DARASI NA 5
Ka Yi Karatu Sumul
1 Timoti 4:13
ABIN DA ZA KA YI: Ka karanta abin da aka rubuta a cikin shafin da babbar murya.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
Ka shirya da kyau. Ka yi tunani a kan dalilin da ya sa aka rubuta labarin. Ka koyi yadda za ka karanta kalmomi da yawa tare, ba kalma bayan kalma ba. Kada ka ƙara ko ka tsallake ko kuma ka cire wasu kalmomi. Ka riƙa lura da ƙa’idojin rubutu kamar waƙafi, aya, da alamar tambaya.
Ka furta kalmomin daidai. Idan ba ka san yadda ake furta wata kalma ba, ka saurari sautin littafin don ka ji yadda ake furta kalmar ko kuma ka nemi taimakon wanda ya iya karatu.
Maganarka ta fita sosai. Ka yi karatu da kyau, ka ɗaga kanka kuma ka buɗe bakinka sosai. Ka yi ƙoƙari ka furta kowace kalma daidai.