TALIFIN NAZARI NA 19
Ta Yaya Za Mu Daɗa Gaskata da Alkawarin Sabuwar Duniya?
“[Jehobah] ya taɓa yin alkawari, ya kāsa cikawa ne?”—L. ƘID. 23:19.
WAƘA TA 142 Mu Jimre, Aljanna Ta Kusa
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1-2. Yayin da muke jiran aljanna ta zo, mene ne muke bukatar mu yi?
BA MA wasa da alkawarin da Jehobah ya yi cewa zai mai da duniyar nan ta zama aljanna. (2 Bit. 3:13) Ko da yake ba mu san yaushe ne wannan alkawarin zai cika ba, abubuwan da suke faruwa a duniya suna nuna mana cewa lokacin ya kusa.—Mat. 24:32-34, 36; A. M. 1:7.
2 Kafin aljannar ta zo, muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah. Me ya sa? Domin ko da muna da bangaskiya sosai, za ta iya yin sanyi. Manzo Bulus ya ce da rashin bangaskiya, “zunubin da ya riƙe mu kam-kam.” Wato ba abu mai wuya ba ne mu rasa bangaskiya. (Ibran. 12:1) Don mu hana bangaskiyarmu yin sanyi, muna bukatar mu bincika abubuwan da suka tabbatar mana da cewa aljanna za ta zo da gaske kuma ta kusa.—Ibran. 11:1.
3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa guda uku da za su taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu game da sabuwar duniya: (1) yin tunani mai zurfi a kan fansar Yesu, (2) yin tunani a kan ikon Jehobah, (3) yin ayyukan ibada a-kai-a-kai. Bayan haka, za mu tattauna yadda abin da Jehobah ya gaya wa Habakkuk zai ƙarfafa bangaskiyarmu a yau. Amma da farko, bari mu tattauna wasu abubuwan da muke fuskanta yanzu da suka sa muke bukatar mu ƙara gaskata cewa aljanna za ta zo.
ABUBUWAN DA SUKA SA MUKE BUKATAR BANGASKIYA SOSAI
4. Waɗanne shawarwari ne muke yankewa da suke bukatar mu nuna bangaskiya sosai?
4 Kowace rana, muna yanke shawarwarin da suke bukatar mu nuna bangaskiya sosai. Alal misali, muna yanke shawarwari game da abokanmu, da nishaɗin da za mu yi, da makaranta, da aure, da renon yara, da aikinmu. Zai dace mu tambayi kanmu cewa: ‘Shin shawarwarina suna nuna ina da tabbaci cewa nan ba da daɗewa ba, Allah zai mai da duniya ta zama aljanna? Ko dai ina yin abubuwa yadda waɗanda ba su gaskata cewa za su yi rayuwa har abada ba suke yi?’ (Mat. 6:19, 20; Luk. 12:16-21) Idan muka ƙarfafa bangaskiyarmu cewa nan ba da daɗewa ba sabuwar duniya za ta zo, hakan zai taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau.
5-6. Me ya sa muke bukatar bangaskiya sosai saꞌad da muke fuskantar matsaloli? Ka ba da misali.
5 Ƙari ga haka, muna fuskantar matsalolin da suke bukatar mu nuna bangaskiya sosai. Mukan yi fama da tsanantawa da rashin lafiya mai tsanani ko kuma wasu abubuwan da za su sa mu yi sanyin gwiwa. Da farko, za mu ga kamar za mu iya jimre matsalar nan. Amma idan matsalar ta ƙi tafiya, sai da bangaskiya sosai ne za mu iya jimre ta kuma mu ci gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki.—Rom. 12:12; 1 Bit. 1:6, 7.
6 Idan muna fuskantar wata matsala, za mu ga kamar sabuwar duniya ba za ta zo ba. Shin hakan na nuna cewa ba mu da bangaskiya ne? Ba lallai ba. Ga wani misali. Idan muna lokacin sanyi sosai, za mu ga kamar ba za a taɓa yin zafi ba. Amma komin yaya, lokacin zafi zai zo. Hakazalika, idan muna fama da abin da ya sa mu sanyin gwiwa sosai, za mu ji kamar sabuwar duniya ba za ta taɓa zuwa ba. Amma idan muna da bangaskiya sosai, za mu kasance da tabbaci cewa Allah zai cika alkawarinsa. (Zab. 94:3, 14, 15; Ibran. 6:17-19) Idan muna da wannan tabbaci, za mu ci gaba da mai da bautar Jehobah abu mafi muhimmanci a rayuwarmu.
7. Wane hali ne muke bukatar mu guje wa?
7 Wata hanya kuma da muke bukatar mu nuna bangaskiya ita ce saꞌad da muke waꞌazi. Mutane da yawa da muke gaya musu “labari mai daɗi” game da sabuwar duniya ba su gaskata cewa hakan zai faru ba. (Mat. 24:14; Ezek. 33:32) Kada mu bar wannan shakkar da suke yi ta shafe mu. Me zai taimaka mana mu yi hakan? Muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. Bari mu ga yadda za mu yi hakan a hanyoyi uku.
MU YI TUNANI MAI ZURFI A KAN FANSAR YESU
8-9. Ta yaya yin tunani mai zurfi a kan fansar Yesu zai ƙarfafa bangaskiyarmu?
8 Hanya ɗaya da za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu ita ce ta yin bimbini, wato yin tunani mai zurfi a kan fansar Yesu. Fansar Yesu tana tabbatar mana cewa alkawuran Allah za su faru da gaske. Idan muka yi tunani sosai a kan dalilin da ya sa aka ba da fansar da kuma abin da hakan ya kunsa, za mu ƙara kasance da tabbaci cewa Allah zai sa mu rayu har abada a sabuwar duniya kamar yadda ya faɗa. Me ya sa muka ce hakan?
9 Mene ne fansar Yesu ta ƙunsa? Yesu shi ne farkon halitta na Jehobah kuma shi ne ya fi kusa da Allah. Duk da haka, Jehobah ya turo shi duniya a matsayin kamiltaccen mutum. Da Yesu yake duniya, ya sha wahala sosai kuma ya jimre. Bayan haka, ya yi mutuwar wulaƙanci. Wannan ba ƙaramin abu ba ne Jehobah ya yi. Jehobah ba zai taɓa barin Ɗansa ya sha wahala kuma ya mutu don kawai mu ji daɗin rayuwa na ƙanƙanin lokaci ba. (Yoh. 3:16; 1 Bit. 1:18, 19) Da yake Jehobah ya ba da fansa mafi daraja, zai tabbata cewa mun ji daɗin rayuwa har abada a sabuwar duniya.
MU YI TUNANI GAME DA IKON JEHOBAH
10. Bisa ga abin da ke Afisawa 3:20, mene ne Jehobah zai iya yi?
10 Hanya ta biyu da za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu ita ce ta yin tunani a kan ikon Jehobah. Jehobah yana da ikon yin duk abubuwan da ya yi alkawarin su. Zai yi wa ꞌyan Adam wuya su gaskata da alkawarin yin rayuwa har abada a duniya. Amma Jehobah ya saba yin alkawarin abubuwan da ꞌyan Adam ba za su taɓa iya yi ba. Zai iya yin hakan domin shi ne Allah mai iko duka. (Ayu. 42:2; Mar. 10:27) Don haka, bai kamata mu yi mamaki idan ya yi alkawarin yin abubuwan ban alꞌajibi ba.—Karanta Afisawa 3:20.
11. Ka ambata wani alkawari mai ban alꞌajibi da Allah ya yi. (Ka kuma duba akwatin nan “Wasu Alkawura Masu Ban Alꞌajabi da Suka Cika.”)
11 Ka yi laꞌakari da wasu alkawuran da Jehobah ya yi wa mutanensa a dā. Ya yi musu alkawuran da mutane suke ganin ba za su taɓa yiwuwa ba. Ya gaya wa Ibrahim da Saratu cewa za su haifi ɗa duk da cewa sun tsufa a lokacin. (Farawa 17:15-17) Ya kuma gaya wa Ibrahim cewa zuriyarsa za ta gāji ƙasar Kanꞌana. ꞌYaꞌyan Ibrahim sun yi shekaru suna bauta a ƙasar Masar. A wannan lokacin, ƙila sun ga kamar alkawarinsa ba zai taɓa cikawa ba. Amma alkawarin ya cika da gaske. Daga baya, Jehobah ya annabta cewa Alisabatu za ta haifi ɗa duk da cewa ita tsohuwa ce. Ƙari ga haka, ya gaya ma wata budurwa mai suna Maryamu cewa za ta haifi Ɗansa kuma hakan zai cika alkawarin da ya yi dubban shekaru da suka shige a lambun Adnin.—Far. 3:15.
12. Mene ne Yoshuwa 23:14 da Ishaya 55:10, 11 suka tabbatar mana game da ikon Jehobah?
12 Idan muka yi tunani game da dukan alkawuran da Jehobah ya yi da yadda ya cika su, za mu gano cewa yana da iko sosai. Hakan zai sa mu ƙara gaskata da alkawarin aljanna da ya yi mana. (Karanta Yoshuwa 23:14; Ishaya 55:10, 11.) Da wannan tabbacin, za mu iya taimaka wa mutane su fahimci cewa sabuwar duniya za ta zo da gaske, ba ƙarya ba ce. Ga abin da Jehobah da kansa ya ce game da sabon sammai da sabuwar duniya. Ya ce: “Wannan maganar gaskiya ce, kuma tabbatacciya ce.”—R. Yar. 21:1, 5.
MU SHAGALA A AYYUKAN IBADA
13. Ta yaya taron ikilisiya yake ƙarfafa bangaskiyarmu? Ka bayyana.
13 Hanya ta uku da za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu ita ce ta yin ayyukan ibada a-kai-a-kai. Alal misali, taron ikilisiya yana amfanar mu. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Anna da ta daɗe tana jin daɗin fannoni dabam-dabam na hidima ta cikakken lokaci ta ce: “Taron ikilisiya yana taimaka mini in ƙarfafa bangaskiyata. Ko da mai jawabin bai iya ba da jawabi ba ko bai faɗi wani sabon abu ba, nakan ji wani abin da zai taimaka mini in ƙara sanin koyarwar Littafi Mai Tsarki, ko wani abin da zai ƙarfafa bangaskiyata.”b Muna jin daɗin kalamai masu ban ƙarfafa da ꞌyanꞌuwa a taro suke yi.—Rom. 1:11, 12; 10:17.
14. Ta yaya yin waꞌazi yake ƙarfafa bangaskiyarmu?
14 Muna kuma ƙarfafa bangaskiyarmu idan muka fita waꞌazi. (Ibran. 10:23) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Barbara da ta yi fiye da shekaru 70 tana bauta wa Jehobah ta ce: “A ko da yaushe, yin waꞌazi yana ƙarfafa bangaskiyata sosai. A duk lokacin da nake gaya wa mutane game da alkawuran Jehobah masu ban mamaki, hakan yana sa bangaskiyata ta ƙara ƙarfi.”
15. Ta yaya yin nazari yake ƙarfafa bangaskiyarmu? (Ka kuma duba hotunan.)
15 A ibadarmu, wani abu kuma da ke ƙarfafa bangaskiyarmu shi ne, yin nazari. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Susan ta ce abin da yake taimaka mata shi ne ta tsara lokacin da za ta riƙa yin nazari. Ta ce: “Ranar Lahadi, nakan yi nazarin Hasumiyar Tsaro da za a tattauna a mako na gaba. Ranar Litinin da Talata kuma, nakan shirya taron tsakiyar mako. Sai in yi amfani da sauran ranakun da suka rage don in yi nazari game da wani abu dabam.” Da yake Susan ta ci gaba da bin wannan tsarin, bangaskiyarta sai ƙaruwa take yi. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Irene ta yi shekaru tana hidima a hedkwatarmu. Ita ma ta ce nazarin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki yana ƙarfafa bangaskiyarta. Ta ce: “Idan na ga yadda annabce-annabcen Jehobah suke cika dalla-dalla, abin yana ba ni mamaki.”c
“LALLAI ZA TA ZO”
16. Ya muka san cewa tabbacin da Jehobah ya ba wa Habakkuk ya shafe mu a yau? (Ibraniyawa 10:36, 37)
16 Wasu bayin Jehobah sun daɗe suna jiran ƙarshen wannan zamanin ya zo. Wasu mutane suna ganin cewa ƙarshen zamanin yana jinkirin zuwa. Jehobah ya san yadda bayinsa suke ji. Shi ya sa ya ba wa annabinsa Habakkuk tabbaci ta wajen cewa: “Gama har yanzu ru’uyar tana jira lokacinta tana saurin zuwa ga cikawa, ba za ta zama ƙarya ba. Ko da ma ta daɗe, ka jira ta, lallai za ta zo, ba za ta yi latti ba.” (Hab. 2:3) Shin Habakkuk ne kawai Allah ya ba wa wannan tabbacin? Waɗannan kalaman sun shafe mu a yau kuwa? Ƙwarai da gaske. Jehobah ya hure manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci waɗannan kalmomin. A lokacin, suna jiran sabuwar duniya ta zo. (Karanta Ibraniyawa 10:36, 37.) Ko da muna ganin kamar alkawarin da Jehobah ya yi yana jinkirin zuwa, mu kasance da tabbaci cewa “za ta zo, ba za ta yi latti ba.”
17. Ta yaya wata ꞌyarꞌuwa ta bi gargaɗin da Jehobah ya ba wa Habakkuk?
17 Akwai bayin Jehobah da yawa da suka bi gargaɗin da ya bayar cewa, “ka jira ta,” kuma sun yi shekaru da yawa suna hakan. Alal misali, Louise ta soma bauta wa Jehobah a 1939. Ta ce: “A lokacin, na zata Armageddon zai zo kafin na gama makaranta. Amma hakan bai faru ba. A cikin shekarun nan, karanta labarai game da mutanen da suka jira Jehobah ya cika alkawarinsa ya taimaka mini ni ma in jira alkawuran Jehobah. Na karanta game da Nuhu da Ibrahim da Yusufu da dai sauransu. Gaskata cewa alkawuran nan za su cika ya taimaka mini da wasu ma mu kasance da tabbacin cewa sabuwar duniya ta kusa.” Bayin Jehobah da yawa da suka daɗe suna bauta masa sun yarda da abin da ꞌyarꞌuwar nan ta ce!
18. Ta yaya kallon halittu zai ƙarfafa bangaskiyarmu game da sabuwar duniya?
18 Gaskiya ne cewa sabuwar duniya ba ta zo ba tukuna. Amma ku yi laꞌakari da abubuwan da muke gani yanzu, wato taurari, da bishiyoyi, da dabbobi da kuma mutane. Babu wanda zai yi shakkar cewa akwai abubuwan nan. Ko da yake akwai lokacin da babu su. Yanzu muna ganin su ne domin Jehobah ya halicce su. (Far. 1:1, 26, 27) Haka ma, Allah ya yi alkawari cewa zai yi sabuwar duniya. Zai cika wannan alkawarin. A sabuwar duniya, mutane za su yi rayuwa har abada cikin ƙoshin lafiya. Idan lokacin Jehobah ya yi, za mu ga sabuwar duniyar kuma za ta zama kamar abubuwan da muke gani a yau.—Isha. 65:17; R. Yar. 21:3, 4.
19. Ta yaya za ka ƙarfafa bangaskiyarka?
19 Kafin lokacin, ka yi amfani da duk zarafin da kake da shi don ka ƙarfafa bangaskiyarka. Ka daɗa nuna godiya don fansar Yesu Kristi. Ka riƙa tunani a kan ikon Jehobah. Ka shagala a ayyukan ibada. Idan ka yi abubuwan nan, za ka zama ɗaya daga cikin waɗanda “suka yi haƙuri har suka karɓi abin da Allah ya yi alkawari zai ba su.”—Ibran. 6:11, 12; Rom. 5:5.
WAƘA TA 139 Rayuwa a Cikin Aljanna
a Mutane da yawa ba su gaskata alkawarin da Littafi Mai Tsarki ya yi game da sabuwar duniya ba. Suna ganin cewa tatsuniya ce kawai kuma ba zai taɓa faruwa ba. Amma muna da tabbaci cewa dukan alkawuran Jehobah za su cika. Duk da haka, muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. Ta yaya? Wannan talifin zai gaya mana yadda za mu yi hakan.
b An canja wasu sunaye.
c Za ka iya ganin talifofin da suka yi magana game da annabci a ƙarƙashin jigon nan “Annabci” a Littafin Bincike don Shaidun Jehobah. Alal misali, ka duba talifin nan mai jigo “Abin da Jehobah Ya Annabta Yana Faruwa” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 2008.