TALIFIN NAZARI NA 53
Samari, Ku Yi Ƙoƙari Ku Zama Kiristoci da Suka Manyanta
“Ka ƙarfafa, ka nuna kanka namiji ne.”—1 SAR. 2:2.
WAƘA TA 135 Jehobah Ya Ce: “Ɗana Ka Yi Hikima”
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Mene ne namiji da Kirista ne yake bukatar ya yi don ya yi nasara?
SARKI Dauda ya gaya wa Sulemanu cewa: “Ka ƙarfafa, ka nuna kanka namiji ne.” (1 Sar. 2:1-3) Yana da muhimmanci dukan Kiristoci maza su bi shawarar nan. Idan suna so su yi nasara, dole ne su bi dokokin Allah kuma su bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki a dukan fannonin rayuwarsu. (Luk. 2:52) Me ya sa yake da muhimmanci samari su yi iya ƙoƙarinsu su zama Kiristocin da suka manyanta?
2-3. Me ya sa yake da muhimmanci saurayi ya zama Kiristan da ya manyanta?
2 Namiji da Kirista ne, yana da babban hakki a iyali da kuma ikilisiya. Ba shakka ku samari, kun yi tunani a kan ayyukan da za ku samu a nan gaba. Za ku iya yin burin zama magajaba, bayi masu hidima, daga baya kuma ku zama dattawa. Ƙila ma za ku so ku yi aure kuma ku haifi yara. (Afis. 6:4; 1 Tim. 3:1) Amma sai kun zama Kiristocin da suka manyanta ne za ku iya yin hakan kuma ku yi nasara.b
3 Me zai taimake ku ku zama Kiristocin da suka manyanta? Akwai abubuwa masu muhimmanci da kuke bukatar ku koya. Me za ku iya yi yanzu da zai shirya ku don hakkin da za ku ɗauka a nan gaba kuma ku yi nasara?
ABUBUWAN DA ZA SU SA KA ZAMA KIRISTAN DA YA MANYANTA
4. A ina ne za ku iya samun misalan mutane masu halayen kirki? (Ka kuma duba hoton.)
4 Ka yi koyi da mutane masu halin kirki. A Littafi Mai Tsarki, akwai misalan mutane da yawa masu halayen kirki da samari za su iya yin koyi da su. Waɗannan mutanen sun ƙaunaci Allah kuma sun kula da mutanensa a hanyoyin da yawa. Ƙari ga haka, za ku iya yin koyi da ꞌyanꞌuwa maza masu halayen kirki a ikilisiyarku ko kuma a iyalinku. (Ibran. 13:7) Ban da haka, kuna da wanda ya fi kafa muku misali mai kyau, wato Yesu Kristi. (1 Bit. 2:21) Yayin da kuke nazari game da mutanen nan, ku lura da halayensu masu kyau. (Ibran. 12:1, 2) Sai ku yi tunani a kan yadda za ku bi halinsu.
5. Me zai taimaka maka ka zama mai hankali, kuma me ya sa halin nan yake da muhimmanci? (Zabura 119:9)
5 Ka zama mai “hankali” kuma ka “riƙe” hankalin kam-kam. (K. Mag. 3:21) Mutum mai hankali ba ya ɗaukan mataki cikin garaje. Yakan zauna ya yi tunani kafin ya yi hakan. Don haka, ka yi iya ƙoƙari ka kasance da wannan halin. Me ya sa? Domin a duniyar nan, yawancin mutane suna yanke shawarwari bisa ga nasu raꞌayin ko yadda suke ji. (K. Mag. 7:7; 29:11) Ƙari ga haka, ƙafofin yaɗa labarai ko dandalin sada zumunta suna iya shafan tunaninka. Amma me zai taimaka maka ka zama mai hankali? Da farko, ka koyi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki, kuma ka yi tunani a kan dalilin da ya sa yake da kyau ka bi ƙaꞌidodin nan. (Karanta Zabura 119:9.) Idan ka koyi wannan hali mai muhimmanci, zai taimaka maka ka zama Kiristan da ya manyanta. (K. Mag. 2:11, 12; Ibran. 5:14) Ka ga yadda hankali zai taimaka maka a hanyoyi biyun nan: (1) saꞌad da kake yin shaꞌani da ꞌyanꞌuwa mata da kuma (2) saꞌad da kake yanke shawara a kan kayan da za ka saka da adon da za ka yi.
6. Ta yaya hankali zai taimaka wa saurayi ya riƙa daraja mata?
6 Idan kana yin tunani yadda Jehobah yake tunani, za ka riƙa daraja ꞌyanꞌuwa mata. Alal misali, ɗanꞌuwa da saurayi ne zai iya son wata ꞌyarꞌuwa kuma hakan ba laifi ba ne. Amma saurayi mai hankali, idan bai da niyyar auran ꞌyarꞌuwa, ba zai yi wani abu ko ya faɗi wani abin da zai sa ta ji kamar yana son ta ba. (1 Tim. 5:1, 2) Idan yana neman wata ꞌyarꞌuwa, zai yi iya ƙoƙarinsa ya kāre mutuncinta ta wajen ƙin kasancewa tare da ita a inda babu kowa.—1 Kor. 6:18.
7. Ta yaya hankali zai taimaka wa saurayi saꞌad da yake yanke shawara game da kayan da zai saka da adon da zai yi?
7 Wata hanya kuma da saurayi zai nuna cewa yana da hankali, shi ne saꞌad da yake yanke shawarwari game da kayan da zai saka da adon da zai riƙa yi. A yawancin lokuta, mutanen da suke yin kayan sakawa da tallar su, ba sa bauta wa Jehobah kuma rayuwar lalata suke yi. Don haka, suna yin matsatsun kayayyaki da waɗanda suke sa namiji ya yi kama da mace. Saꞌad da Kiristan da ya manyanta yake zaɓan tufafin da zai saka, zai bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da misalin ꞌyanꞌuwa masu halayen kirki a ikilisiya. Zai dace ya tambayi kansa cewa: ‘Shin zaɓina yana nuna cewa ni mai hankali ne kuma na damu da yadda mutane suke ji? Shin tufafina suna sa mutane su yarda cewa ina bauta wa Jehobah?’ (1 Kor. 10:31-33; Tit. 2:6) Idan saurayi ya nuna cewa shi mai hankali ne, ꞌyanꞌuwa za su daraja shi kuma Jehobah zai ƙaunace shi.
8. Ta yaya saurayi zai zama wanda za a yarda da shi?
8 Ka zama wanda mutane za su iya yarda da shi. Saurayin da za a iya yarda da shi yana yin ayyukan da aka ba shi da kyau kuma da himma. (Luk. 16:10) Ka yi laꞌakari da misalin Yesu. Bai taɓa yin wasa da aikin da aka ba shi ba. A maimakon haka, ya yi dukan ayyukan da Jehobah ya ba shi ko a lokacin da yin hakan yake da wuya. Yana ƙaunar mutane, musamman mabiyansa, har ya ba da ransa a madadin su. (Yoh. 13:1) Ka yi koyi da Yesu kuma ka yi iya ƙoƙarinka ka yi dukan aikin da aka ba ka. Idan kana shakkar yadda za ka yi aikin, ka nuna sauƙin kai kuma ka roƙi ꞌyanꞌuwan da suka manyanta su taimaka maka. Kada ka ce daidai abin da ake bukata ne kawai za ka yi. (Rom. 12:11) A maimakon haka, ka yi aikin gabaki ɗaya kuma ka yi shi ‘kamar ga Ubangiji ne kake yi wa, ba ga mutum ba.’ (Kol. 3:23) Hakika, kai ma za ka iya yin kuskure, don haka ka san kasawarka kuma ka amince da kurakuranka.—K. Mag. 11:2.
KA KOYI ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKA MAKA A RAYUWA
9. Me ya sa yake da muhimmanci saurayi ya koyi wasu abubuwan da za su taimaka masa a rayuwa?
9 Kafin ka zama Kiristan da ya manyanta, kana bukatar ka koyi yin wasu abubuwa. Hakan zai taimaka maka ka iya yin ayyukan da aka ba ka a ikilisiya, ka sami aikin da zai taimaka maka ka kula da iyalinka, kuma ka kasance da dangantaka mai kyau da mutane. Ga wasu daga cikin abubuwa da kake bukatar ka koya.
10-11. Ta yaya saurayi da kuma ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su amfana idan ya koyi yin karatu da rubutu da kyau? (Zabura 1:1-3) (Ka kuma duba hoton.)
10 Ka koyi yin karatu da rubutu da kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce mutumin da yake ɗaukan lokaci ya karanta Kalmar Allah zai yi farin ciki kuma ya yi nasara a rayuwa. (Karanta Zabura 1:1-3.) Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki koyaushe, za ka san yadda Jehobah yake tunani, kuma hakan zai taimaka maka ka san yadda za ka bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarka. (K. Mag. 1:3, 4) Ana bukatar irin waɗannan mazan a ikilisiya. Me ya sa?
11 ꞌYanꞌuwanmu maza da mata sukan je wurin ꞌyanꞌuwa maza da suka manyanta don su nemi shawara daga Littafi Mai Tsarki. (Tit. 1:9) Idan ka iya karatu da rubutu da kyau, za ka iya yin jawabai da kalamai masu kayatarwa da kuma ban ƙarfafa. Ƙari ga haka, za ka iya rubuta darussan da ka koya saꞌad da kake nazari, ko idan kana sauraran jawabai a taron ikilisiya da manyan tarurrukanmu. Waɗannan darussan za su ƙarfafa bangaskiyarka da na wasu.
12. Mene ne zai taimaka maka ka iya tattaunawa da mutane da kyau?
12 Ka zama mai sauraran mutane da mai bayyana raꞌayinsa da kyau. Kiristan da ya manyanta yana bukatar ya kasance da waɗannan halayen. Namijin da ya iya tattaunawa da mutane da kyau yana sauraran su kuma yana fahimtar yadda suke ji. (K. Mag. 20:5) Zai iya sanin yadda mutum yake ji ta muryarsa ko yanayin fuskarsa ko kuma motsin jikinsa. Amma ba za ka iya yin abubuwan nan ba idan ba ka kasancewa tare da mutane. Idan ta waya ko saƙo ne kake yawan tattaunawa da mutane, hakan zai sa ya ƙara yi maka wuya ka iya yin magana da mutane fuska-da-fuska da kyau. Don haka, ka yi iya ƙoƙarinka ka riƙa yin magana da mutane fuska-da-fuska.—2 Yoh. 12.
13. Waɗanne abubuwa ne kuma saurayi yake bukatar ya koya? (1 Timoti 5:8) (Ka kuma duba hoton.)
13 Ka koyi yadda za ka kula da kanka. Wajibi ne Kiristan da ya manyanta ya iya kula da kansa da kuma iyalinsa. (Karanta 1 Timoti 5:8.) A wasu ƙasashe, ꞌyanꞌuwa matasa sukan koyi sanaꞌa a wurin babansu ko kuma wani danginsu. A wasu wuraren kuma, matashi yana iya koyan aikin hannu a makarantar sakandare. Ko da yaya yanayinka yake, zai dace ka koyi wani abu da zai taimaka maka ka sami aiki. (A. M. 18:2, 3; 20:34; Afis. 4:28) Ka sa a san da kai a matsayin wanda yake yin aiki da ƙwazo kuma yake yin ƙoƙarinsa ya gama aikin da aka ba shi. Idan ka yi hakan, mutane za su so su ɗauke ka aiki kuma ba za su so su rasa ka ba. Abubuwan nan da muka tattauna za su taimaka wa Kirista ya iya cika wasu hakkoki a nan gaba. Bari mu tattauna wasu daga cikin hakkokin nan.
KA YI SHIRI DON NAN GABA
14. Mene ne zai taimaka wa matashi ya soma yin hidima ta cikakken lokaci?
14 Hidima ta cikakken lokaci. Kiristoci da yawa da suka manyanta sun soma hidima ta cikakken lokaci tun suna matasa. Hidimar majagaba tana taimaka wa saurayi ya san yadda zai yi aiki tare da mutane dabam-dabam. Tana kuma taimaka masa ya san yadda zai yi amfani da kuɗinsa da kyau, kuma ya guji kashe kuɗi yadda ya ga dama. (Filib. 4:11-13) Wani abin da zai taimaka maka ka soma hidima ta cikakken lokaci shi ne, yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. ꞌYanꞌuwa da yawa sun yi hidimar majagaba na ɗan lokaci kuma hakan ya taimaka musu su zama majagaba na kullum. Yin hidimar majagaba za ta ba ka damar yin wasu hidimomi da yawa a ƙungiyar Jehobah, kamar yin aiki a sashen gine-gine ko hidima a Bethel.
15-16. Me zai taimaka wa saurayi ya iya zama bawa mai hidima ko kuma dattijo?
15 Za ka iya zama bawa mai hidima ko kuma dattijo. Ya kamata duka ꞌyanꞌuwa maza su yi burin yi wa ꞌyanꞌuwansu hidima a matsayin dattawa a ikilisiya. Littafi Mai Tsarki ya ce maza da suke da irin wannan burin “aikin daraja [‘mai kyau,’ NWT]” ne suke marmarin sa. (1 Tim. 3:1) Kafin ɗanꞌuwa ya zama dattijo, dole ya zama bawa mai hidima. Bayi masu hidima suna taimaka wa dattawa a hanyoyi da yawa. Amma dattawa da bayi masu hidima suna yi wa ꞌyanꞌuwansu hidima cikin sauƙin kai, kuma suna yin waꞌazi da ƙwazo. Saurayi zai iya zama bawa mai hidima ko da shekarunsa 17 ne. Bawa mai hidima da ya ƙware zai iya zama dattijo ko da shekarunsa 20 ne.
16 Mene ne za ka iya yi don ka zama bawa mai hidima, daga baya kuma ka zama dattijo? Littafi Mai Tsarki ya ambata wasu halayen da ya kamata ka kasance da su. Idan kana ƙaunar Jehobah da iyalinka da kuma ꞌyanꞌuwa a ikilisiya, hakan zai sa ka koyi halayen nan. (1 Tim. 3:1-13; Tit. 1:6-9; 1 Bit. 5:2, 3) Ka yi ƙoƙari ka fahimci kowane halin da ya kamata ka kasance da shi. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka zama mai halayen nan.c
17. Ta yaya saurayi zai yi shirin zama maigida nagari? (Ka kuma duba hoton.)
17 Za ka iya zama maigida. Kamar yadda Yesu ya faɗa, wasu Kiristoci da suka manyanta sukan ƙi yin aure. (Mat. 19:12) Amma idan ka yi aure, za ka sami hakkin kula da iyalinka a matsayin maigida. (1 Kor. 11:3) Jehobah yana so maigida ya ƙaunaci matarsa, ya biya bukatunta, ya zama abokinta kuma ya taimaka mata ta bauta masa da kyau. (Afis. 5:28, 29) Abubuwan da muka ambata a talifin nan, kamar zama mai hankali, da daraja mata, da zama wanda za a iya yarda da shi, za su taimaka maka ka zama miji nagari. Za su sa ka iya cika hakkinka a matsayin maigida.
18. Ta yaya saurayi zai yi shirin zama uba nagari?
18 Za ka iya zama uba. Bayan ka yi aure, za ku iya haifan yara. Wane darasi ne za ka iya koya daga wurin Jehobah game da zama uba nagari? Akwai darussa da yawa. (Afis. 6:4) Jehobah ya gaya wa ɗansa Yesu a gaban jamaꞌa cewa yana ƙaunar sa kuma ya amince da shi. (Mat. 3:17) Idan kana da yara, ka riƙa tabbatar musu da cewa kana ƙaunar su. Ka riƙa yaba musu don abubuwa masu kyau da suke yi. Ubanni da suke yin koyi da Jehobah suna taimaka wa yaransu su zama Kiristocin da suka manyanta. Za ka iya yin shirin zama uba nagari ta wajen kula da ꞌyan iyalinku da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Ka riƙa gaya musu cewa kana ƙaunar su kuma suna da muhimmanci a gare ka. (Yoh. 15:9) Yin hakan zai taimaka maka ka zama miji da kuma uba nagari a nan gaba. Amma kafin nan, za ka zama mai daraja a gun Jehobah kuma za ka taimaka wa iyalinka, da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya sosai.
MENE NE ZA KA RIƘA YI YANZU?
19-20. Mene ne zai taimaka wa samari su zama Kiristocin da suka manyanta? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
19 ꞌYanꞌuwa samari, ba haka kawai ne za ku zama Kiristocin da suka manyanta ba. Kuna bukatar ku yi koyi da mutanen da suke da halaye masu kyau, ku zama masu hankali, ku zama waɗanda mutane za su yarda da su, ku koyi ayyukan da za su taimaka muku a rayuwa, kuma ku yi shirin ɗaukan ƙarin hakkoki a nan gaba.
20 Idan kuka yi tunani a kan duka abubuwan da ya kamata ku yi, za ku iya gani kamar sun fi ƙarfinku. Amma za ku iya yin nasara. Ku tuna cewa Jehobah yana so ya taimaka muku. (Isha. 41:10, 13) Ban da haka, ꞌyanꞌuwanku maza da mata a ikilisiya za su taimaka muku. Idan ka zama irin mutumin da Jehobah yake so ka zama, za ka yi farin ciki sosai. Muna matuƙar ƙaunar ku, ꞌyanꞌuwanmu samari. Bari Jehobah ya yi muku albarka yayin da kuke yin iya ƙoƙarinku don ku zama Kiristocin da suka manyanta.—K. Mag. 22:4.
WAƘA TA 65 Mu Riƙa Samun Ci Gaba!
a Ana bukatar ꞌyanꞌuwa maza da suka manyanta a ikilisiya. A wannan talifin, za mu ga yadda ku ꞌyanꞌuwa matasa za ku zama Kiristocin da suka manyanta.
b Ka duba “Maꞌanar Kalmomi” a talifi na baya.
c Ka duba littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, darasi na 5 da 6 a Turanci.