TALIFIN NAZARI NA 49
Za Mu Iya Yin Rayuwa Har Abada
“Rai na har abada ke nan.”—YOH. 17:3, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
WAƘA TA 147 Alkawarin Rai Na Har Abada
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Ta yaya yin tunani a kan alkawarin rai na har abada da Allah ya yi mana zai iya shafan mu?
JEHOBAH ya yi alkawari cewa duk waɗanda suka yi masa biyayya za su sami “rai na har abada.” (Rom. 6:23) Idan muka yi tunani sosai a kan alkawarin da Allah ya yi mana, za mu daɗa ƙaunar sa. Ka tuna cewa Ubanmu na sama yana ƙaunar mu sosai. Shi ya sa ba za mu iya rabuwa da shi ba.
2. Ta yaya alkawarin da Allah ya yi mana game da rai na har abada yake taimaka mana?
2 Alkawarin da Allah ya yi mana game da rai na har abada yana taimaka mana mu iya jimre matsaloli. Ko da maƙiyanmu sun yi barazanar kashe mu, ba za mu daina bauta ma Jehobah ba. Me ya sa? Ɗaya daga cikin dalilan shi ne mun san cewa idan mun mutu da aminci ga Jehobah, zai tā da mu daga mutuwa kuma ya ba mu damar yin rayuwa har abada. (Yoh. 5:28, 29; 1 Kor. 15:55-58; Ibran. 2:15) Me ya sa za mu iya kasancewa da tabbaci cewa za mu iya yin rayuwa har abada? Ka yi la’akari da dalilai na gaba.
JEHOBAH YANA RAYUWA HAR ABADA
3. Mene ne ya tabbatar mana cewa Jehobah zai iya sa mu yi rayuwa har abada? (Zabura 102:12, 24, 27)
3 Mun san cewa Jehobah zai iya ya ba mu rai na har abada domin shi ne tushen rai kuma yana rayuwa har abada. (Zab. 36:9) Ka lura da wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka tabbatar mana cewa Jehobah ba shi da farko kuma ba shi da ƙarshe. Zabura 90:2 ta ce Jehobah Allah ne “marar farko marar ƙarshe.” Zabura 102 ma ta faɗi abu makamancin hakan. (Karanta Zabura 102:12, 24, 27.) Saꞌan nan annabi Habakkuk ya rubuta game da Ubanmu na sama ya ce: “Ya Yahweh, daga har abada ne kai! Yahweh Allahna, Mai Tsarkina, ba ka mutuwa!”—Hab. 1:12.
4. Ya kamata mu damu cewa ba mu fahimci yadda Allah marar farko kuma marar ƙarshe ba ne? Ka bayyana.
4 Yana yi maka wuya ka gane cewa Yahweh shi ne “Allah Madawwami”? (Isha. 40:28) Yana yi wa mutane da yawa wuya su fahimci hakan. Elihu ya faɗa game da Allah cewa: “Yawan shekarunsa ya fi gaban bincike.” (Ayu. 36:26) Amma domin ba mu fahimci wani batu ba hakan ba ya nufin cewa batun ba gaskiya ba ne. Alal misali, idan ba mu fahimci yadda ake yi a sami haske ba, hakan yana nufin cewa babu haske ne? Aꞌa! Hakazalika, zai yi wa ’yan Adam wuya su fahimci yadda Jehobah ba shi da farko ko kuma ƙarshe ba. Amma hakan ba ya nufin cewa Jehobah ba ya rayuwa har abada ba. Gaskiya game da Mahalicci bai dangana ga abin da za mu iya ganewa ko wanda ba za mu iya ganewa ba. (Rom. 11:33-36) Kuma yana rayuwa tun kafin sama da ƙasa su kasance, har da rana da kuma taurari. Jehobah ya tabbatar mana cewa shi ne “ya yi ƙasa ta wurin ikonsa.” Kuma ya “shimfiɗa sammai ta wurin ganewarsa.” (Irm. 51:15; A. M. 17:24) Wane dalili ne kuma ya sa mun tabbata cewa za mu iya yin rayuwa har abada?
JEHOBAH YA HALICCE MU DON MU YI RAYUWA HAR ABADA
5. Da farko, wane bege ne aka ba Adamu da Hauwa’u?
5 Jehobah ya halicci ꞌyan Adam su yi rayuwa har abada, amma ba haka yake da sauran halittun da ke duniya ba. A duniya, ꞌyan Adam ne kaɗai ya ba su zarafin yin rayuwa har abada. Amma Jehobah ya gargaɗi Adamu cewa: “Daga Itace Mai Kawo Sanin Nagarta da Mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci daga itacen nan lallai za ka mutu.” (Far. 2:17) Da a ce Adamu da Hauwa’u sun yi biyayya ga Jehobah, da ba su mutu ba. Da alama, da Jehobah ya ba su izinin cin “itace mai ba da rai” bayan wasu lokuta. Hakan zai nuna cewa ya amince su yi rayuwa “har abada.”b—Far. 3:22.
6-7. (a) Mene ne kuma ya nuna cewa ba a halicci ꞌyan Adam su mutu ba? (b) Wane buri ne kake so ka cim ma? (Ka duba hotunan da suka shafi sakin layi na 7.)
6 Abin ban shaꞌawa ne cewa wasu ꞌyan kimiyya sun gano cewa ƙwaƙwalwarmu za ta iya tara bayanai fiye da abubuwan da za mu iya koya a duk tsawon rayuwarmu yanzu. Hakan na da ban shaꞌawa. A shekara ta 2010, wata mujalla ta bayyana cewa ƙwaƙwalwarmu za ta iya adana bayanai da idan aka kwatanta yawansa, zai kai kamar tsawon bidiyo mai saꞌoꞌi fiye da miliyan uku. Mutum zai yi fiye da shekaru 300 yana kallon bidiyon. Da alama ƙwaƙwalwarmu za ta iya adana bayanai fiye da hakan ma. Amma hakan ya nuna mana cewa Jehobah ya shirya ƙwaƙwalwarmu yadda za ta iya adana bayanai fiye da waɗanda za mu iya adanawa a cikin shekaru 70 ko 80.—Zab. 90:10.
7 Jehobah ya kuma halicce mu da niyyar yin rayuwa har abada. Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da ꞌyan Adam, ya ce: ‘Ya sa burin yin rayuwa har abada a zuciyarsu.’ (M. Wa. 3:11, New World Translation) Wannan ɗaya ne daga cikin dalilan da suka sa muke ɗaukan mutuwa a matsayin maƙiyi. (1 Kor. 15:26) Idan muka kamu da rashin lafiya, za mu ƙi yin jinya kuma mu zauna har mu mutu ne? Aꞌa. Mukan je asibiti kuma mai yiwuwa mu sha magani don mu iya samun sauƙi. Mukan yi iya ƙoƙarinmu don kada mu mutu. Kuma saꞌad da wani da muke ƙauna ya mutu, ko da mutumin ya tsufa ko matashi ne, mukan yi baƙin ciki sosai. (Yoh. 11:32, 33) Za mu iya ci gaba da koyan abubuwa babu iyaka, kuma muna da sha’awar yin rayuwa har abada domin yadda Mahaliccinmu mai ƙauna ya yi mu ke nan. Babu shakka zai buɗe mana hanyar yin rayuwa har abada. Amma akwai wasu ƙarin dalilai da suka nuna cewa za mu iya yin rayuwa har abada. Don haka, bari mu bincika wasu abubuwa da Jehobah ya yi a dā kuma yake yi a yanzu da suka nuna cewa bai canja nufinsa wa ꞌyan Adam ba.
JEHOBAH BAI CANJA NUFINSA WA ꞌYAN ADAM BA
8. Wane tabbaci ne Ishaya 55:11 ta ba mu game da nufin Allah wa ꞌyan Adam?
8 Ko da yake Adamu da Hauwaꞌu sun yi zunubi kuma sun jawo wa ꞌyaꞌyansu mutuwa, Jehobah bai canja nufinsa wa ꞌyan Adam ba. (Karanta Ishaya 55:11.) Har yanzu, nufinsa shi ne ꞌyan Adam masu aminci su yi rayuwa har abada. Mun san hakan ta wajen abubuwan da Jehobah ya faɗa kuma ya yi don ya cika nufinsa.
9. Wane alkawari ne Allah ya yi mana? (Daniyel 12:2, 13)
9 Jehobah ya yi alkawari cewa zai tā da matattu kuma ya ba su damar yin rayuwa har abada. (A. M. 24:15; Tit. 1:1, 2) Bawan Allahn nan mai aminci wato Ayuba, ya kasance da tabbaci cewa Jehobah yana marmarin tā da waɗanda suka mutu. (Ayu. 14:14, 15) Annabi Daniyel ya san cewa za a tā da matattu kuma a ba su damar yin rayuwa har abada. (Zab. 37:29; karanta Daniyel 12:2, 13.) Yahudawa a zamanin Yesu ma sun san cewa Jehobah zai iya ba ma bayinsa masu aminci “rai na har abada.” (Luk. 10:25; 18:18) Sau da dama Yesu ya yi magana game da wannan alkawarin, kuma shi ma, Allah ya tā da shi daga mutuwa.—Mat. 19:29; 22:31, 32; Luk. 18:30; Yoh. 11:25.
10. Wane tabbaci ne muke da shi don tashin matattu da aka yi a dā? (Ka duba hoton da ya shafi sakin layi na 10.)
10 Jehobah shi ne mai ba da rai kuma yana da ikon tā da matattu. Ya ba ma Iliya ikon tā da yaron wata gwauruwa a Zarefat. (1 Sar. 17:21-23) Daga baya, Allah ya taimaka ma Elisha ya tā da ɗan wata mata a garin Shunem. (2 Sar. 4:18-20, 34-37) Waɗannan tashin matattu da ma wasu sun tabbatar mana cewa Jehobah yana da ikon tā da matattu. Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna cewa Ubansa ya ba shi ikon tā da matattu. (Yoh. 11:23-25, 43, 44) A yanzu Yesu yana sama kuma an ba shi “dukan iko a sama da kuma nan duniya.” Don haka, zai iya cika alkawarin nan cewa zai tā da “duk waɗanda suke cikin kaburbura” kuma ya ba su damar yin rayuwa har abada.—Mat. 28:18; Yoh. 5:25-29.
11. Ta yaya fansar Yesu Kristi ta buɗe mana hanyar samun rai na har abada?
11 Me ya sa Jehobah ya ƙyale Ɗansa ya sha wahala kuma ya mutu? Yesu ya gaya mana dalilin, ya ce: “Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Da yake Allah ya ba da ɗansa ya mutu domin zunubanmu, Allah ya buɗe mana hanyar samun rai na har abada. (Mat. 20:28) Ga yadda manzo Bulus ya bayyana wannan batun: “Tun da yake mutuwa ta zo ne ta wurin mutum, haka ma tashin matattu ya zo ne ta wurin mutum. Gama kamar yadda duka ake mutuwa saboda Adam, haka za a tā da duka saboda Almasihu.”—1 Kor. 15:21, 22.
12. Ta yaya Jehobah zai cika nufinsa?
12 Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi adduꞌa Mulkin Allah ya zo kuma a yi nufinsa a duniya. (Mat. 6:9, 10) Ɗaya daga cikin nufin Allah shi ne ꞌyan Adam su yi rayuwa har abada a duniya. Jehobah ya naɗa Ɗansa a matsayin Sarkin Mulkin Allah don ya cim ma wannan nufin. Tun daga ƙarni na farko, Allah ya fara zaɓan mutane 144,000 daga duniya da za su yi aiki tare da Yesu don su cim ma nufin Allah.—R. Yar. 5:9, 10.
13. Mene ne Jehobah yake yi a yanzu, kuma mene ne ya kamata ka yi?
13 Jehobah yana tattara taro mai girma ko “babban taro” kuma yana koya musu yadda za su yi rayuwa a ƙarƙashin Mulkinsa. (R. Yar. 7:9, 10; Yak. 2:8) Ko da yake yawancin mutane a yau ba su da haɗin kai saboda ƙiyayya da yaƙe-yaƙe, waɗanda suke cikin taro mai girma sun yi ƙoƙari sun kawar da kowace irin ƙiyayya daga zuciyarsu. Suna nuna ta halayensu cewa sun mai da takubbansu garmar noma. (Mik. 4:3) Maimakon su saka hannu a cikin yaƙe-yaƙen da ya zama sanadiyyar mutuwar mutane da dama, suna taimaka wa mutane su iya samun “ainihin rai” ta wurin koya musu game da Jehobah da kuma nufinsa. (1 Tim. 6:19) Membobin iyalinsu za su iya tsananta musu, kuma za su iya shiga matsalar rashin kuɗi domin suna goyon bayan Mulkin Allah, amma Jehobah yana tabbata cewa suna samun abubuwan biyan bukata. (Mat. 6:25, 30-33; Luk. 18:29, 30) Hakan ya tabbatar mana da cewa Mulkin Allah yana sarauta da gaske, kuma zai ci gaba da cika nufin Allah.
ALKAWARI MAI KYAU GAME DA NAN GABA
14-15. Ta yaya alkawarin da Allah ya yi na kawar da mutuwa har abada zai cika?
14 A yanzu, Yesu yana sarauta a Mulkin Allah a sama, kuma zai cika dukan alkawuran da Allah ya yi mana. (2 Kor. 1:20) Tun daga 1914, Yesu ya ci gaba da yin nasara a kan maƙiyansa. (Zab. 110:1, 2) Nan ba da daɗewa ba, Yesu da kuma abokan sarautarsa za su ci nasara a kan maƙiyansu gabaki ɗaya kuma su hallaka su.—R. Yar. 6:2.
15 A lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu, za a tā da matattu, kuma a sa waɗanda suka yi biyayya ga Jehobah su zama kamiltattu. Bayan gwaji na ƙarshe, waɗanda suke da adalci a idon Jehobah ‘za su gāji ƙasar, su zauna a ciki har abada.’ (Zab. 37:10, 11, 29) Kuma abin farin ciki shi ne “abokiyar gaba ta ƙarshe da za a kawar, ita ce mutuwa.”—1 Kor. 15:26.
16. Mene ne ya kamata ya zama ainihin dalilin da ya sa muke bauta ma Jehobah?
16 Kamar yadda muka gani, begenmu na yin rayuwa har abada ya jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Begen zai taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da aminci a wannan kwanakin ƙarshe. Amma idan muna so mu faranta ma Jehobah rai, ba begen yin rayuwa har abada a duniya ne kawai ya kamata ya sa mu kasance da aminci ba. Dalili mafi muhimmanci da ya sa ya kamata mu kasance da aminci ga Jehobah da kuma Yesu shi ne don yadda muke ƙaunar su. (2 Kor. 5:14, 15) Ƙaunar nan tana sa mu gaya ma wasu game da begen da muke da shi. (Rom. 10:13-15) Yayin da muke ƙoƙari mu zama marasa son kai, da masu bayarwa, za mu zama irin mutane da Jehobah yake so su zama abokansa har abada.—Ibran. 13:16.
17. Wane hakki ne kowannenmu yake da shi? (Matiyu 7:13, 14)
17 Za mu kasance cikin waɗanda za su sami rai na har abada? Jehobah ya riga ya buɗe mana hanyar samun rai na har abada. Yanzu ya rage namu ne mu kasance a wannan hanyar da za ta kai mu ga samun rai na har abada. (Karanta Matiyu 7:13, 14.) Yaya rayuwa za ta kasance a aljanna? Za mu tattauna amsar a talifi na gaba.
WAƘA TA 141 Rai, Kyauta Ce Daga Allah
a Kana sa ran yin rayuwa har abada? Jehobah ya yi mana alkawari cewa nan ba da jimawa ba za mu yi rayuwa ba tare da jin tsoron mutuwa ba. A wannan talifin, za mu ga abin da ya sa za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawarin nan da ya yi mana.
b Ka duba akwatin nan “Furucin nan “Har Abada” a Cikin Littafi Mai Tsarki.”
c BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa da ya tsufa yana tunani a kan abubuwan da zai mora a aljanna.