TALIFIN NAZARI NA 16
“Ɗanꞌuwanki Zai Tashi”!
“Yesu ya ce [wa Marta], ‘Ɗanꞌuwanki zai tashi.’”—YOH. 11:23.
WAƘA TA 151 Zai Kira Su
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Ta yaya wani yaro ya nuna cewa ya gaskata da tashin matattu?
WANI yaro mai suna Matthew yana rashin lafiya mai tsanani kuma hakan ya sa an yi masa tiyata sau da yawa. Saꞌad da yake shekara bakwai, shi da iyayensa suna kallon shirin Tashar JW. Da shirin ya kusan ƙarewa, sun kalli wata waƙa da ta nuna yadda mutane suke marabtar ƙaunatattunsu da aka tayar daga mutuwa.b Bayan sun gama kallon shirin, Matthew ya tashi kuma ya riƙe hannun mamarsa da babansa. Sai ya ce musu: “Mama da Baba, kun gani ko? Ko da na mutu, zan tashi a lokacin tashin matattu. Za ku iya jira na, kome zai yi kyau.” Ka yi tunanin irin farin ciki da iyayen nan suka yi da suka ga imanin ɗansu!
2-3. Me ya sa ya dace mu tattauna game da alkawarin tashin matattu?
2 Zai dace dukanmu mu ɗau lokaci kuma mu yi tunani a kan alkawarin da Allah ya yi game da tashin matattu a-kai-a-kai. (Yoh. 5:28, 29) Me ya sa? Domin za mu iya kamuwa da rashin lafiya mai tsanani ba zato ko kuma wanda muke ƙauna ya rasu. (M. Wa. 9:11; Yak. 4:13, 14) Begen tashin matattu zai iya taimaka mana mu jimre matsalolin nan. (1 Tas. 4:13) Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Ubanmu na sama ya san mu sosai kuma yana ƙaunar mu. (Luk. 12:7) Jehobah yana bukatar ya san mu sosai kafin ya iya ta da mu da halayen da muke da su da kuma abubuwan da muka sani kafin muka mutu. Jehobah yana ƙaunar mu sosai shi ya sa yi mana alkawarin rai na har abada kuma ko da mun mutu, zai ta da mu.
3 A wannan talifin, za mu soma da tattauna dalilin da ya sa muka gaskata da alkawarin tashin matattu. Bayan haka, za mu tattauna wani labari mai ban ƙarfafa da ke Littafi Mai Tsarki. A cikin labarin ne aka ɗauko jigon wannan talifin, wato: “Ɗanꞌuwanki zai tashi.” (Yoh. 11:23) A ƙarshe, za mu koyi yadda za mu daɗa gaskata da alkawarin tashin matattu.
DALILIN DA YA SA ZA MU IYA GASKATA DA ALKAWARIN TASHIN MATATTU
4. Kafin mu gaskata da alkawarin da wani ya yi mana, mene ne muke bukatar mu tabbata da shi? Ka ba da misali.
4 Kafin mu gaskata da alkawarin da mutum ya yi mana, sai mun tabbata cewa mutumin yana da niyya da kuma ikon cika alkawarin. Alal misali, a ce guguwa ta lalata gidanka sosai. Sai wani abokinka ya zo kuma ya yi maka alkawari cewa zai taimaka ya gyara maka gidan. Ka san cewa da gaske yake kuma yana da niyyar taimaka maka. Idan shi ƙwararren magini ne kuma yana da kayan aiki, za ka yarda cewa zai iya yin hakan kuma za ka gaskata alkawarinsa. Alkawarin da Allah ya yi mana game da tashin matattu kuma fa? Shin yana da niyya da kuma ikon cika alkawarin?
5-6. Me ya sa za mu iya tabbata cewa Jehobah yana marmarin ta da matattu?
5 Shin Jehobah yana da niyyar ta da matattu? Babu shakka yana da niyya. Ya sa marubutan Littafi Mai Tsarki da yawa su rubuta alkawarin da ya yi game da tashin matattu a nan gaba. (Isha. 26:19; Hos. 13:14; R. Yar. 20:11-13) Kuma a duk lokacin da Jehobah ya yi alkawari, yana cikawa. (Yosh. 23:14) Jehobah yana marmarin ta da waɗanda suka mutu. Me ya tabbatar mana da hakan?
6 Ka yi laꞌakari da abin da Ayuba ya faɗa. Yana da tabbaci cewa ko da ya mutu, Jehobah zai sake ta da shi. (Ayu. 14:14, 15, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Jehobah yana marmarin ta da dukan bayinsa da suka mutu. Yana marmarin ta da su cikin ƙoshin lafiya da kuma farin ciki. Me zai faru da waɗanda suka mutu kuma ba su samu zarafin koya game da Jehobah ba? Su ma Ubanmu mai ƙauna yana so ya ta da su. (A. M. 24:15) Yana so su sami zarafin zama abokansa kuma su yi rayuwa har abada a duniya. (Yoh. 3:16) Ba shakka, Jehobah yana marmarin ta da matattu.
7-8. Me ya sa muka tabbata cewa Jehobah yana da ikon ta da matattu?
7 Shin Jehobah yana da ikon ta da matattu? Ƙwarai kuwa! Shi ne “Mai Iko Duka.” (R. Yar. 1:8) Don haka, yana da ikon cin nasara a kan dukan maƙiyansa, har ma da mutuwa. (1 Kor. 15:26) Sanin hakan yana ƙarfafa mu kuma yana taꞌazantar da mu. Ka yi laꞌakari da misalin ꞌYarꞌuwa Emma Arnold. Ita da iyalinta sun fuskanci gwaji sosai a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu. Gwamnatin Nazi ta kashe ꞌyanꞌuwansu a kurkuku. Don ta iya taꞌazantar da ꞌyarta, Emma ta ce: “Idan mutanen da suka mutu ba za su sake rayuwa ba, hakan yana nufin cewa mutuwa ta fi Allahnmu iko. Amma hakan ba gaskiya ba ne.” Tabbas, ba abin da ya kai Jehobah iko! Allah mafi iko da ya halicci rai yana da ikon sake maido da rai ga mutanen da suka mutu.
8 Wani dalili kuma da ya sa muka gaskata cewa Allah yana da ikon ta da matattu shi ne, ba ya mantuwa. Yana kiran dukan taurari da sunayensu. (Isha. 40:26) Kuma yana tunawa da mutanen da suka mutu. (Ayu. 14:13; Luk. 20:37, 38) Ba zai yi masa wuya ya tuna kome da kome game da waɗanda za a tā da su ba. Hakan ya haɗa da kamaninsu da halayensu da abubuwan da suka fuskanta a rayuwa da kuma tunaninsu.
9. Me ya sa ka gaskata da alkawarin da Jehobah ya yi game da tashin matattu a nan gaba?
9 Babu shakka, za mu iya gaskata da alkawarin da Allah ya yi game da tashin matattu domin yana da niyya da kuma ikon cika alkawarin. Wani dalili kuma da zai sa mu daɗa gaskata da hakan shi ne, Jehobah ya taɓa ta da mutane a dā. A zamanin dā, Jehobah ya ba ma wasu mutane iko su ta da matattu, har da Yesu. Bari mu tattauna ɗaya daga cikin tashin matattu da Yesu ya yi da aka rubuta a littafin Yohanna sura 11.
ABOKIN YESU YA RASU
10. Me ya faru saꞌad da Yesu yake waꞌazi a tsallaken Kogin Urdun daga Betani? (Yohanna 11:1-3)
10 Karanta Yohanna 11:1-3. Ka yi tunanin abin da ya faru a Betani a wajen ƙarshen shekara ta 32 bayan haifuwar Yesu. Yesu yana da abokai a ƙauyen nan, wato Liꞌazaru da ꞌyanꞌuwansa Maryamu da Marta. (Luk. 10:38-42) Amma Liꞌazaru ya soma rashin lafiya kuma ꞌyanꞌuwansa sun damu. Sun aika a gaya wa Yesu, amma a lokacin, Yesu yana ƙetaren Kogin Urdun da ke da nisan tafiyar kwana biyu daga Betani. (Yoh. 10:40) Abin baƙin ciki, Liꞌazaru ya mutu kafin Yesu ya sami saƙon. Ko da yake Yesu ya san cewa abokinsa ya mutu, ya sake yin kwana biyu a inda yake kafin ya soma tafiya zuwa Betani. Don haka, saꞌad da Yesu ya isa, Liꞌazaru ya yi kwana huɗu da mutuwa. Yesu yana so ya yi abin da zai amfani abokansa kuma ya kawo ɗaukaka ga Allah.—Yoh. 11:4, 6, 11, 17.
11. Wane darasi ne za mu iya koya game da abokantaka daga labarin nan?
11 Wannan labarin ya koya mana darasi mai kyau game da abokantaka. Ka yi laꞌakari da wannan: Saꞌad da Maryamu da Marta suka aika wa Yesu saƙo, ba su gaya masa ya zo Betani ba. Sun dai gaya masa cewa abokinsa yana rashin lafiya. (Yoh. 11:3) Da Liꞌazaru ya mutu, Yesu zai iya ta da shi daga nesa. Amma ya zaɓi ya je Betani don ya kasance da abokansa Maryamu da Marta. Shin kana da aboki da zai iya kawo maka ɗauki ba tare da ka roƙe shi ba? Idan kana da irin wannan abokin, kana da tabbacin cewa zai taimaka maka “a kwanakin masifa.” (K. Mag. 17:17) Kamar Yesu, bari dukanmu mu zama irin abokin nan ga mutane! Yanzu bari mu sake koma ga labarin don mu ga abin da ya faru bayan hakan.
12. Wane alkawari ne Yesu ya yi wa Marta, kuma me ya sa ba cika baki yake yi ba? (Yohanna 11:23-26)
12 Karanta Yohanna 11:23-26. Marta ta ji cewa Yesu ya kusan isowa Betani. Sai ta fita da wuri don ta marabce shi kuma ta ce masa: “Ubangiji, ai, da kana nan da ɗanꞌuwana bai mutu ba.” (Yoh. 11:21) Gaskiya ne, da ya warkar da Liꞌazaru. Amma Yesu yana so ya yi abin da ya fi hakan muhimmanci. Ya yi alkawari cewa: “Ɗanꞌuwanki zai tashi.” Ya kuma ba wa Marta ƙarin dalili da zai sa ta gaskata da alkawarin da ya yi mata. Ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai.” Hakika, Jehobah ya ba shi iko a kan rai da kuma mutuwa. Kafin wannan lokacin, ya ta da wata yarinya ƙarama da ta mutu, ya kuma ta da wani matashi a kan hanya, wanda bai daɗe da mutuwa ba. (Luk. 7:11-15; 8:49-55) Amma zai iya ta da wanda ya yi kwana huɗu da mutuwa kuma jikinsa ya fara ruɓewa?
“LI’AZARU, FITO!”
13. Kamar yadda Yohanna 11:32-35 suka ce, mene ne Yesu ya yi saꞌad da ya ga Maryamu da wasu suke kuka? (Ka kuma duba hoton.)
13 Karanta Yohanna 11:32-35. Ka yi tunanin abin da ya faru bayan hakan. Maryamu, ꞌyarꞌuwar Liꞌazaru, ita ma ta je ta marabci Yesu. Ta maimaita abin da ꞌyarꞌuwarta ta faɗa: “Ubangiji, ai, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.” Ita da sauran mutane da suke tare da ita suna matuƙar baƙin ciki. Da Yesu ya ga suna kuka, sai ya yi baƙin ciki sosai. Da yake ya tausaya wa abokansa sosai, sai ya zub da hawaye. Ya san zafin da mutum yakan ji idan ya rasa na kusa da shi. Babu shakka, yana marmarin ƙawar da baƙin cikin da suke yi!
14. Me za mu iya koya game da Jehobah daga abin da Yesu ya yi saꞌad da ya ga Maryamu tana kuka?
14 Abin da Yesu ya yi saꞌad da ya ga Maryamu tana kuka ya taimaka mana mu fahimci cewa Jehobah Allah ne mai tausayi. Me ya sa muka faɗi hakan? Kamar yadda muka ga a talifin da ya gabata, Yesu yana tunani da kuma yin abubuwa kamar Ubansa. (Yoh. 12:45) Don haka, idan muka karanta cewa Yesu ya tausaya wa abokansa har ya zub da hawaye, mu tabbata cewa Jehobah ma yana damuwa domin matsalolin da muke fuskanta. (Zab. 56:8) Hakika, hakan ya sa kana so ka yi kusa da Ubanmu mai tausayi, ko ba haka ba?
15. Bisa ga labarin da ke Yohanna 11:41-44, ka bayyana abin da ya faru a kabarin Liꞌazaru. (Ka kuma duba hoton.)
15 Karanta Yohanna 11:41-44. Yesu ya je inda aka binne Liꞌazaru, kuma ya ce a cire dutsen da aka rufe kabarin da shi. Marta ba ta yarda da hakan ba domin a ganinta jikin ya soma wari. Yesu ya amsa mata ya ce: “Ba na riga na gaya miki cewa idan kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah ba?” (Yoh. 11:39, 40) Sai Yesu ya ɗaga idanunsa sama kuma ya yi adduꞌa a gaban jamaꞌa. Ya yi hakan ne domin yana so a yabi Jehobah. Sai Yesu ya ce: “Liꞌazaru, fito!” Sai Liꞌazaru ya fito daga kabarin! Yesu ya yi abin da wasu suke ganin ba zai taɓa yiwuwa ba.—Ka kuma duba bayanin da aka yi (study note) a kan Yohanna 11:17 a NWT na nazari.
16. Ta yaya labarin da ke Yohanna sura 11 ya ƙara tabbatar mana cewa za a ta da matattu?
16 Labarin da muka karanta a Yohanna sura 11 ya ƙara tabbatar mana cewa za a ta da matattu. Ta yaya? Ka tuna da alkawarin da Yesu ya yi wa Marta, ya ce: “Ɗanꞌuwanki zai tashi.” (Yoh. 11:23) Kamar Ubansa, Yesu yana da niyya da kuma ikon cika wannan alkawarin. Hawaye da Yesu ya yi, ya nuna cewa yana marmarin kawo ƙarshen mutuwa da kuma matsaloli da hakan ya jawo. Kuma yadda Liꞌazaru ya fito daga kabarin ƙarin tabbaci ne cewa Yesu yana da ikon ta da matattu. Ƙari ga haka, ka yi tunani a kan tunasarwa da Yesu ya yi wa Marta, cewa: ‘Ba na riga na gaya miki cewa idan kin ba da gaskiya za ki ga ɗaukakar Allah ba?’ (Yoh. 11:40) Muna da dalilai masu kyau na gaskata cewa alkawarin da Allah ya yi game da tashin matattu zai cika. Amma mene ne za mu yi don mu daɗa gaskata da wannan alkawarin?
TA YAYA ZA MU DAƊA GASKATA DA ALKAWARIN TASHIN MATATTU?
17. Me muke bukatar mu yi yayin da muke karanta game da tashin matattu?
17 Ka karanta labaran tashin matattu da aka yi a dā kuma ka yi bimbini a kai. Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mutane takwas da aka ta da su a nan duniya.c Me zai hana ka yin nazari mai zurfi a kan kowanne ɗayansu? Yayin da kake yin hakan, ka tuna cewa waɗannan mutane ne kamar ka, maza da mata da kuma yara. Ka nemi darasi da za ka iya koya daga labarin. Ka yi tunani a kan yadda kowanne ɗaya daga cikin labaran ya nuna yadda Allah yake da niyya da kuma ikon ta da matattu. Ka yi tunani a kan tashin matattu mafi muhimmanci, wato na Yesu. Ka tuna cewa akwai ɗaruruwan mutane da suka shaida tashin Yesu daga mutuwa, kuma hakan ya ba mu dalili mai kyau na gaskatawa da alkawarin tashin matattu.—1 Kor. 15:3-6, 20-22.
18. Ta yaya za ka iya amfana daga waƙoƙinmu game da tashin matattu? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)
18 Ka saurari waƙoƙi da suka ambaci tashin matattu.d (Afis. 5:19) Waƙoƙin nan suna sa mu daɗa gaskata da tashin matattu kuma suna ƙara ba mu bege. Ka saurare su kuma ka koyi yadda za ka rera su. Ƙari ga haka, ku tattauna maꞌanar kalmomin waƙoƙin saꞌad da kuke ibada ta iyali. Ka haddace kalmomin waƙoƙin kuma ka yi tunani a kan su domin su ƙarfafa ka kuma su ratsa zuciyarka. Don haka, saꞌad da ka kamu da rashin lafiya mai tsanani ko kuma wanda kake ƙauna ya rasu, ruhu mai tsarki zai taimaka maka ka tuna da kalmomin waƙoƙin kuma ka sami taꞌaziya da ƙarfafa.
19. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yin tunanin su game da tashin matattu? (Ka duba akwatin nan “Wace Tambaya Za Ka Yi Musu?”)
19 Ka ɗauka kana cikin aljanna. Jehobah ya halicce mu yadda za mu iya ɗauka muna rayuwa a cikin aljanna. Wata ꞌyarꞌuwa ta bayyana cewa: “Na ɗau lokaci sosai ina tunanin rayuwa a cikin aljanna, har na ji kamar ina jin ƙanshin fulawowi da suke tsirowa a aljanna.” Ka yi tunanin haɗuwa da maza da mata masu bangaskiya da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Waye a cikinsu kake marmarin haɗuwa da shi? Wace tambaya za ka so ka yi masa? Ka yi tunanin yadda za ka sake haɗuwa da ƙaunatattunka da suka mutu bayan an ta da su. Ka yi tunanin abu na farko da za ka gaya musu, yadda za ka rungume su da kuma yadda za ka yi farin cikin sake haɗuwa da su.
20. Wane abu ne ya kamata mu ƙudiri niyyar yi?
20 Muna godiya sosai ga Jehobah domin alkawarin da ya yi mana cewa zai ta da matattu! Za mu iya kasance da tabbaci cewa alkawarin nan zai cika domin Jehobah yana da niyya da kuma ikon cika alkawarin. Bari mu ƙudiri niyyar ci gaba da gaskata da alkawarin tashin matattu. Ta hakan, za mu ƙara kusantar Allah wanda ya yi mana alkawari cewa, ‘Ƙaunatattunku za su tashi!’
WAƘA TA 147 Alkawarin Rai Na Har Abada
a Idan wanda kake ƙauna ya rasu, babu shaka alkawarin tashin matattu zai taꞌazantar da kai. Amma ta yaya za ka iya bayyana ma wasu dalilin da ya sa ka gaskata da wannan alkawarin? Kuma ta yaya za ka iya daɗa gaskata da alkawarin? An shirya wannan talifin ne domin ya taimaka ma dukanmu mu daɗa gaskata da alkawarin tashin matattu.
b Jigon waƙar shi ne Aljanna Ta Kusa kuma an fitar da waƙar a shirin Tashar JW na Nuwamba 2016.
c Ka duba akwatin nan “Tashin Matattu Takwas da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 2015, shafi na 4.
d Ka duba waƙoƙin nan da ke ‘Ku Rera Waƙa da Murna’ ga Jehobah: “Rayuwa a Cikin Aljanna” (Waƙa ta 139), “Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!” (Waƙa ta 144), da kuma “Zai Kira Su” (Waƙa ta 151). Ka kuma duba waɗannan waƙoƙin JW a dandalinmu, “Aljanna Ta Kusa,” “Rayuwa a Cikin Aljanna,” da kuma “Ku Zo Ku Ga Aljannar.”