Ka Sani?
Shin Romawa za su yarda a binne Yesu da kyau duk da cewa su ne suka rataye shi a kan gungume?
MUTANE da yawa sun san labarin yadda aka rataye Yesu a kan gungume tare da ɓarayi guda biyu. (Mat. 27:35-38) Amma wasu mutane sun ce abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa an shirya gawar Yesu kuma aka binne shi a cikin kabari ba gaskiya ba ne.—Mar. 15:42-46.
Waɗanda suke neman ƙaryata littattafan Linjila sun ce ba zai yiwu waɗanda suka kashe Yesu su yarda a binne shi da kyau a cikin kabari ba. A maimakon haka, sun ce akwai yadda ake bi da waɗanda aka kashe su a kan gungume. Wani ɗan jarida mai suna Ariel Sabar, ya rubuta a cikin jaridar Smithsonian dalilin da ya suka gaskata da hakan. Ya ce: “Waɗanda aka gicciye su mutane ne da suka yi laifi mafi muni. Don haka, wasu masana sun ce wauta ce mu yi tunani cewa Romawa za su yarda a binne irin mutanen nan da kyau.” Romawa sukan so su wulaƙanta waɗanda aka rataye, shi ya sa sukan bar gawawwakinsu a kan gungume don dabbobi su cinye. Daga baya sai su zubar da ƙasusuwan a cikin rami tare da wasu gawawwaki.
Amma masu tona kayan tarihi sun gano ƙasusuwan wasu Yahudawa da aka kashe da suka nuna cewa a wasu lokuta, ba haka yake ba. A 1968, an tono ƙasusuwan wani mutum da aka kashe a ƙarni na farko, daga kabarin wani iyalin Yahudawa kusa da Urushalima, a cikin wani akwati. A cikin ƙasusuwan, akwai ƙashin dudduge. An buga ƙashin a kan katako da kusa mai tsawon inci 4.5. Sabar ya ƙara da cewa “ƙashin duddugen, wanda na wani mutum ne mai suna Yehochanan ya ba da tabbaci cewa abubuwa da littattafan Linjila suka faɗa game da yadda aka binne Yesu gaskiya ne.” Saboda haka, “ƙashin dudduge na Yehochanan misali ne mai kyau na yadda Romawa suka amince a binne wani mutum da suka gicciye a zamanin Yesu.”
Har ila, akwai ra’ayoyi dabam-dabam game da yadda aka rataye Yesu bisa ga ƙashin dudduge na Yehochanan da aka samu. Amma abin da muka tabbatar yanzu shi ne, wasu masu laifi da aka rataye su, an amince a binne su da kyau, ba kawai an zubar da su a cikin rami ba. Don haka, abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa an binne Yesu da kyau gaskiya ne. Ƙashin da aka samu ya nuna cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne.
Abu mafi muhimmanci shi ne, Jehobah ya annabta cewa za a binne Yesu a kabarin wani mai arziki kuma babu wanda ya isa ya hana annabcin Jehobah cika.—Isha. 53:9; 55:11.