TALIFIN NAZARI NA 30
Ka Nuna Godiya don Abubuwan da Jehobah Ya Ba Ka
“Gama da kaɗan ka sa ya gaza mala’iku, da daraja da girma kuma ka naɗa shi.”—ZAB. 8:5, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Me ke zuwa zuciyarmu idan muka yi tunani a kan abubuwan da Jehobah ya halitta?
IDAN muka yi tunani a kan abubuwan da Allah ya halitta a sama da ƙasa, za mu kasance da ra’ayi ɗaya da Dauda, marubucin zabura wanda ya tambayi Jehobah a cikin addu’a cewa: “Sa’ad da na duba sararin sama, aikin yatsunka, da wata da taurarin da ka kafa a wurarensu, sai na ce, ‘Mene ne mutum da ka damu da shi, ɗan Adam, har da ka kula da shi?” (Zab. 8:3, 4) Kamar yadda Dauda ya yi, mu ma za mu iya ganin ƙanƙancinmu idan muka gwada kanmu da taurari, kuma mu yi mamakin abin da ya sa Jehobah yake kula da mu. Kamar yadda za mu gani a wannan talifin, Jehobah bai lura da Adamu da Hauwa’u kawai ba, amma ya kawo su cikin iyalinsa.
2. Mene ne Jehobah ya nufa wa yaransa na farko a duniya?
2 Adamu da Hauwa’u ne ’ya’yan Allah na farko a duniya, kuma Jehobah ya zama Uba mai ƙauna a gare su. Ya ba su aikin yi kuma ya ce musu: “Ku yi ta haifuwa sosai ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta.” (Far. 1:28) Ya kamata su haifi ’ya’ya kuma su kula da duniya. Da a ce sun yi biyayya, da su da ’ya’yansu sun ci gaba da kasancewa a cikin iyalin Allah har abada.
3. Me ya sa za mu iya cewa Jehobah ya ba wa Adamu da Hauwa’u matsayi mai kyau a iyalinsa?
3 Jehobah ya ba wa Adamu da Hauwa’u matsayi mai kyau a cikin iyalinsa. Ga abin da Dauda ya faɗa game da yadda Allah ya yi ’yan Adam, ya ce: “Gama da kaɗan ka sa ya gaza mala’iku, da daraja da girma kuma ka naɗa shi.” (Zab. 8:5, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Gaskiya ne cewa ba a halicci ’yan Adam da ƙarfi da basira kamar mala’iku ba, kuma ba za su iya yin abubuwa kamar mala’iku ba. (Zab. 103:20) Duk da haka, “da kaɗan” ne kawai mala’iku suka fi su. Hakan na da ban mamaki! Sa’ad da Jehobah ya halicci iyayenmu na farko, ya ba su rayuwa mai inganci sosai.
4. Me ya faru da Adamu da Hauwa’u bayan sun yi rashin biyayya ga Jehobah, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?
4 Abin baƙin ciki shi ne, Adamu da Hauwa’u sun yi rashin biyayya ga Jehobah, sai ya kore su daga cikin iyalinsa. Hakan ya jawo ma ’ya’yansu babban matsala kamar yadda za mu tattauna a wannan talifin. Amma Jehobah bai canja nufinsa ba. Yana so ’yan Adam masu biyayya su zama yaransa har abada. Da farko, bari mu tattauna yadda Jehobah ya nuna cewa muna da daraja a gabansa. Sa’an nan, za mu tattauna abin da za mu iya yi yanzu don mu nuna cewa muna so mu kasance a iyalin Allah. A ƙarshe, za mu tattauna abubuwa masu kyau da iyalin Jehobah a duniya za ta mora har abada.
YADDA JEHOBAH YA DARAJA ’YAN ADAM
5. Ta yaya za mu nuna godiya ga Jehobah don ya halicce mu a cikin kamanninsa?
5 Jehobah ya nuna cewa muna da daraja a gabansa ta wajen halittar mu a cikin kamanninsa. (Far. 1:26, 27) Da yake Allah ya halicce mu a cikin kamanninsa, za mu iya koyan halayensa masu kyau. Alal misali, za mu iya kasancewa da halaye kamar ƙauna da tausayi da aminci da kuma adalci ko gaskiya. (Zab. 86:15; 116:5; 145:17) Yayin da muke nuna waɗannan halaye, muna ɗaukaka Jehobah ne da kuma yi masa godiya. (1 Bit. 1:14-16) Idan muka yi rayuwa yadda Jehobah yake so, za mu yi farin ciki. Kuma da yake muna da halaye irin na Jehobah, za mu zama waɗanda yake so su kasance a cikin iyalinsa.
6. Ta yaya Jehobah ya daraja ’yan Adam yayin da yake halittar duniya?
6 Jehobah ya shirya mana gida mai kyau. Jehobah ya shirya duniya da kyau, tun kafin ya halicci mutum na farko. (Ayu. 38:4-6; Irm. 10:12) Da yake Jehobah mai alheri ne da kuma mai bayarwa hannu sake, ya yi abubuwa da yawa da za su sa mu farin ciki. (Zab. 104:14, 15, 24) Akwai lokacin da ya yi tunani a kan abubuwan da ya yi, kuma ‘ya ga suna da kyau.’ (Far. 1:10, 12, 31) Ya nuna cewa ’yan Adam suna da daraja a gabansa ta wajen sa su “yi mulki a kan” dukan abubuwa masu kyau da ya halitta. (Zab. 8:6) Nufin Jehobah shi ne ’yan Adam kamiltattu su ji daɗin kula da abubuwa masu kyau da ya halitta har abada. Shin kana gode wa Jehobah a kullum don wannan nufi mai kyau da yake da shi?
7. Ta yaya Yoshuwa 24:15 ta nuna cewa ’yan Adam suna da ’yancin yin zaɓi?
7 Jehobah ya ba mu ’yancin zaɓan abin da muke so. Za mu iya zaɓan abin da muke so mu yi a rayuwa. (Karanta Yoshuwa 24:15.) Allahnmu mai ƙauna yana farin ciki a duk lokacin da muka zaɓa mu bauta masa. (Zab. 84:11; K. Mag. 27:11) Za mu iya amfani da wannan ’yancin da ya ba mu mu yanke shawarwari masu kyau. Bari mu tattauna wata hanya da Yesu ya yi amfani da ’yancin yin zaɓi da Jehobah ya ba shi.
8. A wace hanya ce Yesu ya yi amfani da ’yancinsa na yin zaɓi?
8 Za mu iya bin misalin Yesu ta wajen yin abin da zai amfani wasu, maimakon kanmu. Akwai lokacin da Yesu da manzanninsa suka gaji sosai, kuma suka yi tafiya zuwa wani wurin da babu kowa don su huta. Amma ba su samu sun huta ba. Taron jama’a sun je sun same su, kuma sun so Yesu ya koyar da su. Amma Yesu bai ɓata rai ba. A maimakon haka, ya tausaya musu. Me Yesu ya yi? ‘Ya fara koya musu abubuwa da yawa.’ (Mar. 6:30-34) A duk lokacin da muka yi koyi da Yesu ta wajen yin amfani da lokacinmu da ƙarfinmu mu taimaka wa mutane, muna ɗaukaka Ubanmu na sama ne. (Mat. 5:14-16) Ƙari ga haka, za mu nuna wa Jehobah cewa muna so mu kasance cikin iyalinsa.
9. Wace kyauta mai daraja ce Jehobah ya ba wa ’yan Adam?
9 Jehobah ya ba wa ’yan Adam damar haifan ’ya’ya da kuma hakkin koya musu game da shi. Idan kuna da yara, shin kuna godiya don wannan kyautar da Allah ya ba ku? Jehobah ya ba wa mala’iku baiwa da yawa, amma bai ba su damar haifan yara ba. Don haka, idan kuna da yara, ku gode wa Allah don damar da ya ba ku na haifan su. Allah ya ba wa iyaye aiki mai muhimmanci na renon yaransu ta wajen “horo da gargaɗi ta hanyar Ubangiji.” (Afis. 6:4; M. Sha. 6:5-7; Zab. 127:3) Ƙungiyarmu ta wallafa abubuwa da yawa da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki don ta taimaka wa iyaye su iya renon yaransu. Alal misali, an wallafa abubuwa kamar littattafai da bidiyoyi da waƙoƙi da kuma talifofi a dandalinmu na jw.org. Babu shakka, Jehobah da kuma Ɗansa Yesu suna ƙaunar ƙananan yara. (Luk. 18:15-17) Idan iyaye suka dogara ga Jehobah yayin da suke renon yaransu, Jehobah zai yi farin ciki. Ƙari ga haka, irin iyayen nan za su taimaka wa yaransu su sami begen kasancewa a cikin iyalin Jehobah har abada!
10-11. Wace dama ce Jehobah ya ba mu saboda fansar Yesu Kristi?
10 Jehobah ya ba da Ɗansa wanda yake ƙauna sosai don mu iya dawo cikin iyalinsa. Kamar yadda aka ambata a sakin layi na 4, zunubin da Adamu da Hauwa’u suka yi ya sa sun daina kasancewa a cikin iyalin Jehobah kuma hakan ya shafi ’ya’yansu. (Rom. 5:12) Adamu da Hauwa’u sun yi wa Allah rashin biyayya da gangan, don haka, ya dace da Allah ya kore su daga cikin iyalinsa. Amma ’ya’yansu fa? Jehobah yana ƙaunar ’yan Adam, don haka, ya shirya yadda waɗanda suka yi masa biyayya za su kasance a cikin iyalinsa. Ya yi hakan ta wajen ba da Ɗansa makaɗaici, wato Yesu Kristi don ya mutu a madadinmu. (Yoh. 3:16; Rom. 5:19) Don hadayar da Yesu ya bayar, Jehobah ya shigar da mutane masu aminci guda 144,000 cikin iyalinsa.—Rom. 8:15-17; R. Yar. 14:1.
11 Ban da waɗannan, akwai miliyoyin mutane masu aminci da suke yin nufin Allah a yau. Mutanen nan suna da begen kasancewa a cikin iyalin Jehobah bayan gwaji na ƙarshe da za a yi a ƙarshen shekara 1000 na sarautar Yesu. (Zab. 25:14; Rom. 8:20, 21) Saboda wannan begen da suke da shi, ko a yanzu ma suna kiran Jehobah Mahaliccinsu, ‘Uba.’ (Mat. 6:9) Waɗanda aka tā da su daga matattu ma za su sami damar koyan abin da Jehobah yake so su yi. Waɗanda suka yi abin da Jehobah yake so su yi, a ƙarshe za su kasance cikin iyalinsa.
12. Wace tambaya ce za mu amsa?
12 Kamar yadda muka gani, Jehobah ya yi abubuwa da yawa don ya nuna cewa yana daraja ’yan Adam. Ya riga ya mai da shafaffun Kiristoci ’ya’yansa kuma ya ba wa “babban taro,” ko kuma taro mai girma begen kasancewa cikin iyalinsa a sabuwar duniya. (R. Yar. 7:9) Me za mu yi yanzu don mu nuna wa Jehobah cewa muna so mu kasance cikin iyalinsa har abada?
KA NUNA WA JEHOBAH CEWA KANA SO KA KASANCE CIKIN IYALINSA
13. Mene ne za mu yi don mu kasance cikin iyalin Jehobah? (Markus 12:30)
13 Ka nuna cewa kana ƙaunar Jehobah ta wajen bauta masa da dukan zuciyarka. (Karanta Markus 12:30.) Jehobah ya ba mu kyaututtuka da yawa. Babu shakka gatan bauta masa yana ɗaya daga cikin kyaututtuka mafi muhimmanci da ya ba mu. Za mu nuna wa Jehobah cewa muna ƙaunarsa ta wajen “kiyaye umarnansa.” (1 Yoh. 5:3) Ɗaya daga cikin umurnai da Jehobah yake so mu bi shi ne umurnin da Yesu ya ba mu na almajirtarwa da kuma yi wa mutane baftisma. (Mat. 28:19) Ya kuma umurce mu mu ƙaunaci juna. (Yoh. 13:35) Jehobah zai marabci waɗanda suke yi masa biyayya cikin iyalinsa.—Zab. 15:1, 2.
14. Ta yaya za mu iya nuna wa mutane ƙauna? (Matiyu 9:36-38; Romawa 12:10)
14 Ka ƙaunaci mutane. Ƙauna ce halin Jehobah mafi muhimmanci. (1 Yoh. 4:8) Jehobah ya nuna mana ƙauna tun ba mu san shi ba. (1 Yoh. 4:9, 10) Za mu iya yin koyi da halin Jehobah ta wajen nuna wa mutane ƙauna. (Afis. 5:1) Ɗaya daga cikin hanyoyi mafi muhimmanci da za mu iya nuna wa mutane ƙauna ita ce ta wurin koya musu game da Jehobah yanzu da lokaci bai ƙure ba. (Karanta Matiyu 9:36-38.) Ta yin hakan muna ba su damar kasancewa cikin iyalin Jehobah. Kuma bayan sun yi baftisma, muna bukatar mu ci gaba da ƙauna da kuma daraja su. (1 Yoh. 4:20, 21) Ta yaya za mu yi hakan? Hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce ta wajen yarda da su. Alal misali, idan ba mu fahimci dalilin da ya sa suka yi wani abu ba, ba za mu yi saurin cewa sun yi hakan domin son kai ba. A maimakon haka, ya kamata mu girmama ’yan’uwanmu kuma mu ɗauke su da daraja fiye da kanmu.—Karanta Romawa 12:10; Filib. 2:3.
15. Ga su wa ya kamata mu yi alheri da jinƙai?
15 Ka nuna jinƙai da alheri ga dukan mutane. Idan muna so mu kasance cikin iyalin Jehobah, dole ne mu bi abin da Kalmarsa ta ce. Alal misali, Yesu ya koya mana cewa mu yi alheri da jinƙai ga kowa, har ma ga maƙiyanmu. (Luk. 6:32-36) A wasu lokuta, yin hakan yana iya mana wuya. Idan haka ne, dole ne mu bi tunani da kuma halayen Yesu. Idan mun yi iya ƙoƙarinmu don mu yi biyayya ga Jehobah kuma mu yi koyi da Yesu, za mu nuna wa Ubanmu na sama cewa muna so mu kasance a cikin iyalinsa har abada.
16. Ta yaya za mu guji ɓata sunan iyalin Jehobah?
16 Kada ka ɓata sunan iyalin Jehobah. A cikin iyali, yaro yakan yi koyi da abin da yayansa yake yi. Idan yayan yana bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarsa, zai kafa misali mai kyau ga ƙanensa. Idan kuma yayan yana yin abubuwa marasa kyau, ƙanen zai iya bin misalinsa marar kyau. Haka yake a iyalin Jehobah. Idan wani Kirista mai aminci a dā ya yi ridda ko ya soma yin lalata ko kuma wasu abubuwa da ba su dace ba, wasu za su iya bin misalinsa kuma su soma yin abin da bai dace ba. Waɗanda suke yin hakan, suna ɓata sunan iyalin Jehobah. (1 Tas. 4:3-8) Muna bukatar mu guji bin misalin da bai dace ba, kuma kada mu bar wani abu ya ɓata dangantakarmu da Ubanmu na sama mai ƙauna.
17. Wane irin tunani ne ya kamata mu guji yi, kuma me ya sa?
17 Ka dogara ga Jehobah maimakon abin duniya. Jehobah ya yi alkawari cewa zai yi mana tanadin abinci da sutura da wurin kwana idan muka saka Mulkinsa farko a rayuwarmu kuma muka bi ƙa’idodinsa. (Zab. 55:22; Mat. 6:33) Idan muka yarda da wannan alkawari da Jehobah ya yi mana, ba za mu ɗauka cewa abin duniya zai kāre mu kuma ya sa mu farin ciki ba. Mun san cewa abin da zai ba mu kwanciyar hankali na gaske shi ne yin nufin Jehobah. (Filib. 4:6, 7) Ko da muna da kuɗin sayan abubuwa da yawa, dole ne mu yi tunani ko muna da lokaci ko ƙarfin yin amfani da abubuwan da kuma kula da su. Idan ba mu yi hankali ba, abubuwan nan za su iya zama farko a rayuwarmu. Dole ne mu tuna cewa Jehobah ya ba mu aikin yi a iyalinsa. Hakan yana nufin cewa bai kamata mu bar wani abu ya raba hankalinmu ba. Hakika ba ma so mu zama kamar matashin da ya ƙi bin Yesu saboda abubuwan da ya mallaka. Hakan ya sa ya rasa gatan bauta ma Jehobah da kuma zama ɗaya daga cikin ’ya’yansa!—Mar. 10:17-22.
ABIN DA ’YA’YAN JEHOBAH ZA SU MORA HAR ABADA
18. Wane gata da kuma albarku ne ’yan Adam masu biyayya za mora har abada?
18 ’Yan Adam da suka yi biyayya za su mori gata mafi girma na bauta wa Jehobah da kuma ƙaunar sa har abada! Waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya kuma, za su ji daɗin kula da wannan kyakkyawar duniya da Jehobah ya shirya musu. Nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai sabunta duniya da kome da ke cikinta. Yesu Kristi zai magance dukan matsalolin da Adamu da Hauwa’u suka jawo wa yaransu sa’ad da suka zaɓi su bar iyalin Jehobah. Jehobah zai tā da miliyoyin mutane daga mutuwa kuma ya ba su gatan yin rayuwa har abada cikin ƙoshin lafiya a aljanna. (Luk. 23:42, 43) Sa’ad da ’yan Adam da suke bauta ma Jehobah suka zama kamiltattu, kowannensu zai sami “daraja da girma” da Dauda ya yi magana a kai.—Zab. 8:5, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
19. Me ya kamata mu tuna?
19 Idan kana cikin taro mai girma, kana da bege mai kyau. Allah yana ƙaunar ka kuma yana so ka kasance a cikin iyalinsa. Saboda haka, ka yi iya ƙoƙarinka don ka faranta masa rai. A ko da yaushe, ka riƙa tunani a kan alkawuran da Allah ya yi. Ka riƙa nuna godiya don gatan da kake da shi na bauta wa Ubanmu na sama, da kuma damar yabon sa har abada!
WAƘA TA 107 Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Ƙauna
a Kafin iyali ta zauna lafiya, dole ne kowa a iyalin ya san abin da ya kamata ya yi kuma ya taimaka ma sauran membobin iyalin. Maigida zai nuna ƙauna yayin da yake yi ma iyalinsa ja-goranci, matarsa za ta goyi bayansa yaransu kuma za su yi biyayya ga iyayensu. Haka yake da iyalin Jehobah. Allah yana da dalilin da ya sa ya halicce mu kuma idan muka yi rayuwar da ta jitu da nufinsa, za mu kasance a cikin iyalinsa har abada.
b BAYANI A KAN HOTUNA: Jehobah ya halicci mutane yadda za su iya yin koyi da halayensa. Shi ya sa ma’auratan nan suke iya nuna ƙauna da tausayi ga juna da kuma yaransu. Da yake ma’auratan suna ƙaunar Jehobah, suna nuna godiyarsu don damar haifan yara ta wajen koya wa yaran su ƙaunaci Jehobah kuma su bauta masa. Iyayen suna amfani da bidiyo don su nuna wa yaransu dalilin da ya sa Jehobah ya ba da Yesu a matsayin fansa. Ban da haka, suna koya musu cewa a cikin aljanna, za mu kula da duniya da kuma dabbobi har abada.