Kana Daraja Mata Yadda Jehobah Yake Yi?
MUNA da gatan yin aiki tare da ꞌyanꞌuwa mata da yawa masu aminci. Kuma muna gode wa ꞌyanꞌuwa matan nan don yadda suke ma Jehobah aiki da ƙwazo!a Don haka, ꞌyanꞌuwa maza, muna so mu riƙa nuna musu alheri da yi musu adalci da kuma daraja su. Amma da yake mu ajizai ne, a wasu lokuta yin hakan zai yi mana wuya. Akwai wasu ꞌyanꞌuwa da yin hakan ya fi yi musu wuya.
Wasu sun taso a inda maza ba sa ɗaukan mata da muhimmanci. Alal misali, wani mai kula da daꞌira mai suna Hans da ke zama a ƙasar Bolibiya ya ce: “A wasu alꞌadu, wasu maza suna ganin kamar sun fi mata daraja, don haka sukan rena su.” Wani dattijo mai suna Shengxian a ƙasar Taiwan ya ce: “A inda nake zama, maza suna ganin cewa bai kamata mata su sa baki a harkarsu ba. Idan namiji ya faɗi raꞌayin mace game da wani abu, abokansa za su yi masa ganin rago.” Wasu maza kuma sukan rena mata a wasu hanyoyi dabam. Alal misali, sukan yi maganganun da ke ƙasƙantar da mata don su ba mutane dariya.
Abin farin ciki shi ne, ko da wane irin hali ne mutum yake da shi saboda alꞌadarsa zai iya canjawa. Zai iya koyan cewa mata ma suna da daraja kamar maza. (Afis. 4:22-24) Zai iya yin hakan idan ya yi koyi da Jehobah. A wannan talifin, za mu ga yadda Jehobah yake bi da mata, da yadda ꞌyanꞌuwa maza za su iya bi da mata kamar yadda Jehobah yake yi, da kuma yadda dattawa za su iya kafa misali mai kyau wajen daraja mata.
YAYA JEHOBAH YAKE BI DA MATA?
Jehobah ne ya fi kafa misali mai kyau a kan yadda ya kamata a bi da mata. Shi Uba ne da ke ƙaunar ꞌyaꞌyansa sosai. (Yoh. 3:16) ꞌYanꞌuwanmu mata ꞌyaꞌyansa ne da yake ƙauna sosai. Ga wasu hanyoyi da Jehobah ya nuna cewa yana daraja mata.
Ba ya nuna musu bambanci. Jehobah ya halicci maza da mata a kamanninsa. (Far. 1:27) Bai ba ma maza baiwa ko kuma ilimi fiye da mata ba, kuma ba ya son maza fiye da mata. (2 Tar. 19:7) Ya halicci maza da mata a hanyar da dukansu za su iya fahimtar gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, kuma su yi koyi da halayensa masu kyau. Jehobah yana ƙaunar maza da mata da suke ba da gaskiya gare shi, kuma ya ba su begen yin rayuwa a sama ko kuma a nan duniya. (2 Bit. 1:1) Hakika, Jehobah ba ya nuna wa mata bambanci.
Yana saurarar su. Jehobah ya damu da mata kuma yana so ya san yadda suke ji da kuma matsalar da suke fuskanta. Alal misali, ya saurari adduꞌar Rahila da kuma Hannatu, kuma ya amsa musu. (Far. 30:22; 1 Sam. 1:10, 11, 19, 20) Ya kuma sa marubutan Littafi Mai Tsarki su rubuta labarin maza da suka saurari mata. Alal misali, Ibrahim ya bi umurnin Jehobah cewa ya saurari matarsa, Saratu. (Far. 21:12-14) Sarki Dauda ya saurari Abigail. Ya ma ce Jehobah ne ya aiko ta ta yi masa magana. (1 Sam. 25:32-35) Yesu da yake yin koyi da halayen Ubansa sosai, shi ma ya saurari mamarsa, Maryamu. (Yoh. 2:3-10) Misalan nan sun nuna mana cewa hanya ɗaya da Jehobah yake daraja mata shi ne ta wajen saurarar su.
Ya yarda da su. Alal misali, Jehobah ya yarda da Hauwaꞌu shi ya sa ya ba ta aikin kula da abubuwan da ya yi a duniya tare da Adamu. (Far. 1:28) Abin da Jehobah ya yi ya nuna cewa bai ɗauki Adamu da muhimmanci fiye da ita ba. Amma ya ɗauke ta a matsayin mai taimako ga Adamu. Jehobah ya kuma ba wa annabiya Deborah da Hulda aikin ba da shawara ga mutanensa, har da wani alƙali da wani sarki, domin ya yarda da su. (Alƙa. 4:4-9; 2 Sar. 22:14-20) A yau ma, Jehobah ya yarda da ꞌyanꞌuwa mata kuma ya ba su aikin yi. Waɗannan ꞌyanꞌuwa masu bangaskiya suna aiki a matsayin masu shela da majagaba da kuma masu waꞌazi a ƙasashen waje. Suna taimaka wajen tsara da gina Majamiꞌar Mulki da ofisoshinmu, kuma suna kula da su. Wasunsu suna aiki a Bethel, wasu kuma suna aiki a ofisoshin fassara. Waɗannan mata suna kamar babbar runduna da Jehobah yake amfani da su don ya cim ma nufinsa. (Zab. 68:11) Hakika, Jehobah ba ya ɗaukan mata a matsayin ragwaye da ba za su iya yin aiki ba.
YAYA ꞌYANꞌUWA MAZA ZA SU KOYI BI DA MATA YADDA JEHOBAH YAKE YI?
ꞌYanꞌuwa maza, don mu san ko muna bi da mata yadda Jehobah yake yi, muna bukatar mu bincika yadda muke tunani da abubuwan da muke yi. Muna bukatar taimako don mu iya yin hakan. Likita zai iya amfani da naꞌura don ya san ko zuciyar mutum tana aiki da kyau ko ba ta aiki da kyau. Haka ma, abokanmu ko kuma Kalmar Allah za su iya taimaka mana mu san ko yadda muke ɗaukan mata yana faranta ran Jehobah ko aꞌa. Me za mu yi don mu sami taimakon?
Ka tambayi amininka. (K. Mag. 18:17) Zai dace mu tambayi wani amininmu mai alheri da sanin yakamata cewa: “Ya kake ganin yadda nake bi da mata? Suna ganin cewa ina daraja su kuwa? Akwai abin da zan iya yi don in ƙara daraja su?” Idan abokinka ya gaya maka hanyoyin da kake bukatar gyara, kada ka soma ba da hujjoji. A maimakon haka, ka kasance a shirye don ka yi gyara.
Ka yi nazarin Kalmar Allah. Abin da zai fi taimaka mana mu san ko muna bi da mata yadda ya dace shi ne, mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki don mu bincika tunaninmu da kuma abubuwan da muke yi. (Ibran. 4:12) Yayin da muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki, za mu koya game da maza da suka daraja mata da waɗanda ba su yi hakan ba. Za mu iya gwada yadda suka bi da mata da yadda mu muke hakan. Ƙari ga haka, idan muka duba Nassosi dabam-dabam, hakan zai taimaka mana mu guji yin tunani cewa Littafi Mai Tsarki yana goyon bayan raꞌayi marar kyau game da mata. Alal misali, 1 Bitrus 3:7 ta ce maza su girmama mata don mata ‘ba su da ƙarfi kamarsu.’b Shin hakan yana nufin cewa mata ba su da ilimi kuma ba za su iya yin abubuwa kamar maza ba ne? Ba haka ba ne, ko kaɗan! Ka kwatanta abin da Bitrus ya faɗa da abin da ke Galatiyawa 3:26-29, inda aka nuna cewa Jehobah ya zaɓi mata da maza su yi sarauta tare da Yesu a sama. Idan mun karanta Kalmar Allah kuma muka tambayi amininmu ya gaya mana yadda muke bi da mata, za mu san yadda za mu bi da mata a hanyar da ta dace.
YADDA DATTAWA SUKE DARAJA ꞌYANꞌUWA MATA
ꞌYanꞌuwa maza a ikilisiya za su iya bi da ꞌyanꞌuwa mata a hanyar da ta dace idan suna yin koyi da dattawa. Yaya dattawa suke kafa misali mai kyau wajen daraja mata? Ga wasu hanyoyi da suke yin hakan.
Suna yaba ma ꞌyanꞌuwa mata. Manzo Bulus ya nuna wa dattawa hanya mai kyau da za su iya yin hakan. A wasiƙar da ya aika wa ikilisiyar Roma, ya yaba ma ꞌyanꞌuwa mata da yawa kuma kowa ya ji hakan. (Rom. 16:12) Ka yi tunanin yadda ꞌyanꞌuwa matan nan suka yi murna sosai saꞌad da ake karanta wasiƙar Bulus ga ikilisiyar. Haka ma, dattawa suna yaba ma ꞌyanꞌuwa mata sosai domin halaye masu kyau da suke da shi da kuma aikin da suke yi wa Jehobah. Hakan yana sa ꞌyanꞌuwa matan su san cewa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya suna ƙaunarsu kuma suna daraja su. Mai yiwuwa abin da ꞌyanꞌuwa matan suke bukata don su ci-gaba da bauta ma Jehobah da aminci shi ne ƙarfafa daga dattawa.—K. Mag. 15:23.
Saꞌad da dattawa suke yaba ma ꞌyanꞌuwa mata, zai dace su faɗi gaskiya kuma su faɗi dalilin da ya sa suke yaba musu. Me ya sa? Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Jessica ta ce: “Yana da kyau idan dattawa suka gaya wa ꞌyarꞌuwa cewa, ‘Sannu da aiki.’ Amma mun fi jin daɗi idan ɗanꞌuwa ya yaba mana domin takamammen abin da muka yi, kamar koya wa yaranmu su yi shiru a taro ko kuma sadaukarwa da muka yi don mu kawo ɗalibanmu zuwa taro.” Idan dattawa suka yaba wa ꞌyanꞌuwa mata don takamammen abin da suka yi, hakan zai sa ꞌyanꞌuwa mata su ji cewa suna da amfani da kuma daraja a cikin ikilisiya.
Suna saurarar ꞌyanꞌuwa mata. Dattawa masu sauƙin kai sun san cewa ba su fi kowa sanin abubuwa ba. Irin dattawan nan sukan tambayi raꞌayin ꞌyanꞌuwa mata game da wani abu, kuma suna saurara da kyau yayin da ꞌyanꞌuwa matan suke bayyana raꞌayinsu. Ta yin hakan, dattawan suna ƙarfafa mata kuma su ma suna amfana. Ta yaya? Wani ɗanꞌuwa mai suna Gerardo da ke hidima a Bethel ya ce: “Na lura cewa neman shawarar mata kafin in yi aiki, yana taimaka min in ƙara yin aikin da kyau. A yawancin lokaci, matan sun daɗe suna aikin fiye da ꞌyanꞌuwa maza.” A ikilisiya, ꞌyanꞌuwa mata da yawa suna yin hidimar majagaba, don haka sun san mutanen da ke a yankin da suke waꞌazi sosai. Wani dattijo mai suna Bryan ya ce: “ꞌYanꞌuwanmu mata suna da halaye masu kyau da kuma ƙwarewa da ƙungiyarmu take bukata. Don haka, ka amfana daga ƙwarewarsu.”
Dattawa masu hikima ba sa watsi da shawarar mata. Me ya sa? Wani dattijo mai suna Edward ya ce: “Shawarar ꞌyarꞌuwa za ta iya taimaka wa mutum ya ƙara fahimtar wani batu da kyau, kuma raꞌayinta zai taimaka masa ya san yadda wasu suke ji.” (K. Mag. 1:5) Ko da dattijon ba zai iya bin shawarar da ꞌyarꞌuwar ta bayar ba, zai dace ya gode mata don shawarar da ta bayar.
Suna koyar da ꞌyanꞌuwa mata. Dattawa masu hikima suna neman zarafi da za su koyar da ꞌyanꞌuwa mata. Alal misali, za su iya koya wa ꞌyanꞌuwa mata yadda za su gudanar da taron fita waꞌazi don su iya yin hakan idan babu ɗanꞌuwa da ya yi baftisma. Za su kuma iya koya musu yadda ake gini da kuma kula da gine-ginen ƙungiyarmu. A Bethel, ꞌyanꞌuwa maza da ke ja-goranci suna koya wa mata yadda za su yi ayyuka dabam-dabam. Hakan ya haɗa da kula da gini, da sayayya, da kula da harkokin kuɗi, da tsara wasu ayyukan kwamfuta da dai sauransu. Idan dattawa sun horar da mata, za su nuna cewa sun yarda da su kuma sun san cewa za su iya yin aikin da aka ba su.
Mata da yawa sun yi amfani da abin da dattawa suka koya musu don su amfani wasu. Alal misali, wasu mata da suke aiki a sashen gine-gine sun yi amfani da abin da suka koya wajen sake gina gidajen ꞌyanꞌuwa da balaꞌi ya rusa. Wasu ꞌyanꞌuwa mata kuma da aka koya musu yadda ake waꞌazi a inda jamaꞌa suke, sun yi amfani da darasin wajen koyar da wasu ꞌyanꞌuwa mata don su ma su iya yin hakan. Yaya ꞌyanꞌuwa mata suke ji game da dattawan da suke koyar da su? Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Jennifer ta ce: “Saꞌad da na taimaka wajen gina Majamiꞌar Mulki, wani dattijo ya ɗau lokaci sosai ya horar da ni. Ya lura da aikin da na yi kuma ya yaba min. Na ji daɗin yin aiki da shi domin ya girmama ni kuma ya nuna min cewa ina da daraja.”
MUHIMMANCIN ƊAUKAN MATA A IKILISIYA KAMAR ꞌYANꞌUWANMU
Muna ƙaunar mata masu aminci kamar yadda Jehobah yake ƙaunar su! Shi ya sa muke ɗaukan su a matsayin ꞌyan iyalinmu. (1 Tim. 5:1, 2) Muna ƙaunar su kuma muna jin daɗin yin aiki tare da su. Kuma muna farin ciki sosai idan suka ga cewa muna ƙaunar su da kuma taimaka musu. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Vanessa ta ce: “Ina godiya sosai ga Jehobah don ya jawo ni cikin ƙungiyarsa, kuma ya ba ni ꞌyanꞌuwa maza da suke ƙarfafa ni.” Wata ꞌyarꞌuwa a ƙasar Taiwan ta ce: “Ina farin ciki domin yadda Jehobah da ƙungiyarsa suna ɗaukan mata da daraja sosai kuma ba sa wasa da yadda suke ji. Hakan yana ƙarfafa bangaskiyata kuma yana sa in daɗa nuna godiya don gatan da na samu na kasancewa a ƙungiyar Jehobah.”
Babu shakka Jehobah zai yi farin ciki sosai idan ya ga yadda maza masu aminci suke iya ƙoƙarinsu don su daraja mata yadda yake yi! (K. Mag. 27:11) Wani ɗanꞌuwa a ƙasar Sukotilan mai suna Benjamin ya ce, “Mutane a duniya ba sa daraja mata sam-sam. Don haka, a duk lokacin da ꞌyanꞌuwanmu mata suka zo Majamiꞌar Mulki muna so su san cewa muna ƙaunar su kuma muna daraja su.” Bari dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu mu bi gurbin Jehobah, ta wajen nuna wa ꞌyanꞌuwanmu mata ƙauna da daraja domin sun cancanci hakan.—Rom. 12:10.
a “ꞌYanꞌuwa mata” da aka ambata a wannan talifin, suna nufin ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci.
b Don ƙarin bayani a kan abin da ake nufi da furucin nan “ba su da ƙarfi,” ka duba talifin nan mai jigo “The Value of ‘a Weaker Vessel’” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu 2006, da kuma “Shawara Mai Kyau ga Maꞌaurata” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris 2005.