DARASI NA 53
Ka Zaɓi Nishaɗin da Zai Faranta Ran Jehobah
Jehobah Allah ne mai farin ciki. (1 Timoti 1:11) Yana so mu yi farin ciki kuma mu ji daɗin rayuwa. Yana kuma so mu riƙa hutawa daga aikin da muke yi. A wannan darasin, za mu ga yadda za mu yi amfani da lokacin da muke hutawa a hanyoyi da za mu ji daɗi kuma mu faranta ran Jehobah.
1. Me ya kamata mu yi tunani a kai sa’ad da muke zaɓan nishaɗi?
Me kake jin daɗin yi sa’ad da kake shaƙatawa? Wasu mutane sun fi so su huta a gida suna karatu ko suna shan kiɗi ko kallon fim ko kuma su shiga Intane. Wasu kuma suna jin daɗin kasancewa da abokansu, suna hawan duwatsu ko su yi iyo ko su yi wasanni iri-iri. Ko da wane irin nishaɗi ne muka fi so, ya kamata mu tabbata cewa “abin da zai gamshi Ubangiji” ne. (Afisawa 5:10) Yana da muhimmanci mu san hakan domin ana nuna zalunci ko lalata ko kuma sihiri a nishaɗi da yawa da ake da su a yau kuma hakan ba su jitu da ra’ayin Jehobah ba. (Karanta Zabura 11:5.) Mene ne zai taimaka mana mu zaɓi nishaɗin da ya dace?
Idan abokanmu masu ƙaunar Jehobah ne, za su iya taimaka mana mu zaɓi nishaɗin da ya dace. Kamar yadda muka koya a darasi na 48, “wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima.” Amma idan muna abota da mutanen da ba sa bin ƙa’idodin Allah, za mu sha wahala kuma mu “lalace.”—Karin Magana 13:20.
2. Me ya sa yake da muhimmanci mu rage yawan lokaci da muke nishaɗi?
Ko da nishaɗin da muke yi ba zai shafi dangantakarmu da Jehobah ba, bai kamata mu ɓata lokaci da yawa muna yin su ba. Idan muna yin haka, ba za mu sami isashen lokaci na yin ayyuka masu muhimmanci ba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mu ‘yi amfani da lokacinmu da kyau.’—Karanta Afisawa 5:15, 16.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu koyi yadda za mu tsai da shawarwari masu kyau game da nishaɗi.
3. Ka guji nishaɗi marar kyau
Me ya sa za mu mai da hankali sa’ad da muke zaɓan nishaɗi? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.
Ta yaya wasannin da ake yi a ƙasar Roma ta dā suka yi kama da nishaɗin da ake yi a yau?
A bidiyon, mene ne Danny ya koya game da nishaɗi?
Ku karanta Romawa 12:9, sai ku tattauna tambayar nan:
Ta yaya wannan ayar za ta taimaka maka ka zaɓi nishaɗi mai kyau?
Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya tsana? Ku karanta Karin Magana 6:16, 17 da Galatiyawa 5:19-21. Bayan kun karanta kowane nassi, sai ku tattauna tambayar nan:
Wanne cikin abubuwan da aka ambata a ayoyin nan ne ake yawan gani a nishaɗin da ake yi a yau?
Tambayoyin da za su taimaka maka ka zaɓi nishaɗi mai kyau
Ka tambayi kanka:
Nishaɗin ya ƙunshi wani abin da Jehobah ya tsana?
Zai hana ni yin abubuwa masu muhimmanci ne?
Zai sa in riƙa cuɗanya a kai a kai da mutanen da ba sa ƙaunar Jehobah?
Zai fi kyau mu yi nisa daga wani abin da ke da haɗari. Shi ya sa zai dace mu guji duk wani nishaɗin da muke ganin zai ɓata halinmu
4. Ka yi amfani da lokacinka da kyau
Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.
Ko da yake ɗan’uwan da ke bidiyon ba ya kallon wani abu marar kyau, mece ce matsalarsa?
Ku karanta Filibiyawa 1:10, sai ku tattauna tambayar nan:
Ta yaya wannan ayar za ta taimaka mana mu san yawan lokacin da za mu yi muna yin nishaɗi?
5. Ka zaɓi nishaɗi mai kyau
Ko da yake wasu nishaɗi suna ɓata wa Jehobah rai, akwai waɗanda ba sa ɓata wa Jehobah rai da za mu iya jin daɗinsu. Ku karanta Mai-Wa’azi 8:15 da Filibiyawa 4:8, sai ku tattauna tambayar nan:
Wane nishaɗi ne kake jin daɗinsa?
WASU SUN CE: “Nishaɗin da ya ƙunshi zalunci ko lalata ko sihiri ba laifi ba ne muddin ba na aikata su.”
Me za ka ce?
TAƘAITAWA
Jehobah yana so mu zaɓi nishaɗi mai kyau kuma mu ji daɗin sa.
Bita
Wane irin nishaɗi ne bai kamata Kiristoci su yi ba?
Me ya sa za mu mai da hankali game da yawan lokacin da muke amfani da shi wajen yin nishaɗi?
Me ya sa za ka zaɓi nishaɗin da ke faranta ran Jehobah?
KA BINCIKA
Ku karanta talifin nan don ku ga wanda yake da hakkin zaɓar mana nishaɗin da za mu yi.
Ku karanta talifin nan don ku ga ko waye ne yake da hakkin zaɓar mana nishaɗin da za mu yi.
“Nishaɗin Da Kake Yi Yana Amfane Ka Kuwa?” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Oktoba, 2011)
Ku karanta talifin nan “Na Daina Nuna Ƙiyayya,” don ku ga abin da ya sa wani mutum ya daina nishaɗin da yake yi.
“Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuli, 2010)
Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wata mahaifiya ta tsai da shawara mai kyau game da fina-finan sihiri da take kallo.