TALIFIN NAZARI NA 35
Ka Riƙa Daraja Kowa a Ikilisiya
“Ba dama ido ya ce wa hannu, ‘Ba ruwana da kai,’ ko kuwa kai ya ce wa ƙafafu, ‘Ba ruwana da ku.’”—1 KOR. 12:21.
WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Mene ne Jehobah ya ba kowane bawansa?
JEHOBAH ya ba kowane bawansa aiki a ikilisiya. Ko da yake ayyukan da muke yi sun bambanta, kowannenmu yana da amfani kuma muna bukatar juna. Manzo Bulus ya taimaka mana mu koyi wannan darasi mai muhimmanci. Yaya ya yi hakan?
2. Kamar yadda Afisawa 4:16 ta nuna, me ya sa muke bukatar mu riƙa daraja juna da kuma aiki da haɗin kai?
2 Kamar yadda aka ambata a ayar da aka ɗauko jigon wannan talifin, Bulus ya nuna cewa babu wani a cikinmu da zai gaya wa wani bawan Jehobah cewa: “Ba ruwana da kai.” (1 Kor. 12:21) Idan muna so a yi zaman lafiya a ikilisiya, wajibi ne mu riƙa daraja juna kuma mu yi aiki tare. (Karanta Afisawa 4:16.) Idan muna aiki da haɗin kai, ’yan’uwa a ikilisiya za su ga cewa ana ƙaunar su kuma hakan zai ƙarfafa su.
3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna muna daraja ’yan’uwa a ikilisiya? A wannan talifin, za mu tattauna yadda dattawa za su riƙa daraja juna. Kuma za mu tattauna yadda dukanmu za mu riƙa daraja ’yan’uwa maza da mata da ba su da aure. A ƙarshe, za mu koya yadda za mu riƙa daraja waɗanda ba su iya yarenmu ba.
DATTAWA KU RIƘA DARAJA JUNA
4. Wace shawarar Bulus da ke Romawa 12:10 ce ya kamata dattawa su bi?
4 Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki don ya naɗa dattawa. Duk da haka, kowannensu yana da baiwa da iyawa dabam-dabam. (1 Kor. 12:17, 18) Bai daɗe da aka naɗa wasu dattawa ba, saboda haka, ba su ƙware ba sosai. Wasu kuma ba sa iya yin wasu ayyuka don sun tsufa ko kuma suna rashin lafiya. Duk da haka, bai kamata dattijo ya yi tunanin cewa waɗannan dattawa ba su da amfani ba. A maimakon haka, ya kamata kowanne dattijo ya bi shawarar Bulus da ke littafin Romawa 12:10.—Karanta.
5. Ta yaya dattawa za su nuna cewa suna daraja sauran dattawa, kuma me ya sa ya kamata su yi hakan?
5 Dattawa suna nuna cewa suna daraja juna ta wajen saurarar juna sosai. Hakan yana da muhimmanci musamman sa’ad da ake tattauna wani batu mai muhimmanci a taron dattawa. Me ya sa? A Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 1988, an faɗa cewa: “Ya kamata dattawa su fahimci cewa Yesu zai iya yin amfani da ruhu mai tsarki don ya taimaka wa kowane dattijo ya ambata ƙa’idar Littafi Mai Tsarki da za ta taimaka wa dattawa su san shawarar da za su yanke a wani yanayi. (A. M. 15:6-15) Ruhu mai tsarki yana iya taimaka wa dukan dattawa a ikilisiya, ba mutum ɗaya kawai ba.”
6. Mene ne zai taimaka wa dattawa su yi aiki da haɗin kai, kuma ta yaya ’yan’uwa za su amfana sa’ad da suka yi hakan?
6 Dattijon da ke daraja sauran dattawa ba zai zama na farko da zai yi magana a taron dattawa a kowane lokaci ba. Ba ya ganin cewa ra’ayinsa ne ya fi dacewa. A maimakon haka, yana faɗin ra’ayinsa da sauƙin kai. Kuma yana saurarar ra’ayin sauran dattawa. Abin da ya fi muhimmanci ma shi ne, yana a shirye ya ambata abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma yana bin ja-gorancin “bawan nan mai aminci, mai hikima.” (Mat. 24:45-47) Yayin da dattawa suke nuna wa juna ƙauna da kuma daraja sa’ad da suke tattaunawa, ruhu mai tsarki zai yi musu ja-goranci kuma ya sa su tsai da shawarwari da za su amfani ’yan’uwa a ikilisiya.—Yaƙ. 3:17, 18.
KU RIƘA DARAJA ’YAN’UWA MARASA AURE
7. Yaya Yesu ya ɗauki waɗanda ba su da aure?
7 A ikilisiyoyi a yau, akwai ma’aurata da kuma iyalai. Duk da haka, akwai ’yan’uwa maza da mata da yawa da ba su da aure. Yaya ya kamata mu riƙa ɗaukan waɗannan ’yan’uwa? Ya kamata mu yi koyi da yadda Yesu ya ɗauke su. Yesu bai yi aure ba, amma ya mai da hankali ga yin aikin da aka ba shi. Bai taɓa koyar cewa ya kamata mutum ya yi aure ko kuma kada ya yi aure ba. Amma ya ce wasu Kiristoci ba za su so yin aure ba. (Mat. 19:11, 12) Yesu ya daraja waɗanda ba su yi aure ba. Bai rena waɗanda ba su yi aure ba ko kuma ya riƙa ganin cewa marasa aure ba sa jin daɗin rayuwa.
8. Kamar yadda 1 Korantiyawa 7:7-9 suka nuna, mene ne Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su yi la’akari da shi?
8 Kamar Yesu, manzo Bulus bai yi aure ba. Bulus bai taɓa koyar cewa bai dace Kirista ya yi aure ba, don ya san cewa wannan shawara ce da mutum zai tsai da da kansa. Duk da haka, Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su yi tunani ko za su iya zama ba su yi aure ba. (Karanta 1 Korintiyawa 7:7-9.) Bai rena waɗanda ba su yi aure ba. Ya zaɓi Timoti da ba shi da aure ya yi ayyuka masu muhimmanci.b (Filib. 2:19-22) Saboda haka, ba zai dace ba a yi tunani cewa wani ɗan’uwa ya cancanta yin wata hidima ko bai cancanta ba don ya yi aure ko don bai yi aure ba.—1 Kor. 7:32-35, 38.
9. Mene ne za mu iya cewa game da aure da kuma ƙin yin hakan?
9 Yesu da Bulus ba su koyar cewa wajibi ne Kiristoci su yi aure ko kuma kada su yi hakan ba. To mene ne za mu iya cewa game da aure da ƙin yin hakan? Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 2012, ta ba da amsa mai kyau cewa: “Hakika, aure da ƙin yin aure baiwa ce daga Allah. . . . Jehobah ba ya ganin cewa ya kamata waɗanda ba su yi aure ba su riƙa jin kunya ko kuma baƙin ciki.” Saboda haka, ya kamata mu riƙa daraja ’yan’uwa maza da mata da ba su yi aure ba.
10. Ta yaya za mu daraja ’yan’uwa da ba su da aure?
10 Ta yaya za mu riƙa daraja waɗanda ba su yi aure ba? Ya kamata mu tuna cewa wasu ’yan’uwa ne suka zaɓa cewa ba za su yi aure ba. Wasu kuma za su so su yi aure, amma ba su samu wanda ya dace da su ba. Ban da haka, wasu kuma mijinsu ko matarsu ta rasu. Ko da mene ne dalilin, bai kamata waɗanda suke ikilisiya su soma tambayar ’yan’uwa da ba su yi aure ba dalilin da ya sa ba su yi hakan ba ko kuma mu ce za mu nemo musu mata ko miji. Hakika, wasu Kiristoci da ba su yi aure ba suna iya neman taimako. Amma idan ba su ce ka taimaka musu ba, za su ji kunya idan ka ce za ka nemo musu miji ko mata. (1 Tas. 4:11; 1 Tim. 5:13) Bari mu yi la’akari da furucin wasu ’yan’uwa maza da mata da ba su yi aure ba.
11-12. Ta yaya za mu iya sa waɗanda ba su yi aure ba sanyin gwiwa?
11 Wani ɗan’uwa mai kula da da’ira da ya ƙware a aikinsa yana ganin cewa ƙin yin aure yana da amfani sosai. Amma ya ce yana sa shi sanyin gwiwa sa’ad da ’yan’uwa da suke so su taimaka masa suka tambaye shi: “Me ya sa ba ka yi aure ba?” Wani ɗan’uwa kuma da ba shi da aure da ke hidima a wani reshen ofishinmu, ya ce: “A wasu lokuta, ’yan’uwa suna tunani cewa ya kamata su riƙa jin tausayin waɗanda ba su yi aure ba. Yin hakan zai sa ya zama kamar ƙin yin aure matsala ce ba baiwa ba ce.”
12 Wata ’yar’uwa da ba ta da aure da ke hidima a Bethel ta ce: “Wasu masu shela suna ganin cewa dukan waɗanda ba su yi aure ba suna neman wanda zai aure su ko kuma suna ganin cewa lokacin yin liyafa zarafi ne na neman miji ko mata. Akwai lokacin da na je yin aiki a wani wuri a ƙasarmu, kuma na halarci taro. ’Yar’uwa da nake zama a gidanta ta gaya mini cewa akwai ’yan’uwa maza biyu tsarana a ikilisiyarsu. Ta gaya mini cewa ba ƙoƙarin nema mini miji take yi ba. Amma da muka shiga Majami’ar Mulki, sai ta kai ni wurin ’yan’uwan nan. Hakan ya sa ni da ’yan’uwan kunya sosai.”
13. Waɗanne misalai ne suka ƙarfafa wata ’yar’uwa da ba ta da aure?
13 Wata ’yar’uwa kuma da ba ta yi aure ba da take hidima a Bethel ta ce: “Na san majagaba da ba su da aure da suka manyanta kuma sun kafa maƙasudan bauta wa Jehobah sosai. Suna a shirye su taimaka wa wasu kuma suna farin ciki. Suna taimaka wa ’yan’uwa sosai a ikilisiya. Sun kasance da ra’ayin da ya dace, ba sa ganin sun fi wasu don ba su yi aure ba kuma ba sa ganin ba za su yi farin ciki ba domin ba su da aure da kuma yara ba.” Kyaun kasancewa cikin ikilisiyar da ’yan’uwa suke daraja juna ke nan. Za ka san cewa ’yan’uwa ba sa jin tausayinka don ba ka yi aure ba ko kuma su yi kishinka. Ba sa yin banza da kai kuma ba sa ganin ka fi su. Za ka dai san cewa suna ƙaunar ka.
14. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja waɗanda ba su da aure?
14 ’Yan’uwanmu da ba su da aure za su yi farin ciki idan muna daraja su don halayensu masu kyau. Bai kamata muna jin tausayinsu domin ba su da aure ba. Maimakon mu riƙa jin tausayinsu, zai dace muna daraja su don amincinsu. Idan muka yi hakan, ’yan’uwanmu da ba su da aure ba za su taɓa tunanin cewa muna ce musu: “Ba ruwana da ku.” (1 Kor. 12:21) Maimakon haka, za su san cewa muna daraja su kuma muna farin cikin kasancewa tare da su a ikilisiya.
KA RIƘA DARAJA WAƊANDA BA SU IYA YARENKU SOSAI BA
15. Waɗanne canje-canje wasu suka yi don su daɗa ƙwazo a wa’azi?
15 A kwanan nan, ’yan’uwa da yawa suna kafa maƙasudin koyan wani yare don su yi wa mutane da yawa wa’azi. Hakan yana nufin cewa za su yi wasu canje-canje a rayuwarsu. Waɗannan ’yan’uwan sun bar ikilisiyar da ake yarensu domin su yi hidima a ikilisiyar da ake bukatar masu shela kuma ake wani yare. (A. M. 16:9) Sun tsai da wannan shawarar domin su bauta wa Jehobah. Suna taimaka wa ikilisiyar sosai ko da yake zai ɗau shekaru kafin su iya yaren sosai. Halayensu masu kyau yana ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya. Muna daraja waɗannan ’yan’uwa don sadaukarwa da suka yi!
16. Mene ne zai nuna ko ɗan’uwa ya cancanci zama dattijo ko kuma bawa mai hidima?
16 Bai kamata rukunin dattawa su ƙi naɗa ɗan’uwa dattijo ko bawa mai hidima don bai iya yaren da ake yi a ikilisiyar sosai ba. Ya kamata dattawa su yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don dubawa ko ɗan’uwan ya cancanci zama dattijo ko bawa mai hidima. Bai kamata su yanke shawara bisa yadda ya iya yaren da ake yi a ikilisiyar ba.—1 Tim. 3:1-10, 12, 13; Tit. 1:5-9.
17. Wace shawara ce ya kamata iyaye su tsai da sa’ad da suka koma wata ƙasa?
17 Wasu iyalai sun ƙaura zuwa wata ƙasa don su guji mawuyacin yanayi da ke ƙasarsu ko kuma su nemi aiki. Hakan zai sa yaransu su je makarantar da ake yaren ƙasar da suka koma. Wataƙila iyayen za su bukaci su koyi yaren don su sami aiki. Idan akwai ikilisiya ko rukuni da ake yarensu kuma fa? Wace ikilisiya ce ya kamata su riƙa halartan taro? Shin ikilisiyar da ake yaren ƙasar da suka koma ko kuma wadda ake yarensu?
18. Kamar yadda Galatiyawa 6:5 ta nuna, ta yaya za mu amince da shawarar da maigidan ya tsai da?
18 Wajibi ne maigida ya tsai da shawarar ikilisiyar da iyalinsa za su riƙa halartan taro. Da yake shi ne zai yanke wannan shawara, wajibi ne ya yi la’akari da abin da zai taimaka wa iyalinsa sosai. (Karanta Galatiyawa 6:5.) Bai kamata mu saka baki a shawarar da maigidan ya tsai da ba. Bari mu nuna mun amince da hakan ta wajen marabtar iyalin da kuma nuna musu ƙauna.—Rom. 15:7.
19. Mene ne ya kamata magidanta su yi tunani a kai kuma su yi addu’a game da shi?
19 Wasu iyalai kuma suna iya halartan taro a ikilisiyar da ake yarensu, amma yaran ba sa jin yaren sosai. Idan ikilisiyar tana wurin da ake yaren da yaran suke yi a makaranta, hakan yana iya sa ya yi wa yaran wuya su fahimci abin da ake yi a taro kuma ba za su samu ci gaba ba. Me ya sa? Domin yaran suna zuwa makaranta da ake yaren ƙasar ba yaren iyayensu ba. A irin wannan yanayin, ya kamata magidanta su yi tunani sosai kuma su yi addu’a don su san abin da ya kamata su yi don su taimaka wa yaransu su kusaci Jehobah da kuma mutanensa. Za su bukaci su koya wa yaransu yaren sosai ko kuma su koma ikilisiyar da ake yaren da yaransu za su fahimta. Ko da wace shawara ce maigidan ya tsai da, ya kamata ’yan’uwa da ke ikilisiyar da ya zaɓa iyalinsa su riƙa halartan taro su daraja iyalin kuma su ƙaunace su.
20. Ta yaya za mu nuna muna daraja ’yan’uwan da suke koyon wani yare?
20 Don dukan dalilan da muka tattauna a talifin nan, a ikilisiyoyi da yawa da akwai ’yan’uwa da suke fama su koyi sabon yare. Yana iya yi musu wuya su faɗi ra’ayinsu. Amma idan ba ma mai da hankali ga yadda suke yaren, za mu ga cewa suna ƙaunar Jehobah kuma suna so su bauta masa. Idan muka lura da halayen nan masu kyau, za mu riƙa daraja ’yan’uwa sosai. Ba za mu ce musu “ba ruwana da ku” ba, domin ba su iya yarenmu sosai ba.
MUNA DA DARAJA GA JEHOBAH
21-22. Wace gata ce muke da ita?
21 Muna godiya ga Jehobah domin ya ba kowannenmu aikin da za mu yi a ikilisiya. Kowa yana da daraja ga Jehobah da kuma ’yan’uwa ko da shi namiji ne ko ta mace, mai aure ko marar aure, tsoho ko matashi, ya iya wani yare sosai ko kuma bai iya ba.—Rom. 12:4, 5; Kol. 3:10, 11.
22 Bari mu ci gaba da yin amfani da darussa da yawa da muka koya daga kwatancin Bulus game da jikin ɗan Adam. Ta yin hakan, za mu nemi ƙarin hanyoyi da za mu ƙarfafa ’yan’uwanmu da daraja su da kuma nuna musu ƙauna.
WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna
a Bayin Jehobah sun fito daga wurare dabam-dabam kuma suna ayyuka dabam-dabam a ikilisiya. A wannan talifin, za mu ga dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu riƙa daraja kowa a cikin ikilisiya.
b Ba mu san ko Timoti ya yi aure daga baya ba.