Jehobah Zai Cika Nufinsa!
“Na faɗi, zan kuwa sa shi tabbata; na ƙudurta, zan kuwa aika.”—ISHA. 46:11.
1, 2. (a) Mene ne Jehobah ya bayyana mana? (b) Wane tabbaci muke da shi a littafin Ishaya 46:10, 11 da 55:11?
FURUCI na farko mai muhimmanci da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin farko Allah ya halicci sama da ƙasa.” (Far. 1:1) Gaskiya ne cewa ba mu fahimci abubuwa da yawa da Allah ya halitta kamar su sarari da haske da kuma ƙarfin da yake sa idan aka jefa abubuwa a sama sai su faɗo ba. Ban da haka ma, dukan abubuwan da muke gani kaɗan ne kawai daga cikin abubuwan da ke sama da ƙasa da Allah ya halitta. (M. Wa. 3:11) Duk da haka, Jehobah ya bayyana mana nufinsa ga duniya da kuma ‘yan Adam. Kuma Allah ya halicci ‘yan Adam a cikin surarsa, domin wannan duniya ce gidan da ya dace da su. (Far. 1:26) Jehobah zai zama Ubansu kuma su zama yaransa.
2 Amma ba a yi nufin Jehobah kamar yadda aka bayyana a sura ta uku na littafin Farawa ba. (Far. 3:1-7) Duk da haka, Jehobah ya yi shirin yadda zai cika nufinsa ga duniya, kuma babu wanda zai hana shi yin hakan. (Isha. 46:10, 11; 55:11) Saboda haka, muna da tabbaci cewa Jehobah zai cika nufinsa na asali a lokacin da ya dace!
3. (a) Waɗanne koyarwa masu muhimmanci ne za su taimaka mana mu fahimci abin da ke Littafi Mai Tsarki? (b) Me ya sa muke nazarin waɗannan koyarwa a yanzu? (c) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
3 Babu shakka, mun san abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da nufin Allah ga duniya da ‘yan Adam da kuma aikin da Yesu Kristi zai yi don a yi nufin Allah. Waɗannan koyarwar suna da muhimmanci sosai kuma wataƙila suna cikin abubuwa na farko da muka koya sa’ad da muka fara nazarin Kalmar Allah. Ƙari ga haka, muna so mu taimaka wa mutane su san waɗannan koyarwa masu muhimmanci. Yanzu da muke nazarin wannan talifin, muna ƙoƙari mu gayyaci mutane da yawa don su halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu. (Luk. 22:19, 20) Waɗanda suka halarci taron za su koyi abubuwa da yawa game da nufin Allah. Saboda haka, a waɗannan ‘yan kwanaki da suka rage kafin wannan taron, ya dace mu yi tunanin tambayoyi da za mu yi wa ɗalibanmu da wasu don su san muhimmancin taron nan. Za mu tattauna tambayoyi uku: Mene ne nufin Allah na asali ga duniya da kuma ‘yan Adam? Mene ne ya sa nufinsa bai cika ba? Kuma me ya sa hadayar fansa da Yesu ya ba da ne za ta taimaka wajen cim ma nufin nan?
MENE NE NUFIN JEHOBAH NA ASALI?
4. Ta yaya halittu suke nuna ɗaukakar Jehobah?
4 Jehobah Mahalicci ne mai yin abubuwa masu ban al’ajabi kuma dukan abubuwan da ya halitta suna da ban sha’awa sosai. (Far. 1:31; Irm. 10:12) Mene ne za mu iya koya a yadda abubuwan da Allah ya halitta suke da kyau da kuma tsari? A lokacin da muke kallon halittu, dukan abubuwan da Jehobah ya halitta suna da gwanin kyau kuma dukansu suna da amfani. Dukanmu muna mamaki game da ƙwayoyin halitta na jiki da yadda jarirai suke ko kuma yadda rana take faɗuwa, ko ba haka ba? Waɗannan halittun suna burge mu don an halicce mu da sanin abubuwan da suke da ban sha’awa sosai.—Karanta Zabura 19:1; 104:24.
5. Ta yaya Jehobah ya tabbata cewa dukan abubuwan da ya halitta suna aiki bisa tsari?
5 Kamar yadda muka gani, dukan halittun Jehobah suna da iyaka. Ya kafa dokoki na halittu da na ɗabi’a don ya tabbata cewa dukan abubuwa sun kasance da tsari. (Zab. 19:7-9) Saboda haka, dukan abubuwan da ke sama da ƙasa suna da aikinsu. Alal misali, maganaɗisun ƙasa shi ne yake sa mu samu iskar da muke shaƙa a duniya. Idan babu shi, duk ruwan da ke tekuna zai yi sama. Kuma yana sa dukan abubuwan da ke duniya su kasance da tsari. Dukan halittu, har da ‘yan Adam suna da iyaka a abubuwan da suke yi. Hakika, yadda halittu suke da tsari ya nuna cewa akwai dalilin da ya sa Allah ya halicci duniya da kuma mutane. Muna iya koya wa mutane game da wanda ya sa dukan abubuwan nan suka kasance da tsari sa’ad da muke wa’azi.—R. Yoh. 4:11.
6, 7. Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya ba Adamu da Hauwa’u?
6 Abin da ya sa Jehobah ya halicci mutane shi ne don su yi rayuwa har abada a duniya. (Far. 1:28; Zab. 37:29) Ya ba Adamu da Hauwa’u abubuwa dabam-dabam da suka taimaka musu su ji daɗin rayuwa a duniya. (Karanta Yaƙub 1:17.) Jehobah ya ba su ‘yanci su yi abin da suke so. Ban da haka, ya sa su iya yin tunani, su riƙa ƙaunar mutane kuma su ƙulla abota da juna. Mahaliccin ya yi magana da Adamu kuma ya ba shi dokokin da zai riƙa bi. Adamu ya kuma koyi yadda zai biya bukatunsa da yadda zai kula da dabobbi da kuma inda yake zama. (Far. 2:15-17, 19, 20) Ƙari ga haka, Jehobah ya halicce Adamu da Hauwa’u su riƙa sanin ɗanɗanon abinci da harshensu, ya ba su idanu da hannu da hanci da kuma kunne don su riƙa yin abubuwa. Hakan zai sa su ji daɗin gidansu a Aljanna. Adamu da Hauwa’u za su ji daɗin aikinsu kuma su riƙa koyan abubuwa har abada.
7 Ban da waɗannan abubuwa, mene ne kuma nufin Allah? Jehobah ya halicci Adamu da Hauwa’u don su iya haifan yara kamiltattu. Ƙari ga haka, Allah yana so yaransu su haifi yara, har sai mutane sun cika duniya. Ya so Adamu da Hauwa’u da dukan iyaye a duniya su riƙa ƙaunar yaransu yadda Jehobah yake ƙaunar mutane. Ban da haka ma, Allah ya yi wa mutane kyautar duniya da dukan abubuwan da ke cikinta. Kuma ya so su yi rayuwa a cikinta har abada.—Zab. 115:16.
ME YA SA NUFINSA BAI CIKA BA?
8. Me ya sa aka ba da dokar da ke littafin Farawa 2:16, 17?
8 Nufin Allah bai cika yadda yake so ba. Me ya sa? Jehobah ya ba Adamu da Hauwa’u wata doka mai sauƙi don su fahimci cewa akwai wasu abubuwan da bai kamata su riƙa yi ba. Ya ce: “An yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Far. 2:16, 17) Adamu da Hauwa’u sun fahimci wannan dokar sosai kuma ba zai yi musu wuya su bi ta ba. Domin suna da abubuwa da yawa da za su riƙa ci.
9, 10. (a) Wace ƙarya ce Shaiɗan ya yi a kan Jehobah? (b) Mene ne Adamu da Hauwa’u suka tsai da shawara za su yi? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)
9 Shaiɗan ya yi amfani da maciji ya ruɗi Hauwa’u ta yi wa Jehobah rashin biyayya. (Karanta Farawa 3:1-5; R. Yoh. 12:9) Shaiɗan yana son ya nuna cewa Allah azzalumi ne da yake bai yarda mutane su “ci dukan itatuwa na gona ba.” Kamar dai yana cewa: ‘Kina nufin cewa ba za ki iya yin abin da kike so ba?’ Bayan haka, sai ya yi ƙarya cewa: “Ba lallai za ku mutu ba.” Sai ya yi ƙoƙari ya tabbatar wa Hauwa’u cewa bai kamata ta saurari Allah ba, ya ce: “Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su buɗe.” Shaiɗan yana nufin cewa Jehobah ba ya son su ci ‘ya’yan itacen don yin hakan zai sa kansu ya waye. Ƙari ga haka, Shaiɗan ya yi ƙarya cewa: “Za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.”
10 Yanzu, Adamu da Hauwa’u ne za su yanke shawara a kan abin da za su yi. Shin za su yi wa Jehobah biyayya ko kuma za su saurari macijin? Sun tsai da shawarar su yi wa Allah rashin biyayya. Ta yin hakan, sun bi ra’ayin Shaiɗan kuma suka yi wa Jehobah tawaye. Sun ƙi Jehobah ya zama Ubansu kuma ta hakan sun ƙi sarautarsa.—Far. 3:6-13.
11. Me ya sa Jehobah bai yi shiru da tawayen da Adamu da Hauwa’u suka yi ba?
11 Adamu da Hauwa’u sun zama ajizai sa’ad da suka yi wa Jehobah tawaye. Ƙari ga haka, tawayensu ya sa Jehobah ya daina sha’ani da su don ‘idonsa ya fi gaban duban mugunta.’ Saboda haka, ‘bai iya kallon shiririta ba.’ (Hab. 1:13) Da a ce ya amince da abin da suka yi, da hakan zai shafi dukan halittu masu rai a sama da kuma duniya. Ban da haka ma, da a ce Allah bai yi kome game da zunubin da aka yi a Adnin ba, da hakan zai sa a daina amincewa da shi. Amma Jehobah ba ya karya dokokinsa. (Zab. 119:142) Saboda haka, ko da yake Adamu da Hauwa’u suna da ‘yancin zaɓan abin da za su yi, hakan bai ba su damar taka dokar Allah ba. Sun mutu kuma suka zama ƙasa da Allah ya halicce su da ita domin sun yi tawaye.—Far. 3:19.
12. Me ya faru da ‘ya’yan Adamu?
12 Adamu da Hauwa’u sun daina kasancewa cikin sashen iyalin Allah na sama da kuma duniya sa’ad da suka ci wannan ‘ya’yan itacen. Allah ya kore su daga Adnin, kuma ba su iya komawa ba. (Far. 3:23, 24) Sa’ad da Jehobah ya kore su sun sha wahala don zunubinsu. (Karanta Kubawar Shari’a 32:4, 5.) ‘Yan Adam ba sa iya nuna halayen Allah sosai don sun zama ajizai. Ban da haka, Adamu ya rasa rayuwa mai kyau kuma ya sa yaransu suka gāji ajizanci da zunubi da kuma mutuwa. (Rom. 5:12) Ya hana ‘ya’yansa begen yin rayuwa har abada. Ƙari ga haka, Adamu da Hauwa’u ba su haifi yara kamiltattu ba kuma yaransu ba su iya yin hakan ba. Bayan da Shaiɗan ya sa Adamu da Hauwa’u suka daina bauta wa Allah, ya ci gaba da yaudarar mutane har wa yau.—Yoh. 8:44.
MENE NE FANSA TA CIM MA?
13. Mene ne Jehobah yake son mutane su yi?
13 Amma har ila Allah yana ƙaunar ‘yan Adam. Ko da yake Adamu da Hauwa’u sun yi tawaye, Jehobah yana son mutane su zama aminansa. Ba ya son kowa ya mutu. (2 Bit. 3:9) Saboda haka, bayan abin da ya faru a Adnin, Allah ya yi shirin da zai taimaka wa ‘yan Adam su soma abota da shi kuma. Ta yaya Jehobah ya cim ma wannan ba tare da saɓa wa ƙa’idodinsa ba?
14. (a) Bisa ga Yohanna 3:16, wane tanadi ne Allah ya yi don ya sa ‘yan Adam su zama aminansa? (b) Wace tambaya ce za mu iya tattaunawa da waɗanda suke son saƙonmu?
14 Karanta Yohanna 3:16. Mutane da yawa da muka gayyata don su halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu sun san wannan ayar sosai. Amma tambayar ita ce, Ta yaya hadaya da Yesu ya yi ta sa zai yiwu ‘yan Adam su riƙa rayuwa har abada? Kamfen don Tuna da Mutuwar Yesu da muke yi, da taron Tuna da Mutuwar Yesu da kuma komawa don mu ziyarci waɗanda suka halarci taro zai ba mu damar taimaka wa mutane su san amsar tambayar nan mai muhimmanci. Irin waɗannan mutane za su yi farin ciki sa’ad da suka soma fahimtar yadda Jehobah ya nuna yana ƙaunarmu da kuma hikimarsa sa’ad da ya yi tanadin fansa. Waɗanne abubuwa game da fansa za mu bayyana?
15. Ta yaya Yesu ya bambanta da Adamu?
15 Jehobah ya kawo ɗan Adam kamiltacce da zai iya mana tanadin fansa. Wannan kamiltaccen yana bukatar ya kasance da aminci ga Jehobah kuma ya kasance a shirye ya ba da ransa a madadin dukan mutane. (Rom. 5:17-19) Jehobah ya ƙaurar da ran halittarsa na farko daga sama zuwa duniya. (Yoh. 1:14) Ta hakan, Yesu ya zama kamiltacce kamar yadda Adamu yake a dā. Yesu bai bi misalin Adamu ba don ya yi rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin da Jehobah ya tsara wa kamiltaccen mutum. Ko a lokacin da ya fuskanci jaraba mai tsanani, Yesu bai yi zunubi ba kuma bai taka dokar Allah ba.
16. Me ya sa fansa ta zama kyauta mai tamani?
16 Da yake Yesu kamiltacce ne, ya ceci ‘yan Adam daga zunubi da mutuwa don ya mutu a madadinsu. Ya yi dukan abubuwan da ya kamata Adamu ya yi a matsayinsa na kamiltacce, ya kasance da aminci kuma ya yi wa Allah biyayya. (1 Tim. 2:6) Hadayar fansa da Yesu ya ba da za ta sa dukan mutane su yi rayuwa har abada. (Mat. 20:28) Hakika, fansa ce za ta sa Allah ya cim ma nufinsa na asali ga ‘yan Adam da duniya. (2 Kor. 1:19, 20) Fansa ta sa dukan ‘yan Adam su kasance da begen samun rai na har abada.
JEHOBAH YA BA MU DAMAR KOMOWA GARE SHI
17. Mene ne fansa ta cim ma?
17 Jehobah ya yi sadaukarwa sosai sa’ad da ya yi tanadin fansa. (1 Bit. 1:19) Yana ƙaunar ‘yan Adam sosai shi ya sa ya ba da Ɗansa makaɗaici ya mutu a madadinsu. (1 Yoh. 4:9, 10) Ma’ana, Yesu ya zama ainihin Ubanmu maimakon Adamu. (1 Kor. 15:45) Ta wurin yin hakan, Yesu ya ba mu damar samun rai na har abada da kuma kasancewa cikin iyalin Allah. Hakika, bisa ga hadayar Yesu, Jehobah ya amince ‘yan Adam su dawo cikin iyalinsa ba tare da ya taka dokokinsa ba. Ƙari ga haka, abin ƙarfafa ne yin tunanin lokacin da dukan ‘yan Adam masu aminci za su zama kamiltattu. Iyalinsa na sama da duniya za su kasance da haɗin kai sosai. A lokacin ne za mu zama ‘ya’yan Allah da gaske.—Rom. 8:21.
18. A wane lokaci ne Jehobah zai zama “kome da kome”?
18 Ko da yake Shaiɗan ya yi tawaye, hakan bai hana Jehobah ƙaunar ‘yan Adam ba kuma bai hana mutane kasancewa da aminci ga Jehobah ba. Don fansa da Jehobah ya yi tanadinsa, zai taimaka wa dukan yaransa su zama masu adalci. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance sa’ad da kowane mutum wanda ya amince da ‘Ɗan kuma yana ba da gaskiya gare shi,’ zai sami rai na har abada. (Yoh. 6:40) Tun da yake Jehobah mai hikima ne sosai kuma yana ƙaunar mutane, zai sa su zama kamiltattu kamar yadda ya so a dā. A lokacin, Jehobah zai zama musu “kome da kome.”—1 Kor. 15:28, Littafi Mai Tsarki.
19. (a) Mene ne ya kamata tanadin fansa da aka yi zai sa mu yi? (Ka duba akwatin nan “Bari Mu Ci Gaba da Neman Masu Son Jin Wa’azi.”) (b) Wane fanni na fansa ne za mu tattauna a talifi na gaba?
19 Idan muna godiya don fansar, ya kamata hakan ya sa mu yi iya ƙoƙarinmu mu wajen taimaka ma wasu su san cewa za su iya amfana daga wannan kyauta mai tamani. Ya kamata mutane su san cewa ta hanyar fansa ce Jehobah ya sa dukan mutane su kasance da begen yin rayuwa har abada. Amma fansa ta cim ma wasu abubuwa fiye da hakan. A talifi na gaba, za a tattauna yadda hadayar da Yesu ya ba da ta bayyana batutuwa da Shaiɗan ya ta da a gonar Adnin.