RAYUWAR KIRISTA
Ta Yaya ’Yan’uwa Mata Za Su Biɗi Ƙarin Aiki?
’Yan’uwa mata suna taimakawa sosai a ayyukan da suka shafin wa’azi game da Mulkin Allah. (Za 68:11) Suna nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Su suka fi yawa a cikin masu hidimar majagaba na kullum. ’Yan’uwa mata da yawa suna hidima a Bethel, da wa’azi a ƙasashen waje, da aikin gine-gine na gida da na ƙasashen waje, da kuma fassara. ’Yan’uwa mata da suka manyanta suna ƙarfafa iyalinsu da kuma ikilisiya. (K. Ma 14:1) Ko da yake ’yan’uwa mata ba za su iya zama dattawa ko bayi masu hidima ba, za su iya kafa maƙasudai. A waɗanne hanyoyi ne ’yar’uwa mata za su iya biɗan ƙarin aiki?
Ku riƙa nuna halayen masu kyau da za su ƙarfafa dangantakarku da Jehobah.—1Ti 3:11; 1Bi 3:3-6
Ku taimaka wa ’yan’uwa mata da ba su manyanta ba tukuna.—Tit 2:3-5
Ku riƙa yin wa’azi sosai kuma ku inganta yadda kuke yin wa’azi
Ku koyi wani yare
Ku je hidima a wuraren da ake bukatar masu shela
Ku cika fom na yin hidima a Bethel ko kuma taimaka da gina wuraren ibada
Ku cika fom na Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki
KU KALLI BIDIYON NAN ‘MATA MASU HIDIMAR UBANGIJI DA ƘWAZO,’ SAI KU AMSA TAMBAYA NA GABA:
Ta yaya kalaman ’yan’uwa matan nan suka ƙarfafa ka?