da nuna sabon hali?
11 Ko da yake ka yi ƙoƙari ka daina halayenka na dā, yana da muhimmanci ka ɗau sabon hali. Ta yaya za ka iya yin hakan? Ka kafa maƙasudin yin koyi da Jehobah yayin da kake koya game da halayensa. (Afis. 5:1, 2) Alal misali, idan ka karanta wani nassi a Littafi Mai Tsarki da ya nuna yadda Jehobah yake gafartawa, ka tambaye kanka, ‘Ina gafarta wa mutane kuwa?’ Saꞌad da ka karanta yadda Jehobah yake jin tausayin waɗanda suke fama da talauci, ka tambaye kanka, ‘Shin ina damuwa a kan ꞌyanꞌuwa a ikilisiya da suke bukatar taimako, kuma ina nuna hakan a halayena?’ Ka ci gaba da sabunta tunaninka da hankalinka yayin da kake saka sabon hali kuma ka riƙa haƙuri da kanka saꞌad da kana ƙoƙarin nuna wannan halin.
12. Ta yaya Stephen ya shaida yadda Littafi Mai Tsarki yake canja rayuwar mutane?
12 Stephen da aka ambata ɗazu, ya gano cewa a hankali a hankali ne ya koyi sabbin halaye. Ya ce: “Tun da na yi baftisma, na fuskanci yanayoyi da za su iya sa in yi fāda. Na koyi yadda zan guje wa mutanen da suke so su sa ni fushi kuma ina yin amfani da wata dabara don kada faɗa ta taso. Matata da mutane da yawa sun yaba min don yadda na bi da waɗannan yanayoyin. Kuma yadda na bi da yanayin ya ba ni mamaki sosai! Na san cewa ba da ikona ba ne na yi waɗannan canje-canjen. Maimakon haka, na tabbata cewa Littafi Mai Tsarki ne ya taimaka mini in yi hakan.”
KA CI GABA DA YIN TSAYAYYA DA SHAꞌAWOYI MARASA KYAU
13. Me zai taimaka mana mu riƙa shaꞌawar abubuwa masu kyau? (Galatiyawa 5:16)
13 Karanta Galatiyawa 5:16. Jehobah ya yi mana tanadin ruhu mai tsarki don ya taimaka mana mu riƙa yin abin da ya dace. Muna barin wannan ruhun ya taimaka mana idan muna nazarin Kalmar Allah. Muna kuma samun taimakon ruhu mai tsarki saꞌad da muka halarci taro. A taron ikilisiya mukan haɗu da ꞌyanꞌuwanmu maza da mata, waɗanda suke yin iya ƙoƙarinsu don su yi abin da ya dace kamar yadda muke yi. (Ibran. 10:24, 25; 13:7) Ƙari ga haka, saꞌad da muka yi adduꞌa da dukan zuciyarmu ga Jehobah kuma muka roƙe shi ya taimaka mana da kasawarmu, zai ba mu ruhunsa mai tsarki don ya taimaka mana mu guje wa shaꞌawoyi marasa kyau. Ko da yake ayyukan nan ba za su sa mu daina shaꞌawoyi marasa kyau ba, za su taimaka mana mu shawo kansu. Kamar yadda Galatiyawa 5:16 ta faɗa, waɗanda suka yi rayuwa yadda ruhu ya bi da su “ba za su bi halin mutuntaka ba.”
14. Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da kasancewa da shaꞌawar da ta dace?
14 Saꞌad da muka soma yin abubuwan da za su taimaka mana mu kasance da dangantaka mai kyau da Allah, zai dace mu ci gaba da yin abubuwan nan kuma mu kasance da shaꞌawoyin da suka dace. Me ya sa? Domin jarrabar yin abin da bai dace ba tana ɗaya daga cikin abubuwan da za su iya hana mu yin hakan. Ko bayan mun yi baftisma ma, za mu iya gani cewa muna son yin abubuwa da mun riga mun daina yi a dā, kamar caca, da buguwa da giya, da kallon hotunan batsa. (Afis. 5:3, 4) Wani ɗanꞌuwa matashi ya ce: “Wani abin da na yi fama da shi shi ne son wanda jinsinmu ɗaya ne. Na yi tunani cewa zan daina wannan shaꞌawar, amma har ila ina fama da shi.” Mene ne zai taimaka maka idan kana fama da shaꞌawar da ba ta da kyau?
15. Me ya sa yake da ban ƙarfafa cewa akwai wasu da suke fama da shaꞌawoyin da ba su dace ba? (Ka duba hoton.)
15 Idan kana ƙoƙarin shawo kan wata shaꞌawa marar kyau, ka tuna cewa wasu ma suna fama da hakan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa mutum ba.” (1 Kor. 10:13a) An rubuta waɗannan kalmomin domin ꞌyanꞌuwa maza da mata da ke zama a Koranti. A dā wasunsu masu zina ne, ko maza masu kwana da maza, ko kuma masu buguwa. (1 Kor. 6:9-11) Kana ganin cewa bayan sun yi baftisma, ba su sake fama da waɗannan shaꞌawoyin ba? Da wuya. Ko da yake su shafaffun Kiristoci ne, su ma ajizai ne. Babu shakka, sun yi ta fama da shaꞌawoyi marasa kyau a wasu lokuta. Hakan ya kamata ya ƙarfafa mu. Me ya sa? Domin duk wata shaꞌawa marar kyau da kake fama da ita, wani ya riga ya yi tsayayya da ita. Hakika, ya kamata “ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku, da yake kun sani cewa ’yan’uwanku masu bi ko’ina a duniya, su ma suna shan wahala haka.”—1 Bit. 5:9.
16. Wane irin tunani ne ya kamata mu guji yi, kuma me ya sa?
16 Ka guji yin tunani cewa babu wanda zai iya fahimci irin matsalar da kake fuskanta. Yin irin wannan tunanin zai sa ka gan kamar ba ka da mafita, kuma ba za ka iya shawo kan shaꞌawa marar kyau ba. Littafi Mai Tsarki bai yarda da irin tunanin nan ba. Ya ce: “Allah mai aminci ne, ba zai bari a gwada ku fiye da ƙarfinku ba, amma game da gwajin, zai buɗe hanyar tsira yadda za ku iya jimrewa.” (1 Kor. 10:13b) Don haka, ko da muna fama da shaꞌawa marar kyau ne, za mu iya riƙe amincinmu ga Jehobah. Da taimakon Jehobah, za mu iya shawo kan shaꞌawoyin nan.
17. Ko da yake ba za mu iya guje wa yin tunanin da bai dace ba, mene ne za mu iya yi?
17 Ka riƙa tuna cewa: Domin mu ajizai ne, ba za mu iya daina yin tunanin da bai dace ba. Amma idan muka soma tunanin da bai dace ba, za mu iya daina tunanin nan da nan kamar yadda Yusufu ya yi saꞌad da ya gudu daga matar Fotifar. (Far. 39:12) Ba zai dace mu aikata abubuwa marasa kyau da muke tunaninsu ba!
KA CI GABA DA YIN IYA ƘOƘARINKA
18-19. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu yayin da muke iya ƙoƙarinmu mu sabunta tunaninmu da hankalinmu?
18 Sabunta tunaninmu da kuma hankalinmu ya ƙunshi yin iya ƙoƙarinmu mu sa tunaninmu da ayyukanmu su faranta wa Jehobah rai. Don haka, ka bincika kanka a kai a kai kuma ka tambayi kanka: ‘Ayyukana suna nuna cewa na san muna zama a kwanakin ƙarshe? Ina samun ci gaba wajen sabunta halayena? Ina barin ruhun Jehobah ya ja-gorance ni don in shawo kan shaꞌawoyin jiki?’
19 Yayin da kake bincika kanka, kada ka ɗauka cewa ba za ka riƙa yin kuskure ba, amma ka yi farin ciki cewa kana samun ci gaba. Kada ka yi sanyin gwiwa idan ka lura cewa kana bukatar ka yi gyara. A maimakon haka, ka bi shawarar da ke Filibiyawa 3:16 da ta ce: “Duk inda muka kai, mu ci gaba daga nan.” Idan ka yi hakan, ka tabbata cewa Jehobah zai albarkaci ƙoƙarin da kake yi don ka sabunta tunaninka da hankalinka.
WAƘA TA 36 Mu Riƙa Kāre Zuciyarmu
a Manzo Bulus ya gargaɗi ꞌyanꞌuwa masu bi maza da mata kada su yarda wannan muguwar duniya ta shafi tunaninsu da kuma ayyukansu. Wannan shawara ce mai kyau a gare mu a yau. Ya kamata mu tabbata cewa halayen duniya a yau ba su shafe mu ba. Don haka, ya kamata mu ci gaba da canja yadda muke tunani idan mun gano cewa tunaninmu ba ya faranta wa Allah rai. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya yin hakan.
b Ka duba talifin nan “Na Yi Rayuwar Banza” a Hasumiyar Tsaro ta Satumba, 2015.
c BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗanꞌuwa matashi yana tunani ko ya je makarantar jamiꞌa ko kuma ya soma hidimar majagaba.