Maganar Jehobah Rayayyiya Ce
Darussa Daga Littafin Mahukunta
MENENE Jehobah ya yi sa’ad da mutanensa suka juya masa baya kuma suka fara bauta wa allolin ƙarya? Idan suka ƙi yi masa biyayya a kai a kai amma suka nemi ya taimaka musu a lokacin da suke cikin wahala fa? Jehobah ya yi musu tanadin hanyar tsira kuwa a lokacin? Littafin Mahukunta ya amsa waɗannan da wasu muhimman tambayoyi. Annabi Sama’ila ne ya rubuta shi, a kusan shekara ta 1100 K.Z., yana ɗauke ne da abubuwa da suka auku cikin shekaru 330—daga mutuwar Joshuwa zuwa naɗin sarkin Isra’ila na fari.
Da yake yana cikin kalmomi ko saƙonni masu ƙarfi na Allah, littafin Mahukunta yana da muhimmanci a gare mu sosai. (Ibraniyawa 4:12) Labarai masu ban sha’awa da suke ciki, sun ba mu fahimi game da mutuntakar Allah. Abubuwan da muka koya daga ciki sun ƙarfafa bangaskiyarmu kuma sun taimaka mana mu riƙe “rai wanda yake na hakika,” rai madawwami a cikin sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta. (1 Timoti 6:12, 19; 2 Bitrus 3:13) Ayyukan ceto da Jehobah ya yi domin mutanensa sun ba mu haske game da ceto mafi girma da zai yi a nan gaba ta hannun Ɗansa, Yesu Kristi.
ME YA SA AKE BUKATAR MAHUKUNTA?
(Littafin Mahukunta 1:1–3:6)
Bayan sun ci sarakunan ƙasashen Ka’anan da yaƙi a ƙarƙashin shugabancin Joshuwa, kowace ƙabilar Isra’ila ta tafi inda gadōnta yake kuma ta gaji ƙasar. Amma, Isra’ilawan sun ƙi su kori mazauna ƙasar. Kuma hakan ya zama tarko a garesu.
Tsararraki da suka taso bayan zamanin Joshuwa kuwa ‘sun manta da Ubangiji da abubuwan da ya yi wa Isra’ila.’ (Littafin Mahukunta 2:10) Bugu da ƙari, mutanen suka fara auren Kan’aniyawa kuma suka fara bauta wa allolinsu. Saboda haka, Jehobah ya bayar da su ga hannun abokan gabansu. Sa’ad da zaluncin ya yi musu yawa, sai ’ya’yan Isra’ila suka yi kira ga Allah na gaskiya don taimako. A cikin irin wannan yanayi na addinai da zaman jama’a, da siyasa ne aukuwa da ya zama tarihin mahukunta waɗanda Jehobah ya naɗa domin su ceci mutanensa daga hannun abokan gabansu ya faru.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
1:2, 4—Me ya sa aka zaɓi Yahuza ta zama ƙabila ta farko da za ta fara gadōn ƙasar da aka ba ta? Kamar yadda aka sani, ƙabilar Ra’ubainu ɗan farin Yakubu ne ya kamata ta sami wannan gatar. Amma a cikin annabcinsa kafin ya mutu, Yakubu ya annabta cewa Ra’ubainu ba zai fi ’yan’uwansa daraja ba, domin ya yi hasarar matsayinsa na ɗan fari. An warwatsa Saminu da Lawi a cikin Isra’ila, domin sun aikata cikin fushi. (Farawa 49:3-5, 7) Wanda kuma zai sami wannan gatar shi ne Yahuza, ɗan Yakubu na huɗu. Saminu, wanda ke bin Yahuza, ya sami ƙaramin ƙasa wadda aka warwatsa a cikin yankin Yahuza.a—Joshuwa 19:9.
1:6, 7—Me ya sa ake datse manyan yatsu na hannu da kafa na sarakunan da aka ci a yaƙi? Mutumin da ya rasa manyan yatsunsa na kafa da hannu ya sami naƙasa ke nan, don haka, ba zai iya yin aikin soja ba. Idan babu manyan yatsun hannu ta yaya soja zai riƙe takobi ko mashi? Kuma rashin manyan yatsu na kafa zai hana yin tafiya da kyau.
Darussa Dominmu:
2:10-12. Dole ne mu dinga nazarin Littafi Mai Tsarki domin kada mu ‘manta da yawan alherin Jehobah.’ (Zabura 103:2) Iyaye suna bukatan su saka gaskiyar Kalmar Allah cikin zukatan yaransu.—Maimaitawar Shari’a 6:6-9.
2:14, 21, 22. Jehobah yana ƙyale munanan abubuwa su faru ga mutanensa marasa biyayya domin wani dalili—don ya yi musu horo, domin ya gyara su, ko kuma domin ya maido su wurinsa.
JEHOBAH YA NAƊA MAHUKUNTA
(Littafin Mahukunta 3:7–16:31)
Labari mai ban sha’awa na nasarar da mahukunta suka samu ya soma ne sa’ad da Otniyel ya kawo ƙarshen bauta ta shekaru takwas da Isra’ilawa suka yi wa sarkin Mesofotamiya. Mahukunci Ehud ya kashe Eglon sarki mai ƙiba na Mowabawa da dabara. Shamgar wanda jarumi ne, shi kaɗai ya kashe Filistiyawa 600 da tsinken korar shanun noma. Domin ƙarfafa da ya samu daga wurin Debora wadda annabiya ce da kuma goyon bayan Jehobah, Barak da sojojinsa guda dubu goma sun sami nasara bisa sojojin Sisera masu ƙarfi. Jehobah ya naɗa Gidiyon kuma ya ba shi da mutanensa 300 nasara bisa Madayanawa.
Ta hannun Yefta, Jehobah ya ceci Isra’ilawa daga hannun Ammonawa. Tola, Yayir, Ibzan, Eglon, da Abdon suna cikin mutane 12 da suka yi wa Isra’ila hukunci. Samson wanda ya yaƙi Filistiyawa, shi ne mahukunci na ƙarshe.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
4:8—Me ya sa Barak ya nace cewa sai annabiya Debora ta bi shi zuwa bakin daga? Babu shakka, Barak ya ga cewa ba zai iya yaƙan sojojin Sisera shi kaɗai ba. Amma ganin annabiyar tana tare da su zai tabbata musu cewa Allah na tare da su kuma hakan zai ba su ƙarfi. Nacewar da Barak ya yi cewa sai Debora ta bi shi, ba alamar rauni ba ne, amma alama ce ta bangaskiya mai ƙarfi.
5:20—Ta yaya ne taurari daga sama suka yi yaƙi a madadin Barak? Littafi Mai Tsarki bai ce ko wannan ya ƙunshi taimako daga mala’iku ba, ko yayyafin duwatsu waɗanda masu hikima na Sisera suka ce ishara ce ta masifa, ko kuwa abin da wasu masana taurari na Sisera suka ce zai faru wanda ya kasance ƙarya. Amma, babu shakka, Allah ya saka hannu a wannan al’amari.
7:1-3; 8:10—Me ya sa Jehobah ya ce sojojin Gidiyon su 32,000 sun yi wa sojojin magabta su 135,000 yawa? Hakan ya faru ne domin Jehobah ne zai ba Gidiyon da sojojinsa nasara. Allah ba ya son su yi tunanin cewa sune suka ci Madayanawa a yaƙi da ƙarfinsu.
11:30, 31—Sa’ad da yake yin alkawarinsa, hadayar mutum ne Yefta ya yi tunanin bayarwa? Wannan ko kusa ba ta cikin zuciyar Yefta, domin Doka ta ce: “Kada a tarar da wani daga cikinku wanda zai sa ’yarsu ko ɗansu ya wuce ta tsakiyar wuta.” (Maimaitawar Shari’a 18:10) Amma, Yefta ya yi niyyar ba da mutum ne ba dabba ba. Isra’ilawa ba sa kiwon dabbobin da suke yin hadaya da su a gidajensu. Kuma ba da hadayar dabba ba za ta kasance da wani muhimmanci ba. Ƙila Yefta ya sani cewa ’yarsa ce za ta fito daga gidansa ta tarye shi. Ita ce za a miƙa “hadayar ƙonawa” domin za a ba da ita musamman ga hidimar Jehobah a haikalinsa.
Darussa Dominmu:
3:10. Samun nasara wajen biɗan abubuwa na ruhaniya ya dangana ne a kan ruhun Jehobah, ba hikimar mutane ba.—Zabura 127:1.
3:21. Ehud ya yi amfani da takobinsa cikin basira da kuma gaba gaɗi. Dole ne mu kasance gwanaye wajen yin amfani “da takobin Ruhu, wato Maganar Allah.” Wannan na nufin cewa dole ne mu yi amfani da Nassosi da gaba gaɗi a hidimarmu.—Afisawa 6:17; 2 Timoti 2:15.
6:11-15; 8:1-3, 22, 23. Filakon da Gidiyon ya nuna ya koya mana muhimman darussa guda uku: (1) Idan mun sami gatar hidima, ya kamata mu yi bimbini a kan hakkin da ta ƙunsa, maimakon suna ko ɗaukaka da ke tattare da ita. (2) Hikima ce mu nuna filako sa’ad da muke bi da waɗanda suke son su yi faɗa da mu. (3) Filako na kāre mu daga neman ɗaukaka.
6:17-22, 36-40. Ya kamata mu mai da hankali domin “ba kowane ruhu za [mu] gaskata ba.” Maimakon haka, muna bukatar mu “jarraba [mu] gani ko na Allah ne.” (1 Yahaya 4:1) Hikima ce sabon dattijo ya tuntuɓi gogaggen dattijo domin ya tabbata cewa shawarar da zai bayar daga Kalmar Allah ce.
6:25-27. Gidiyon ya yi amfani da hikima domin kada ya ba masu yin adawa da shi haushi. Sa’ad da muke wa’azin bishara, mu mai da hankali kada mu ba mutane haushi ba gaira ba dalili ta yadda muke magana.
7:6. Sa’ad da ya zo ga yi wa Jehobah hidima, dole ne mu kasance kamar sojoji 300 na Gidiyon—a shirye a faɗake.
9:8-15. Wawanci ne mu kasance da girman kai kuma mu kasance da dogon buri na neman ɗaukaka ko iko!
11:35-37. Misali mai kyau na Yefta babu shakka, ya taimaka wa ’yarsa ta kasance da ƙaƙƙarfan bangasikiya da hali na sadaukar da kai. A yau iyaye suna iya ƙafa irin wannan misalin ga yaransu.
11:40. Idan muka yaba wa wanda ya yi hidimar Jehobah da son rai hakan za ta ƙarfafa shi.
13:8. Sa’ad da suke koyar da ’ya’yansu, iyaye suna bukatar su yi wa Jehobah addu’a domin ya yi musu ja-gora kuma su bi ja-gorarsa.—2 Timoti 3:16.
14:16, 17; 16:16. Matsa wa mutum da yawan kuka ko mita na iya lalata dangantaka.—Karin Magana 19:13; 21:19.
WASU LAIFUFFUKA A ISRA’ILA
(Littafin Mahukunta 17:1–21:25)
Sashe na ƙarshe na littafin Mahukunta na ɗauke ne da muhimman labarai guda biyu. Na farko ya shafi wani mutumi ne mai suna Mika, wanda ya kafa gunki a gidansa kuma ya ɗauki wani Balawi ya zama masa firist. Bayan sun halaka birnin Layish, Danawa suka gina birninsu kuma suka sa masa suna Dan. Sun yi amfani da gunkin Mika da firist dinsa, suka kafa wata irin bauta a Dan. Babu shakka, an ci Layish a yaƙi kafin mutuwar Joshuwa.—Joshuwa 19:47.
Aukuwa na biyu ya faru ne ba da daɗewa ba bayan mutuwar Joshuwa. Lalatar da wasu mutanen Biliyaminu mazauna Gibeya suka yi, ya sa aka kusa halaka dukan ƙabilar Biliyaminu—mutane 600 ne kawai suka tsira. Amma wani shirin da aka yi ya sa sun sami mata, kuma yawansu ya ƙaru zuwa mayaƙa kusan 60,000 a lokacin sarautar Dauda.—1 Tarihi 7:6-11.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
17:6; 21:25—Idan “kowa yana ta yin yadda ya ga dama,” hakan zai jawo rashin jituwa ne? Ba lalle ba ne, domin Jehobah ya yi tanadi masu yawa domin ja-gorar mutanensa. Ya ba su Doka da firistoci domin ilimintar da su a hanyarsa. Ta yin amfani da Urim da Tummin, babban firist yana iya tuntuɓar Allah a kan batutuwa masu muhimmanci. (Fitowa 28:30) Kuma kowane birni yana da dattawan da za su ba da gargaɗi mai kyau. Sa’ad da ɗan Isra’ila ya ba da kansa ga waɗannan tanadodi, yana da tsari mai kyau ga lamirinsa. Yin “yadda ya ga dama” a wannan azancin zai zama abu mai kyau. A wani ɓangare kuma, idan mutum ya ƙi bin Doka kuma ya yanke wa kansa shawara game da halin da zai bi da ibada da zai yi, sakamakon zai zama da muni.
20:17-48—Me ya sa Jehobah ya ƙyale ƙabilar Biliyaminu ta fatattaki sauran ƙabilun sau biyu, duk da yake tana bukatar horo? Jehobah ya ƙyale ƙabilu masu aminci su sha wahala ne da farko, domin ya gwada ƙudurin da suka yi na kawar da mugun abu daga Isra’ila.
Darussa da Za Mu Koya:
19:14, 15. Halin karɓan baƙi da mutanen Gibeya suka ƙi nunawa alama ce ta hali marar kyau. An aririci Kiristoci su “himmantu ga yi wa baƙi alheri.”—Romawa 12:13.
Ceto a Nan Gaba
Nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah a hannun Yesu Kristi zai halaka wannan muguwar duniya kuma zai ba da ceto ga adalai da masu kamewa. (Karin Magana 2:21, 22; Daniyel 2:44) ‘Dukan maƙiyan Jehobah za su mutu, kuma abokansa za su haskaka kamar fitowar rana!’ (Littafin Mahukunta 5:31) Bari mu ci gaba da kasancewa cikin masu ƙaunar Jehobah ta yin amfani da abin da muka koya daga cikin littafin Mahukunta.
Muhimmiyar gaskiya da aka yi ta maimaitawa a cikin labarin Mahukunta ita ce: Yi wa Jehobah biyayya na kawo lada mai yawa, rashin biyayya na kawo sakamako marar kyau. (Maimaitawar Shari’a 11:26-28) Yana da muhimmanci mu kasance masu “biyayya da zuciya ɗaya” har sai Allah ya aikata nufinsa!—Romawa 6:17; 1 Yahaya 2:17.
[Hasiya]
a Lawiyawa ba su sami gadō a cikin Ƙasar Alkawari ba, sai dai birane 48 da aka warwatsa cikin Isra’ila.
[Taswira a shafi na 28]
“Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su.”—Littafin Mahukunta 2:16.
MAHUKUNTA
1. Otniyel
2. Ehud
3. Shamgar
4. Barak
5. Gidiyon
6. Tola
7. Yayir
8. Yefta
9. Ibzan
10. Elon
11. Abdon
12. Samson
DAN
MANASSA
NAFTALI
ASHIRU
ZABALUNA
ISSAKA
MANASSA
GAD
IFRAIMU
DAN
BILIYAMINU
RA’UBAINU
YAHUZA
[Hoto a shafi na 29]
Wane darassi ne ka koya daga nacewar da Barak ya yi cewa sai Debora ta bi shi zuwa filin daga?