TARIHI
Jehobah Ya ‘Daidaita Hanyoyina’
WANI ɗan’uwa matashi ya taɓa tambaya ta, “Wane nassi ne ka fi so?” Ba tare da ɓata lokaci ba sai na ce, “Karin Magana sura 3 aya 5 da 6, da suka ce: ‘Ka dogara ga Yahweh da dukan zuciyarka, kada ka dogara ga ganewarka. A dukan hanyoyin rayuwarka ka girmama shi, shi kuwa zai daidaita hanyoyinka.’” Hakika, Jehobah ya daidaita hanyoyina. Ta yaya?
IYAYENA SUN TAIMAKA MINI IN DAIDAITA HANYOYINA
Bayan shekara ta 1920, iyayena sun koya game da Jehobah kafin su yi aure. An haife ni a shekara ta 1939. Sa’ad da nake ƙarami muna zama a Ingila, ina zuwa taro tare da iyayena kuma na saka sunana a Makarantar Hidima ta Allah. Har yanzu, ina tuna yadda na ji a ranar da na hau kan wani akwati don tsayina ya yi daidai da inda mai jawabi ke ɗora littafinsa a dakalin yin magana don in ba da jawabina na farko. Ni ɗan shekara shida ne a lokacin kuma na ji tsoro sosai sa’ad da nake kallon manyan mutane da ke saurarar jawabina.
Mahaifina ya rubuta mini abin da zan riƙa faɗa a wa’azi a wani kati. Ni ɗan shekara takwas ne a lokaci na farko da na yi ma wani mutum wa’azi ni kaɗai. Na yi murna sosai sa’ad da mai gidan ya karanta katina kuma ya karɓi littafin nan “Let God Be True”! Sai na gudu na faɗa wa mahaifina. Yin wa’azi da halartan taro sun sa ni farin ciki kuma sun taimaka mini in so yi wa Jehobah hidima ta cikakken lokaci.
Na soma son Littafi Mai Tsarki sa’ad da mahaifina ya ce a riƙa tura masa Hasumiyar Tsaro kowane wata. Ina karanta kowane talifi da aka turo. Na dogara ga Jehobah kuma na yi alkawarin bauta masa.
Ni da iyayena mun halarci taron Theocracy’s Increase Assembly da aka yi a New York a shekara ta 1950. Jigon taron ranar Alhamis 3 ga Agusta, shi ne “Missionary Day” (Ranar Masu Wa’azi a Ƙasar Waje.) A ranar, Ɗan’uwa Carey Barber wanda daga baya ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne ya yi jawabin baftisma. A ƙarshen jawabinsa, ya yi wa waɗanda za su yi baftisma tambayoyi biyu, sai na tashi na amsa na ce, “E!” Ni ɗan shekara 11 ne a lokacin, amma na san cewa na yanke shawara mai muhimmanci. Na ji tsoron shiga ruwan domin ban iya iyo ba. Kawuna ya raka ni cikin ruwan da aka yi mini baftisma kuma ya tabbatar mini cewa babu abin da zai faru. An kammala baftismar da wuri, ƙafafuna ma ba su taɓa ƙasar tafkin ba. ’Yan’uwa biyu ne suka taimaka mini, ɗaya ya yi mini baftisma ɗaya kuma ya fitar da ni daga ruwan. Tun daga wannan rana mai muhimmanci, Jehobah ya ci gaba da daidaita hanyoyina.
NA ZAƁI IN DOGARA GA JEHOBAH
Sa’ad da na kammala makaranta, ina so in soma hidimar majagaba, amma malamanmu sun ba ni shawarar shiga makarantar jami’a. Na bi shawararsu kuma na shiga jami’a. Amma sai na lura cewa ba zai yiwu in bauta wa Jehobah da ƙwazo kuma in mai da hankali ga karatu a makaranta ba, sai na bar makarantar. Na yi addu’a ga Jehobah, kuma na rubuta wasiƙa cewa zan bar makarantar. Na bar makarantar a ƙarshen shekarata ta farko. Nan da nan sai na soma hidimar majagaba.
A watan Yuli na shekara ta 1957, na soma hidima ta cikakken lokaci a garin Wellingborough. Na gaya wa ’yan’uwan da ke Bethel a Landan su gaya mini ɗan’uwan da ya manyanta da za mu yi hidimar tare. Sai aka haɗa ni da Ɗan’uwa Bert Vaisey kuma ya koya mini abubuwa da yawa. Yana da ƙwazo sosai, ya koya mini yadda zan tsara wa’azina. A ikilisiyarmu, akwai ’yan’uwa mata tsofaffi guda shida da Ɗan’uwa Vaisey da kuma ni. Shirya taro da yin ayyuka a taron sun taimaka mini in dogara ga Jehobah.
Bayan an saka ni a kurkuku na ɗan lokaci don na ƙi yin aikin soja, sai na haɗu da wata ’yar’uwa mai suna Barbara da take hidimar majagaba na musamman. Mun yi aure a shekara ta 1959, kuma muna shirye mu yi hidima a duk inda aka tura mu. Da farko, mun yi hidima a yankin Lancashire da ke arewa maso yammacin Ingila. A watan Janairu 1961, an gayyace ni Makarantar Hidima ta Mulki na wata ɗaya a Bethel da ke Landan. Na yi mamaki domin bayan mun kammala makarantar, an tura ni yin hidimar mai kula mai ziyara. Na yi sati biyu ina koyan yadda zan yi hidimar daga wani mai kula da da’ira a birnin Birmingham, kuma an amince Barbara ta bi ni. Sai muka koma yankunan da muke hidima wato yankunan Lancashire da Cheshire.
DOGARA GA JEHOBAH ABU NE MAFI KYAU
Sa’ad da muka je hutu a watan Agusta 1962, an tura mana wasiƙa daga ofishinmu. An tura mana fom ɗin Makarantar Gilead! Bayan da ni da matata muka yi addu’a, sai muka cika fom ɗin kuma muka tura shi ofishinmu ba tare da ɓata lokaci ba. Wata biyar bayan haka, mun je Brooklyn da ke New York don mu halarci aji na 38 na Makarantar Gilead kuma mun yi wata goma a wurin.
An koya mana abubuwa da yawa game da Kalmar Allah da ƙungiyarmu da kuma ’yan’uwanmu a faɗin duniya. Duk da cewa mu matasa ne, mun koyi abubuwa da yawa daga ’yan ajinmu. Na ji daɗin yin aiki kowace rana tare da Ɗan’uwa Fred Rusk ɗaya cikin malamanmu. Ɗaya daga cikin darussa da ya nanata shi ne cewa a kowane lokaci mu riƙa ba da shawara daga Littafi Mai Tsarki. Wasu daga cikin ’yan’uwan da suka koyar da mu su ne Nathan Knorr da Frederick Franz da kuma Karl Klein. Mun koyi darasi sosai daga misalin Ɗan’uwa A. H. Macmillan. Ya koya mana game da yadda Jehobah ya taimaka wa bayinsa a shekara ta 1914 zuwa 1919 sa’ad da aka jarraba bangaskiyarsu!
AN CANJA MANA HIDIMA
Sa’ad da muka kusa sauke karatu, Ɗan’uwa Knorr ya gaya wa ni da matata cewa za a tura mu yin hidima a ƙasar Burundi da ke Afirka. Nan da nan, sai muka je laburarin da ke Bethel muka duba Yearbook don mu san ko masu shela nawa ne a ƙasar. Amma mun yi mamaki cewa babu Shaidu a ƙasar! E, za mu je wurin da babu wanda ya taɓa yin wa’azi kuma za mu je Afirka. Mun ji tsoro sosai! Amma bayan mu yi addu’a, hankalinmu ya kwanta.
A sabon wurin da aka tura mu hidima, yanayin da al’ada da kuma yare sun bambanta da wanda muka saba. Yanzu za mu koyi Faransanci. Ƙari ga haka, mun bukaci masauki. Kwana biyu bayan mun isa, wani ɗan ajinmu mai suna Harry Arnott ya ziyarce mu sa’ad da yake kan hanyar zuwa wurin da aka tura shi hidima a Zambiya. Ya taimaka mana mu sami gida, kuma wannan ne ya zama masauki na farko na masu wa’azi a ƙasar waje a wurin. Ba daɗewa ba, sai hukuma ta soma tsananta mana domin ba ta san kome game da ayyukan Shaidun Jehobah ba. Yayin da muka soma jin daɗin hidimarmu, hukuma ta gaya mana cewa ba za mu iya zama a ƙasar ba tare da izinin yin aiki ba. Abin baƙin ciki, mun bar ƙasar kuma muka koma ƙasar Yuganda.
Mun ji tsoron zuwa Yuganda domin ba mu da bisa, amma mun dogara ga Jehobah. Wani ɗan’uwa ɗan Kanada da ke hidima a ƙasar ya bayyana wa hukuma yanayin da muke ciki, kuma suka amince mu zauna a ƙasar na wasu watanni har sai mun sami izinin ci gaba da zama. Hakan ya nuna cewa Jehobah yana taimaka mana.
Yanayinmu a wannan ƙasar ta bambanta da Burundi. Akwai Shaidu 28 a ƙasar gabaki ɗaya. A ƙasar, mun haɗu da mutane da yawa da suke yin Turanci. Mun fahimci cewa idan muna so mu taimaka wa mutanen su koyi gaskiya, muna bukatar mu koyi ko da yare ɗaya ne da ake yi a ƙasar. Mun soma wa’azi a birnin Kampala inda ake yaren Luganda, hakan ya sa mun koyi yaren. Mun yi shekaru da yawa kafin mu iya yaren, amma hakan ya taimaka mana a hidimarmu sosai! Mun soma fahimtar abubuwan da ɗalibanmu suke bukatar su koya. Sa’ad da ɗalibanmu suka ga cewa mun damu da su, hakan ya sa su faɗa mana ra’ayinsu game da abin da suke koya.
TAFIYE-TAFIYEN DA MUKA YI
Mun yi farin cikin taimaka wa mutane su koyi gaskiya. Amma mun fi farin ciki sa’ad da aka ce mu yi hidimar masu kula masu ziyara a ƙasar. Ofishinmu da ke Kenya ta gaya mana mu binciko wuraren da ake bukatar majagaba na musamman a ƙasar. Sau da yawa, mutanen da ba su taɓa sanin Shaidu ba sun nuna mana alheri. Sun marabce mu kuma suka dafa mana abinci.
Bayan haka, mun sake yin wani tafiya dabam. Na yi tafiyar kwana biyu ta jirgin ƙasa daga birnin Kampala zuwa Mombasa a Kenya, sai na shiga jirgin ruwa zuwa tsibirin Seychelles da ke Tekun Indiya. Bayan haka, daga shekara ta 1965 zuwa 1972 matata ta soma bi na ziyara tsibirin Seychelles. Da farko, masu shela biyu ne suke wurin, amma daga baya sun zama rukuni kuma suka zama ikilisiya. Bayan haka, na je ƙasar Eritrea da Habasha da Sudan don in ziyarci ’yan’uwa.
Yanayin ƙasar Yuganda ya canja sa’ad da sojoji suka yi juyin mulki. Abubuwan da suka faru bayan haka sun nuna mini muhimmancin yin biyayya ga umurnin da ke Littafi Mai Tsarki cewa: “Ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar.” (Mar. 12:17) Akwai lokacin da aka ce duk bakin da ke ƙasar su je su yi rajista a ofishin ’yan sanda da ke kusa da su. Mun bi wannan umurnin. Bayan wasu kwanaki, sa’ad da muke tuki a birnin Kampala, ’yan sandan ciki sun tsayar da ni da wani ɗan’uwa da muke wa’azi tare. Hankalinmu ya tashi! Sun ce mu ’yan leƙen asiri ne kuma suka kai mu hedkwatar ’yan sanda, a wurin mun bayyana musu cewa mu masu wa’azi ne. Mun gaya musu cewa mun riga mun yi rajista, amma ba su saurare mu ba. Sun kai mu ofishin ’yan sanda da ke kusa da gidanmu. Mun yi farin ciki sa’ad da ɗan sandan da ya yi mana rajista ya tuna mu kuma ya gaya musu cewa su sake mu!
A lokacin, muna yawan fuskantar matsaloli sa’ad da sojoji da suka bugu suka rufe hanya. A kowane lokaci, yin addu’a yana kwantar mana da hankali kafin sojojin su ba mu izinin wucewa. Abin baƙin ciki, a shekara ta 1973, an umurci dukan masu wa’azi a ƙasar waje su bar ƙasar Yuganda.
An tura mu ƙasar Kwaddebuwa da ke yammancin Afirka. Hakan yana nufin cewa za mu yi wasu canje-canje, za mu koyi sabuwar al’ada, mu riƙa Faransanci a kowane lokaci, kuma mu saba da masu wa’azi a ƙasar waje da ke wurin! Mun ga cewa Jehobah yana yi mana ja-goranci domin yadda mutane suke saurarar wa’azinmu nan da nan. Mun ga cewa dogara ga Jehobah ya sa mu daidaita hanyoyinmu.
Farat ɗaya sai aka gano cewa matata Barbara tana da ciwon kansa. Duk da cewa mun je ƙasashe da yawa don yin jinya, a shekara ta 1983, mun ga cewa ba za mu iya yin hidima a Afirka kuma ba. Hakan ya sa mu baƙin ciki!
YANAYINMU YA CANJA
Ciwon matata ya yi tsanani sa’ad da muke hidima a Bethel da ke Landan, kuma daga baya, sai ta rasu. ’Yan’uwa a Bethel sun taimaka mini sosai. Akwai wasu ma’aurata musamman da suka taimaka mini in ci gaba da yin canji da kuma dogara ga Jehobah. Daga baya, na haɗu da wata ’yar’uwa mai suna Ann da take zuwa yin hidima a Bethel daga gidanta, ta taɓa yin hidimar majagaba na musamman kuma tana ƙaunar Jehobah sosai. Mun yi aure a shekara ta 1989, kuma tun lokacin muna hidima a Bethel da ke Landan.
Daga shekara ta 1995 zuwa 2018, na sami damar yin hidimar dattijo mai ziyartar reshen ofisoshinmu kuma na ziyarci ƙasashe wajen 60. A kowane lokaci da muka je ziyara, na lura cewa Jehobah yana taimaka wa mutane a duk yanayin da suke.
A shekara ta 2017, mun koma Afirka ziyara. Na yi farin cikin kai Ann Burundi kuma mun yi mamakin ganin yawan mutanen da suka soma bauta wa Jehobah! Yanzu an gina Bethel mai kyau a titin da na yi wa’azi gida-gida a shekara ta 1964. Yanzu akwai masu shela fiye da 15,500 a ƙasar.
Na yi farin ciki sosai sa’ad da aka gaya mini ƙasashen da zan ziyarta a shekara ta 2018. Kwaddebuwa yana cikin ƙasashen. Na ji kamar na dawo gida sa’ad da muka isa birnin Abidjan. Sa’ad da na duba takardar da ake rubuta lambar mutanen da ke Bethel, na lura cewa ɗakin ɗan’uwa Sossou ne ke kusa da ɗakinmu. Na tuna cewa ya taɓa yin hidimar dattijo mai kula da birni a lokacin da nake Abidjan. Amma ba shi ba ne, ɗansa ne.
Jehobah ya cika alkawuransa. Abubuwa da yawa da suka faru a rayuwata sun tabbatar mini da cewa idan muka dogara ga Jehobah zai taimaka mana. A yanzu, muna so mu ci gaba da bin hanyar da za ta ƙara haskakawa a nan gaba sa’ad da duniya ta zama aljanna.—K. Mag. 4:18.