TALIFIN NAZARI NA 14
WAƘA TA 56 Ka Riƙe Gaskiya
‘Ku Yi Ƙoƙari Ku Manyanta’
“Mu yi ƙoƙari mu manyanta.”—IBRAN. 6:1.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu koyi yadda Kirista da ya manyanta yake yin tunani da kuma aikata abubuwa yadda Jehobah yake so.
1. Mene ne Jehobah yake bukata daga gare mu?
MAꞌAURATA suna farin ciki sosai saꞌad da suka haifi ɗansu na farko. Ko da yake suna ƙaunar jaririnsu sosai, ba za su so ya ci-gaba da zama jariri har abada ba. Za su damu sosai idan jaririn ba ya girma. Haka ma, Jehobah yana farin ciki saꞌad da muka soma koya game da shi. Amma ba Ya so mu tsaya haka, Yana so mu yi ta yin girma. (1 Kor. 3:1) Shi ya sa ya ce mu zama da tunani “irin na manya.”—1 Kor. 14:20.
2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 Yaya Kirista da ya manyanta yake tunani da yin abubuwa? Ta yaya za mu zama Kiristocin da suka manyanta? Ta yaya yin nazarin koyarwa masu zurfi (abinci mai kauri) zai taimaka mana mu ƙara yin kusa da Jehobah? Kuma me ya sa ya kamata mu guji tunanin cewa mun manyanta, don haka ba ma bukatar mu ƙara yin ƙoƙari? A wannan talifin, za mu ga amsoshin tambayoyin nan.
YAYA KIRISTA DA YA MANYANTA YAKE TUNANI DA YIN ABUBUWA?
3. Mene ne ake nufi da mutum ya zama Kirista da ya manyanta?
3 A Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “manya” tana iya nufin “wanda ya yi girma,” ko “cikakke,” ko kuma “kamili.”a (1 Kor. 2:6) Idan aka ce mutum ya zama Kirista da ya manyanta, ana nufin ya ci-gaba da ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah har sai ya kusace Shi sosai. Za mu iya kwatanta hakan da yadda jariri yake girma har ya manyanta. Amma, ko da mun manyanta, kada mu daina yin ƙoƙari a wannan fannin. (1 Tim. 4:15) Dukanmu, har da matasa, za mu iya zama Kiristocin da suka manyanta. Me yake nuna cewa Kirista ya manyanta?
4. Waɗanne halaye ne Kirista da ya manyanta yake da su?
4 Kirista da ya manyanta yana bin dukan dokokin Allah, ba ya zaɓan wanda zai bi da wanda ba zai bi ba. Amma shi ajizi ne, don haka zai yi kurakurai. Duk da haka, a koyaushe yana yin iya ƙoƙarinsa ya riƙa yin tunani da aikata abubuwa yadda Jehobah yake so. Yana kasancewa da sabon hali, kuma yakan zama da raꞌayi irin na Jehobah. (Afis. 4:22-24) Ya riga ya koyi yadda zai yi amfani da dokoki da kuma ƙaꞌidodin Jehobah saꞌad da yake yanke shawarwari. Don haka, ba ya bukatar jerin dokokin da za su gaya masa abin da zai yi da wanda ba zai yi ba. Idan ya yanke wata shawara, yana yin iya ƙoƙarinsa ya yi abin da ya ce zai yi.—1 Kor. 9:26, 27.
5. Mene ne zai iya faruwa da Kirista da bai manyanta ba? (Afisawa 4:14, 15)
5 A wani ɓangaren kuma, bai da wuya a ruɗi Kirista da bai manyanta ba. Yana iya yin saurin yarda da labarai da ba gaskiya ba ko jita-jita da ake yaɗawa a kafofin yaɗa labarai. Yana ma iya gaskatawa da koyarwar ꞌyan ridda.b (Karanta Afisawa 4:14, 15.) Yana iya saurin kishin mutane, ko ya yi faɗa da su, ko ya zama mai saurin fushi, kuma yana yawan yin abin da bai dace ba saꞌad aka jarrabce shi.—1 Kor. 3:3.
6. Me ya sa za mu iya kwatanta yadda Kirista yake manyanta da yadda yaro yake girma? (Ka kuma duba hoton.)
6 Kamar yadda muka ambata ɗazu, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda mutum zai zama Kirista da ya manyanta da yadda jariri yake girma. Akwai abubuwa da yawa da yaro bai sani ba, don haka yana bukatar wanda ya manyanta ya yi masa ja-goranci. Alal misali, mahaifiya za ta iya gaya wa ꞌyarta ta riƙe hannunta idan za su tsallake titi. Yayin da ꞌyar take girma, mahaifiyar za ta iya barin ta ta tsallake titin da kanta, amma za ta tuna mata cewa ta duba hanya da kyau kafin ta tsallake titin. Saꞌad da ꞌyar ta yi girma, za ta san yadda za ta guje wa irin waɗannan haɗarurruka. Yara suna bukatar taimako daga wurin waɗanda suka manyanta. Haka ma, Kiristoci da ba su manyanta ba a kullum suna neman taimako daga Kiristoci da suka manyanta don su iya ƙin yin abin da zai ɓata wa Jehobah rai kuma su yanke shawarwari masu kyau. Amma idan Kiristoci da suka manyanta suna so su yanke wata shawara, su da kansu sukan yi tunani a kan ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki don su san raꞌayin Jehobah game da batun kuma su yi abin da ya dace.
7. Kiristocin da suka manyanta suna bukatar taimako daga wurin wasu?
7 Shin hakan yana nufin cewa Kirista da ya manyanta ba ya bukatar taimakon wani ne? Aꞌa. A wasu lokuta su ma suna bukatar taimako. Kirista da bai manyanta ba zai so wasu su gaya masa abin da zai yi ko su yanke masa shawarar da ya kamata shi ya yanke da kansa. Amma wanda ya manyanta ba ya haka. Kirista da ya manyanta zai iya neman shawara, amma ya san cewa Jehobah yana so “kowa ya ɗauki kayan kansa.”—Gal. 6:5.
8. A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci da suka manyanta suka bambanta da juna?
8 Kamar yadda kamannin mutane sun bambanta, haka ma Kiristocin da suka manyanta suna da halaye dabam-dabam. Wasu na da hikima sosai, wasu na da ƙarfin zuciya, wasu masu alheri ne sosai, wasu kuma suna da tausayi. Kiristoci biyu da suka manyanta suna iya samun kansu a yanayi ɗaya kuma su tsai da shawarwarin da suka bambanta, amma sun jitu da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. Hakan yana yawan faruwa idan babu doka a kan wani batu kuma an ce kowa ya yanke shawarar da ba za ta dami zuciyarsa ba. Don haka, ba za su shariꞌanta juna ba. A maimako, za su yi iya ƙoƙarinsu domin su kasance da haɗin kai.—Rom. 14:10; 1 Kor. 1:10.
TA YAYA ZA MU ZAMA KIRISTOCI DA SUKA MANYANTA?
9. Shin za mu iya zama Kiristoci da suka manyanta haka kawai? Ka bayyana.
9 Jariri yakan yi girma ba tare da ya yi wani ƙoƙari ba, amma ba haka kusantar Jehobah ba, muna bukatar mu sa ƙwazo. Alal misali, ꞌyanꞌuwan da suke Korinti sun amince da waꞌazin da suka ji, sun yi baftisma, an shafe su da ruhu mai tsarki kuma sun amfana daga koyarwar da manzo Bulus ya yi musu. (A. M. 18:8-11) Duk da haka, shekaru da yawa bayan sun yi baftisma, Kiristocin nan ba su manyanta ba. (1 Kor. 3:2) Mene ne za mu yi don kada hakan ya faru da mu?
10. Mene ne mutum yake bukatar yi don ya zama Kirista da ya manyanta? (Yahuda 20)
10 Kafin mutum ya zama Kirista da ya manyanta, yana bukatar ya yi niyyar yin hakan. “Marasa tunani” da waɗanda ba sa so su sami ci-gaba, ba za su taɓa manyanta ba. (K. Mag. 1:22) Ba ma so mu zama kamar waɗanda sun yi girma, amma har ila suna so iyayensu su riƙa yanke musu shawarwari. A maimako, mu san cewa hakkinmu ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. (Karanta Yahuda 20.) Idan har yanzu kana ƙoƙari ka zama Kirista da ya manyanta, ka roƙi Jehobah ya ba ka ‘niyyar’ yin hakan, kuma ya ba ka ƙarfin yin sa.—Filib. 2:13.
11. Mene ne Jehobah ya ba mu don ya taimaka mana mu zama Kiristocin da suka manyanta? (Afisawa 4:11-13)
11 Jehobah ya san cewa ba za mu iya zama Kiristocin da suka manyanta da ƙarfinmu kawai ba. Shi ya sa ya ba mu makiyaya da malamai a ikilisiya da za su taimaka mana mu zama “cikakkun mutane, mu kuma kai matsayi na dukan cikar Almasihu.” (Karanta Afisawa 4:11-13.) Jehobah yana kuma ba mu ruhunsa mai tsarki don ya taimaka mana mu kasance da ‘tunani na Almasihu.’ (1 Kor. 2:14-16) Ƙari ga haka, Jehobah ya sa an rubuta littattafan Linjila da suka bayana mana yadda Yesu yake tunani da yadda ya yi magana da yadda ya yi abubuwa saꞌad da yake duniya. Idan ka bi halin Yesu da yadda yake tunani, za ka zama Kirista da ya manyanta.
YADDA KOYARWA MASU ZURFI ZA SU TAIMAKA MANA
12. Mene ne “koyarwar nan ta farko” ta ƙunsa?
12 Ban da “koyarwar nan ta farko,” muna bukatar mu yi nazarin koyarwa masu zurfi don mu manyanta. Wasu daga cikin koyarwar nan ta farko su ne tuba, bangaskiya, baftisma da kuma tashin matattu. (Ibran. 6:1, 2) Suna cikin koyarwa da ya kamata kowane Kirista ya yi imani da su. Shi ya sa manzo Bitrus ya ambata su saꞌad da yake yi wa mutane waꞌazi a ranar Fentakos. (A. M. 2:32-35, 38) Kafin mu zama mabiyan Yesu, dole ne mu yi imani da su. Alal misali, Bulus ya ce duk wanda ya ƙi amincewa da tashin matattu ba zai iya zama mabiyin Yesu ba. (1 Kor. 15:12-14) Amma bai kamata mu gamsu da waɗannan koyarwa masu sauƙin fahimta kawai ba.
13. Mene ne za mu yi idan muna so mu amfana daga abinci mai kauri da aka ambata a Ibraniyawa 5:14? (Ka kuma duba hoton.)
13 Koyarwa masu zurfi ko kuma abinci mai ƙauri ya ƙunshi dokokin Jehobah da kuma ƙaꞌidodinsa. Suna taimaka mana mu san yadda yake tunani. Amma ba haka yake da koyarwa masu sauƙin fahimta ba. Don mu amfana daga abinci mai kaurin nan, muna bukatar mu yi nazarin Kalmar Allah, mu yi tunani mai zurfi a kan abin da muka karanta kuma mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi abin da muka koya. Idan muka yi hakan, za mu koya wa kanmu yadda za mu yanke shawarwarin da za su faranta wa Jehobah rai.c—Karanta Ibraniyawa 5:14.
14. Ta yaya Bulus ya taimaka wa Korintiyawan su zama Kiristocin da suka manyanta?
14 Idan babu doka a kan batu, yana yi wa Kiristoci da ba su manyanta ba wuya su yanke shawara. Wasu suna ganin cewa tun da babu wata doka game da batun, za su yi duk abin da suka ga dama. Wasu kuma za su ce a ba su doka a yanayin da ba a bukatar doka. Alal misali, da alama Kiristocin da ke Korinti sun gaya wa Bulus ya kafa musu doka game da cin naman da aka miƙa wa gumaka. Maimakon Bulus ya gaya musu abin da za su yi, ya bayyana musu cewa kowa yana bukatar ya yi abin da ba zai dami zuciyarsa ba, kuma kowa yana da “ꞌyancin” yin zaɓi. Ya ambaci wasu ƙaꞌidodi da za su taimaka wa mutum ya yanke shawarar da ba za ta sa zuciyarsa ta riƙa damunsa ko ta sa wasu tuntuɓe ba. (1 Kor. 8:4, 7-9) Ta haka, Bulus ya taimaka ma Korintiyawan su manyanta kuma su iya yin amfani da hankalinsu don su san abu mai kyau da marar kyau, maimakon su bi raꞌayin wasu ko kuma su bukaci a kafa musu doka.
15. Ta yaya Bulus ya taimaka wa Ibraniyawan su zama Kiristoci da suka manyanta?
15 Akwai darasi mai kyau da za mu koya daga abin da Bulus ya rubuta wa Kiristoci Ibraniyawa. Wasunsu ba su ci-gaba da manyanta ba. Maimakon su ci “abinci mai kauri,” sun koma “shan nono kawai.” (Ibran. 5:12) Sun ƙi su koya kuma su amince da sabbin abubuwan da Jehobah yake koya musu ta wurin ikilisiyarsa. (K. Mag. 4:18) Alal misali, Yahudawa da yawa sun ci-gaba da ɗaukaka Koyarwar Musa bayan an riga an kawar da ita wajen shekaru 30 da suka shige, wato saꞌad da Yesu ya ba da hadayar ransa. (Rom. 10:4; Tit. 1:10) Ai shekaru 30 sun isa Yahudawan su san cewa ba sa bukatar Dokar Musa kuma. Idan muka karanta wasiƙar da Bulus ya aika wa Ibraniyawan, za mu ga cewa abubuwa masu zurfi yake koya musu. Wasiƙarsa ta taimaka ma Kiristocin nan su ga cewa sabon tsari da Jehobah yake amfani da shi don ya sa su bauta masa ta wurin Yesu, ya fi wanda suke bi a dā. Kuma wasiƙar ta sa sun ci-gaba da yin waꞌazi da ƙarfin zuciya duk da hamayya da Yahudawa suke yi musu.—Ibran. 10:19-23.
DALILIN DA YA SA MUKE BUKATAR MU CI-GABA DA YIN ƘOƘARI
16. Bayan mun zama Kiristocin da suka manyanta, mene ne muke bukatar mu yi?
16 Idan muka zama Kiristocin da suka manyanta, bai kamata mu tsaya a nan ba. Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci-gaba da zama Kiristocin da suka manyanta. Don haka, kada mu ɗauka cewa da yake mun manyanta, ba ma bukatar mu yi ƙoƙari. (1 Kor. 10:12) Zai dace mu ci-gaba da ‘gwada kanmu’ don mu tabbatar cewa muna samun ci-gaba a ibadarmu ga Jehobah.—2 Kor. 13:5.
17. Ta yaya wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Kolosiyawan ya nuna cewa yana da muhimmanci mu ci-gaba da zama Kiristoci da suka manyanta?
17 A wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Kolosiyawa, ya sake ambata dalilin da ya sa ya kamata mu ci-gaba da zama Kiristoci da suka manyanta. Kolosiyawan sun riga sun manyanta, duk da haka, Bulus ya gargaɗe su cewa su yi hankali don kada a ruɗe su da raꞌayoyin mutanen duniya. (Kol. 2:6-10) Wani mai suna Abafaras ya san ꞌyanꞌuwan sosai, don haka ya yi ta yin adduꞌa don ꞌyanꞌuwan su “zama cikakku” ko kuma ꞌyanꞌuwan da suka manyanta. (Kol. 4:12) Mene ne hakan ya koya mana? Bulus da Abafaras sun san cewa Kiristoci suna bukatar taimakon Jehobah kuma suna bukatar su ci-gaba da ƙarfafa dangantakarsu da shi, don abin da zai sa su ci-gaba da zama Kiristoci da suka manyanta ke nan. Suna kuma so Kolosiyawan su ci-gaba da yin hakan duk da matsalolin da suke fuskanta.
18. Mene ne zai iya faruwa da Kirista da ya manyanta? (Ka kuma duba hoton.)
18 Bulus ya gargaɗi Ibraniyawan cewa idan Kirista bai ci-gaba da manyanta ba, zai iya rasa amincewar Jehobah har abada. Hakan zai iya faruwa idan ya ci-gaba da ƙin yi wa Allah biyayya, kuma ya kasa tuba. Abin farin ciki shi ne yanayin Ibraniyawan bai kai hakan ba. (Ibran. 6:4-9) Waɗanda suka daina zuwa waꞌazi ko halartan taro kuma fa, ko waɗanda aka yi musu yankan zumunci amma suka tuba daga baya? Da yake sun tuba da gaske, su ba kamar waɗanda Bulus ya yi magana a kai ba ne, wato waɗanda Allah ya daina amincewa da su. Amma bayan sun komo ga Jehobah, suna bukatar taimakonsa. (Ezek. 34:15, 16) Dattawa suna iya sa wani Kirista da ya manyanta ya taimaka ma ꞌyanꞌuwan nan su sake aminan Jehobah.
19. Wane maƙasudi ne ya kamata ka kafa wa kanka?
19 Idan kana iya ƙoƙarinka don ka zama Kirista da ya manyanta, muna so ka san cewa za ka iya yin hakan! Saboda haka, ka ci-gaba da yin nazarin koyarwa masu zurfi da kuma kasancewa da raꞌayi irin na Jehobah. Idan kuma ka riga ka manyanta, ka yi iya ƙoƙarinka don ka ci-gaba da zama hakan har abada.
MECE CE AMSARKA?
Mene ne ake nufi da mutum ya zama Kirista da ya manyanta?
Ta yaya za mu zama Kiristoci da suka manyanta?
Me ya sa ya kamata mu guji tunanin cewa ba ma bukatar mu yi ƙoƙari tun da mun riga mun zama Kiristocin da suka manyanta?
WAƘA TA 65 Mu Riƙa Samun Ci Gaba!
a Ko da yake a Nassosin Ibrananci babu kalmomin nan “manya” da “waɗanda ba manya ba,” amma akwai kalmomin da suke da maꞌana ɗaya da su. Alal misali, a littafin Karin Magana, an nuna bambancin wani matashi marar tunani da wani da yake da hikima da kuma ganewa.—K. Mag. 1:4, 5.
b Ka duba talifin nan “Marar Wayo Yana Gaskata Kowace Magana” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba 2015, shafuffuka na 30-32.
c Ka duba talifin nan “Abubuwan da Za Ku Iya Yin Nazari a Kai” a wannan Hasumiyar Tsaro.
d BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa yana bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki saꞌad da yake zaɓan abin da zai kalla.