Kana Samun Ci-gaba don Ka Manyanta Kamar Kristi Kuwa?
“Ka kai . . . cikakken mutum, zuwa misalin tsawon cikar Kristi.”—AFIS. 4:13.
WAKOKI: 69, 70
1, 2. Wane buri ne ya kamata kowane Kirista ya kasance da shi? Ka ba da misali.
SA’AD DA uwargida take sayan tumatir a kasuwa, ba ta zaɓan manya-manya ko kuma masu araha. Maimakon haka, za ta zaɓi jan tumatir masu kyau da za su ba da sinadarin gina jiki.
2 Hakazalika, Allah yana son bayinsa su manyanta. Burin Kirista shi ne ya zama bawan Allah da ya manyanta. Ko da mutum ya keɓe kansa ga Jehobah kuma an yi masa baftisma, manyantarsa ba ta tsaya a nan ba. Manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci da ke Afisa su zama waɗanda suka manyanta. Ya karfafa su su “kai zuwa ɗayantuwar imani na sanin Ɗan Allah, zuwa cikakken mutum, zuwa misalin tsawon cikar Kristi.”—Afis. 4:13.
3. Ta yaya yanayin da ke ikilisiyar da ke Afisa ya zo ɗaya da yanayin mutanen Jehobah a yau?
3 A lokacin da Bulus ya rubuta wannan wasikar ga ’yan’uwa da ke ikilisiyar Afisa, shekaru da yawa sun wuce da kafa ikilisiyar. Almajirai da yawa da ke cikin ikilisiyar sun riga sun manyanta, amma har ila wasu suna bukatar su yi hakan. Hakazalika, ’yan’uwa da yawa a yau sun daɗe suna bauta wa Jehobah kuma sun manyanta. Amma, wasu ba su manyanta ba. Alal misali, ana yi wa dubban mutane baftisma a kowace shekara, saboda haka, wasu suna bukatar su yi kokari don su manyanta. Kai kuma fa?—Kol. 2:6, 7.
YAYA KIRISTA YAKE MANYANTA?
4, 5. A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci da suka manyanta sun bambanta da juna, amma wane hali suke da shi duka? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)
4 Idan ka lura da nunannen tumatir a kasuwa, za ka ga cewa dukansu ba su yi kama ba. Duk da haka, dukansu suna da abin da ya nuna cewa sun nuna. Hakazalika, Kiristoci da suka manyanta suna iya fitowa daga kasashe ko wurare dabam-dabam. Kari ga haka, shekarun wasu da lafiyar jikinsu da abubuwa da suka shaida a rayuwa da halinsu da kuma al’adarsu sun bambanta. Duk da haka, dukan Kiristoci da suka karfafa dangantakarsu da Jehobah suna nuna halayen waɗanda da suka manyanta. Waɗanne halaye ke nan?
5 Bawan Jehobah da ya manyanta yana yin koyi da Yesu kuma yana ‘bin sawunsa’ sau da kafa. (1 Bit. 2:21) Yesu ya ce yana da muhimmanci mutum ya so Jehobah da dukan zuciyarsa da ransa da kuma hankalinsa. Kari ga haka, yana bukatar ya so makwabcinsa kamar ransa. (Mat. 22:37-39) Kirista da ya manyanta yana kokari ya bi wannan shawarar. Yana da dangantaka ta kud da kud da Jehobah kuma yana kaunar mutane sosai. Waɗannan abubuwan ne suka fi muhimmanci a rayuwarsa.
6, 7. (a) Waɗanne halaye ne Kirista da ya manyanta yake nunawa? (b) Wace tambaya ce ya kamata mu yi wa kanmu?
6 Kauna tana cikin halaye masu kyau da ruhu mai tsarki yake sa Kirista da ya manyanta ya nuna. (Gal. 5:22, 23) Halayen kamar tawali’u da kamewa da kuma jimrewa suna da muhimmanci har ila. Za su taimaka masa ya bi da mawuyacin yanayi ba tare da ɓacin rai ba. Kari ga haka, za su sa ya jimre yanayi na bakin ciki ba tare da ya karaya ba. Sa’ad da yake nazarin Littafi Mai Tsarki, yana binciken ka’idodin da za su taimaka masa ya tantance nagarta da mugunta. Shawarwarin da zai yanke bayan haka za su nuna cewa shi mutum ne mai dangantaka ta kud da kud da Jehobah. Alal misali, yana horar da lamirinsa don ya rika bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki. Kirista da ya manyanta yana da tawali’u kuma yana nuna cewa ja-gora da kuma ka’idodi da Jehobah yake bayarwa suna da muhimmanci fiye da nasa ra’ayi.a Yana yin wa’azi da kwazo kuma yana yin abubuwan da suke sa ’yan’uwa su kasance da haɗin kai a cikin ikilisiya.
7 Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah ko da ba mu daɗe ba, kowannenmu zai iya tambayar kansa, ‘Shin akwai wuraren da nake bukatar yin canje-canje don in bi misalin Yesu sau da kafa kuma in ci gaba da inganta ibadata?’
KIRISTOCI DA SUKA MANYANTA BA SA GUJE WA KOYARWA MASU WUYA
8. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya san nassosi kuma ya fahimci yadda ake amfani da su?
8 Yesu Kristi ya san Kalmar Allah sosai. Ko a lokacin da yake shekara 12, ya tattauna wasu batutuwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki da malamai a cikin haikali. “Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki da fahiminsa da magana da yake mayarwa.” (Luk. 2:46, 47) Daga baya, sa’ad da Yesu ya soma wa’azi, ya yi amfani da Kalmar Allah wajen ba da amsa ga abokan gābansa.—Mat. 22:41-46.
9. (a) Wane tsarin nazarin Littafi Mai Tsarki ne zai taimaka wa wanda yake so ya kyautata dangantakarsa da Jehobah? (b) Me ya sa muke nazarin Littafi Mai Tsarki?
9 Kirista da yake so ya manyanta yana bukata ya bi misalin Yesu kuma ya yi iya kokarinsa don ya fahimci Littafi Mai Tsarki da kyau. A koyaushe, yana bincikensa domin ya san cewa “abinci mai-karfi domin isassun mutane ne” ko kuma mutane da suka manyanta. (Ibran. 5:14) Hakika, Kirista da ya manyanta yana so ya sami ilimi ko kuma “sanin Ɗan Allah.” (Afis. 4:13) Shin kana karanta Kalmar Allah a kowace rana? Kana nazarin Littafi Mai Tsarki kuma kana bauta ta iyali a kowane mako? Yayin da kake nazarin Kalmar Allah, ka mai da hankali ga ka’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimake ka ka san ra’ayin Jehobah da kuma tunaninsa. Bayan haka, ka yi kokari ka bi waɗannan ka’idodin yayin da kake yanke shawarwari. Ta yin hakan, za ka kusaci Jehobah sosai.
10. Ta yaya Kirista da ya manyanta yake ɗaukan ka’idodin Allah?
10 Kirista da ya manyanta ya fahimci cewa ya dace ya san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Kari ga haka, ya san cewa yana da muhimmanci ya so umurnin Allah da kuma ka’idodinsa. Yana nuna hakan ta yadda yake son yin nufin Jehobah maimakon bin ra’ayin ’yan Adam. Ya yi aiki tukuru don ya canja tsarin rayuwarsa da halinsa da kuma tunaninsa. Yayin da Kirista yake waɗannan canje-canjen, yana yin koyi da halayen Kristi da aka tsara bisa ga nufin “Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” (Karanta Afisawa 4:22-24.) An rubuta Littafi Mai Tsarki bisa ja-gorar ruhu mai tsarki. Saboda haka, sa’ad da Kirista yake nazarin Littafi Mai Tsarki, ruhu mai tsarki zai taimaka masa ya kara sanin Littafi Mai Tsarki. Hakan zai sa ya kara kaunar Jehobah kuma ya inganta dangantakarsa da shi.
KU KASANCE DA HAƊIN KAI
11. Wane yanayi ne Yesu ya fuskanta sa’ad da yake sha’ani da ’yan’uwansa da kuma almajiransa?
11 Yesu kamili ne. Amma lokacin da yake duniya ya yi cuɗanya da ’yan Adam ajizai. Iyayensa da suka yi rainonsa ajizai ne kuma ya zauna tare da ’yan’uwansa ajizai. Har ma almajiransa sun nuna wasu halaye kamar girman kai da son kai. Alal misali, a yammar nan kafin a kashe Yesu, “gardama kuma ta tashi a tsakaninsu” game da wane ne “babba a cikinsu.” (Luk. 22:24) Amma Yesu ya tabbata cewa almajiransa ajizai za su manyanta kuma su kafa ikilisiya da za ta kasance da haɗin kai. A yammar, Yesu ya yi addu’a ga Ubansa da ke sama don manzaninsa su kasance da haɗin kai. Ya ce: “Domin su duka su zama ɗaya; kamar yadda kai, Uba, kana cikina, ni kuma a cikinka, domin su kuma su zama cikinmu . . . domin su zama ɗaya, kamar yadda mu ɗaya ne.”—Yoh. 17:21, 22.
12, 13. (a) Ta yaya Afisawa 4:15, 16 suka nuna cewa haɗin kai a cikin ikilisiya yana da muhimmanci sosai? (b) Ta yaya wani ɗan’uwa ya sha kan kasawa don ya kasance da haɗin kai da ’yan’uwa a cikin ikilisiya?
12 Kirista da ya manyanta yana yin abubuwan da ke sa ’yan’uwa a cikin ikilisiya su kasance da haɗin kai. (Karanta Afisawa 4:1-6, 15, 16.) Burin dukan Kiristoci shi ne su kasance da haɗin kai kuma su yi aiki da juna cikin lumana. Kalmar Allah ta ce idan muna so mu zauna cikin haɗin kai, wajibi ne mu kasance da tawali’u. Saboda haka, Kirista da ya manyanta yana aiki tukuru don ikilisiya ta kasance da haɗin kai ko da yana ganin kurakuran wasu. Shin sa’ad da wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta yi kuskure, yaya kake bi da yanayin? Ko kuma wane mataki ne kake ɗaukawa idan wani ɗan’uwa ya ɓata maka rai? Kana fushi har ka daina magana da shi ne? Ko kuma kana kokari ka yi sulhu da shi? Hakika, Kirista da ya manyanta yakan yi kokari ya magance matsalar maimakon ya daina magana da ɗan’uwan.
13 Ka yi la’akari da misalin Uwe. A dā, yana barin ajizancin ’yan’uwansa ya dame shi. Amma sai ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki da littafin Insight on the Scriptures don ya yi bincike game da rayuwar Dauda. Me ya sa ya yi nazarin game da rayuwar Dauda? Uwe ya ce: “Dauda ya yi fama da wasu Isra’ilawa da suka yi watsi da ka’idodin Jehobah. Alal misali, Sarki Saul ya so ya kashe shi, wasu mutane sun yi niyyar jifarsa da duwatsu, har ma matarsa ta yi masa ba’a. (1 Sam. 19:9-11; 30:1-6; 2 Sam. 6:14-22) Amma Dauda bai bar halin wasu ya sa shi ya yi sanyin gwiwa a bautarsa ga Jehobah ba. Kari ga haka, Dauda ya gafarta wa mutane, in ma ina bukatar in rika gafarta wa mutane. Abin da na koya a nazarin ya canja yadda nake bi da ’yan’uwana sa’ad da suka yi kuskure. Yanzu ba na lissafin kurakuran ’yan’uwana. A maimakon haka, ina kokarin yin abubuwan da za su sa ’yan’uwa su kasance da haɗin kai a cikin ikilisiya.” Shin kana yin abubuwan da za su sa ’yan’uwa su kasance da haɗin kai a cikin ikilisiya?
KA YI ABOTA DA WAƊANDA SUKE YIN NUFIN ALLAH
14. Waɗanne irin abokai ne Yesu ya zaɓa?
14 Yesu Kristi ya so dukan mutane. Mutane dabam-dabam, maza da mata da yara da kuma tsofaffi sun saki jiki yayin da suke tare da Yesu. Amma, bai mai da kowa abokinsa na kud da kud ba. A maimakon haka, ya gaya wa manzanninsa masu aminci: “Ku ne abokaina idan kun yi abin da na umurce ku.” (Yoh. 15:14) Yesu ya zaɓi waɗannan abokai ne tsakanin almajiransa waɗanda suke bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. Shin kana zaɓan abokai na kud da kud tsakanin waɗanda suke bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya? Me ya sa yin hakan yake da muhimmanci?
15. Ta yaya matasa za su amfana idan suka yi cuɗanya da Kiristoci da suka manyanta?
15 Tumatiri sukan nuna da kyau idan akwai rana. Hakazalika, zumunci da muke mora tare da ’yan’uwanmu zai taimaka mana mu zama Kiristoci da suka manyanta. Watakila kai matashi ne da yake kokarin tsai da shawara game da abin da zai yi a rayuwa. Zai dace ka yi cuɗanya da waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah kuma suna kyautata haɗin kai tsakanin ’yan’uwa. Mai yiwuwa sun fuskanci matsaloli a rayuwa kuma sun jimre kalubale a bautarsu ga Jehobah. Irin waɗannan mutane za su taimake ka ka zaɓi tafarki mafi kyau a rayuwa. Yin cuɗanya sosai da irin waɗannan ’yan’uwan zai taimaka maka ka tsai da shawarwari masu kyau kuma ka manyanta.—Karanta Ibraniyawa 5:14.
16. Ta yaya ’yan’uwa da suka manyanta suka taimaka wa wata matashiya a cikin ikilisiyarsu?
16 Alal misali, Helga ta tuna cewa a shekararta na karshe a makaranta, yawancin abokan ajinta suna magana game da makasudan da suka kafa. Da yawa a cikinsu suna son su je jami’a domin su sami aiki mai kyau kuma su yi nasara a rayuwa. Helga ta tattauna yanayin da abokanta da ke ikilisiyarsu. Ta ce: “Da yawa a cikinsu sun girme ni kuma sun taimaka mini sosai. Sun karfafa ni na soma hidima ta cikakken lokaci. Bayan haka, na yi shekara biyar a hidimar majagaba. Yanzu, bayan shekaru da yawa, ina farin ciki cewa na yi amfani da kuruciyata a hidimar Jehobah. Ban yi nadama cewa na yi hakan ba.”
17, 18. Ta yaya yin abota da waɗanda suka manyanta za su taimaka mana mu cim ma burinmu a rayuwa?
17 Za mu zama Kiristoci da suka manyanta idan muka yi koyi da Yesu. Za mu kusaci Jehobah sosai kuma za mu so mu ci gaba da bauta masa. Bawan Allah da ya manyanta yana bauta wa Jehobah da dukan kwazonsa. Yesu ya karfafa mabiyansa sa’ad da ya ce: “Ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu-kyau, su girmama Ubanku wanda ke cikin sama.”—Mat. 5:16.
18 Kamar yadda muka koya, Kirista da ya manyanta zai taimaka wa ’yan’uwa a cikin ikilisiya sosai. Kuma za a ga hakan a yadda yake amfani da lamirinsa. Ta yaya lamirinmu zai taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau? Ta yaya za mu daraja shawarwari da ’yan’uwa masu bi suka tsai da bisa lamirinsu? Za mu tattauna waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.
a Alal misali, za a iya gaya wa kwararrun ’yan’uwa da suka tsufa su bar wani gatan da suke da shi kuma su tallafa wa ’yan’uwa masu kuzari da aka ba wa wannan gatan.