TALIFIN NAZARI NA 18
Mu Dinga Ƙarfafa Juna a Taron Ikilisiya
“Mu lura da juna . . . , mu dinga ƙarfafa juna.”—IBRAN. 10:24, 25.
WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Me ya sa muke yin kalami a taro?
ME YA sa muke zuwa taron ikilisiya? Muna yin hakan ne musamman don mu yabi Jehobah. (Zab. 26:12; 111:1) Wani dalili kuma da ya sa muke zuwa taro shi ne, don mu ƙarfafa juna, don muna a lokaci mai wuya. (1 Tas. 5:11) Idan muka ɗaga hannu kuma muka yi kalami a taro, za mu cim ma abubuwa biyun nan.
2. A waɗanne lokuta ne za mu iya yin kalami a taronmu?
2 Kowane mako, muna samun zarafin yin kalami a taro. Misali a ƙarshen mako, za mu iya yin kalami saꞌad da ake nazarin Hasumiyar Tsaro. A taronmu na tsakiyar mako kuma, za mu iya yin kalami idan ana tattauna Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah, da Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya, da wasu sassan taronmu da ake tambayoyi da kuma ba da amsa.
3. Waɗanne abubuwa ne za su iya hana mu yin kalami? Kuma ta yaya Ibraniyawa 10:24, 25 za su taimaka mana?
3 Dukanmu muna so mu yabi Jehobah kuma mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu, amma akwai wasu abubuwa da za su iya sa ya yi mana wuya mu yi kalami. Wataƙila muna jin tsoron yin kalami, ko kuma muna son yin kalami amma wasu lokuta ba a kiranmu saꞌad da muka ɗaga hannu. Me zai taimaka mana idan muna irin waɗannan yanayoyin? Wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Ibraniyawa za ta taimaka mana. Da yake magana a kan muhimmancin zuwa taro, manzo Bulus ya ce mu mai da hankali ga “ƙarfafa juna.” (Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.) Ko da gajeren kalami muka yi, zai ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu. Idan muka tuna hakan, ba za mu ji tsoron yin kalami ba. Idan ma wani lokaci ba a kira mu ba, za mu iya yin farin ciki domin hakan zai ba wasu zarafi su ma su yi kalami.—1 Bit. 3:8.
4. Waɗanne abubuwa uku ne za mu tattauna a wannan talifin?
4 A wannan talifin, za mu fara da tattauna yadda za mu ƙarfafa juna idan muna a ƙaramar ikilisiya inda masu yin kalami ba su da yawa. Bayan haka, za mu tattauna yadda za mu ƙarfafa juna a babbar ikilisiya inda masu yin kalami suna da yawa. A ƙarshe, za mu tattauna abin da za mu yi don abin da za mu faɗa a kalaminmu ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa.
MU ƘARFAFA JUNA IDAN MUNA A ƘARAMAR IKILISIYA
5. Ta yaya za mu ƙarfafa juna idan ba mu da yawa a taro?
5 A ƙananan ikilisiyoyi ko rukunoni, ba a samun mutane da yawa da za su yi kalami. Don haka, a wasu lokuta mai gudanar da nazarin zai ɗan dakata yana jira wani ya ɗaga hannu. Hakan yana sa a ci lokaci a taron, kuma ꞌyanꞌuwa ba za su ji daɗin taron ba. Idan kana a irin wannan ikilisiyar, me za ka yi don ka taimaka? Ka yi shirin yin kalami sau da yawa. Idan ka yi hakan, za ka sa ꞌyanꞌuwa ma su so yin kalami sosai.
6-7. Me zai taimaka mana mu rage jin tsoro idan za mu yi kalami?
6 Amma me za ka yi idan kana jin tsoron yin kalami? Akwai mutane da yawa da suke jin hakan. Don ka ƙarfafa ꞌyanꞌuwa a taron, za ka iya bincika hanyoyin da za ka rage wannan tsoro da kake ji. Ta yaya za ka yi hakan?
7 Akwai shawarwari da aka bayar a talifofin Hasumiyar Tsaro da aka wallafa a baya.b Idan ka bincika su, za su iya taimaka maka. Alal misali, ka yi shiri sosai. (K. Mag. 21:5) Idan ka fahimci abin da za a tattauna sosai, hakan zai sa ya yi maka sauƙi ka yi kalami. Ban da haka, ka yi gajeren kalami. (K. Mag. 15:23; 17:27) Idan kalaminka gajere ne, ba za ka ji tsoro sosai ba. Kuma idan ka yi gajeren kalami, wanda wataƙila jimla ɗaya ce ko biyu, zai ma yi wa ꞌyanꞌuwa sauƙi su fahimta, maimakon dogon kalami. Idan ka yi gajeren kalami kuma ka faɗe shi daga zuciyarka, hakan zai nuna cewa ka yi shiri da kyau kuma ka fahimci abin da ake tattaunawa.
8. Yaya Jehobah yake ji idan ya ga muna iya ƙoƙarinmu?
8 Idan ka gwada yin duka abubuwan nan amma har ila kana jin tsoron yin kalami fiye da sau ɗaya fa? Kar ka damu. Ka tuna cewa Jehobah yana farin ciki don iya ƙoƙarin da kake yi. (Luk. 21:1-4) Yin iya ƙoƙarinka ba ya nufin ka yi abin da ya fi ƙarfinka. (Filib. 4:5) Ka dai san abin da kake so ka yi, kuma ka ƙafa maƙasudin yin sa, saꞌan nan ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin zuciya. Wasu daga cikinmu mukan fara ne da maƙasudin yin gajeren kalami.
MU ƘARFAFA JUNA IDAN MUNA A BABBAR IKILISIYA
9. Wace matsala ce ake iya fuskanta a babbar ikilisiya?
9 Idan akwai masu shela da yawa a ikilisiyarku, za ka iya fuskantar wata matsala dabam. Mai yiwuwa ꞌyanꞌuwa da yawa su yi ta ɗaga hannu har ka ga cewa ba a yawan kiran ka. Alal misali, akwai wata ꞌyarꞌuwa mai suna Danielle da take son yin kalami a taro sosai.c A nata raꞌayin, yin kalami ibada ce, hanya ce da take ƙarfafa ꞌyanꞌuwa, kuma yana sa ta ƙara gaskata koyarwar Littafi Mai Tsarki. Amma da ta koma wata babbar ikilisiya, sai ta ga ba a yawan kiran ta ta yi kalami. Har wani lokaci a yi taro a gama ba ta samu ta yi kalami ba. ꞌYarꞌuwar ta ce: “Abin ya ɓata min rai. Na ji kamar an ɗauke min wani gata ne. Kuma idan hakan ya ci gaba da faruwa, za ka ga kamar da gangan mutumin yake ƙin kiranka.”
10. Me za mu iya yi don mu daɗa samun damar yin kalami?
10 Kai ma ka taɓa jin yadda ꞌyarꞌuwa Danielle ta ji? Irin wannan abin zai iya sa ka ƙi yin kalami kuma ka zauna shuru kawai. Amma kada ka yi hakan. Me zai taimaka maka? Ka dinga shirya kalamai da yawa da za ka yi a taro. Idan ka yi hakan, ko da ba a kira ka saꞌad da aka soma nazarin ba, ba mamaki a kira ka saꞌad da nazarin yake tafiya. Idan kana shirya nazarin Hasumiyar Tsaro, ka yi laꞌakari da alaƙar da ke tsakanin kowane sakin layi da jigon talifin da ake tattaunawa. Hakan zai taimaka maka ka sami kalami mai kyau da za ka yi daga farko har zuwa ƙarshen nazarin. Ban da hakan ma, idan akwai sakin layi da ya tattauna koyarwar Littafi Mai Tsarki mai wuyar bayyanawa, za ka iya shirya yin kalami a wurin. ( 1 Kor. 2:10) Me ya sa? Domin mutane ƙalila ne za su ɗaga hannu a wannan lokacin. Idan ka gwada yin duka abubuwan nan, amma har ila ka ga cewa an yi taro sau da sau kuma ba ka samu ka yi kalami ba fa? Za ka iya zuwa ka sami wanda yake gudanar da nazarin, ka gaya masa tambayar da kake so ya ba ka damar amsawa.
11. Mene ne littafin Filibiyawa 2:4 ta shawarce mu mu yi?
11 Karanta Filibiyawa 2:4. Allah ya hure manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su dinga tunanin abin da zai amfane waɗansu mutane. Ta yaya za mu yi hakan idan muna a taro? Mu tuna cewa ba mu ne kaɗai muke so mu yi kalami ba.
12. Ta wace hanya mai kyau ce za mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwa a taro? (Ka kuma duba hoton.)
12 Ga wani misali. Idan kana hira da abokanka, za ka ta yin magana ne, ba za ka ba su dama su ma su yi magana ba? Ba za ka yi hakan ba, domin kana so su ma su sa baƙi a tattaunawar. Haka ma idan ana taro, zai dace mu bar mutane su ma su yi kalami. Ka tuna cewa ɗaya daga cikin hanyoyi mafi kyau da za mu iya ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu ita ce, ta wurin ba su dama su furta bangaskiyarsu. (1 Kor. 10:24) Bari mu ga yadda za mu yi hakan.
13. Me za mu yi don mutane da yawa su samu damar yin kalami?
13 Wani abu mai muhimmanci shi ne, mu dinga yin gajerun kalamai, hakan zai ba wa ꞌyanꞌuwanmu damar yin kalamai. Zai dace dattawa da masu shela da suka ƙware su kafa misali mai kyau a yin hakan. Ko da gajeren kalami za ka yi, kar ka yi magana a kan batutuwa da yawa. Domin idan ka faɗi kome-da-kome da ke sakin layin, sauran ꞌyanꞌuwa ba za su samu abin da za su faɗa ba. Alal misali, a wannan sakin layin, an ba da shawarwari guda biyu. Wato ka yi gajeren kalami kuma kada ka yi magana a kan batutuwa da yawa. Idan kai aka fara kira ka ba da amsa a wannan sakin layin, zai fi dacewa ka ɗauki ɗaya ka bar ɗaya.
14. Me zai taimaka mana mu san ko zai dace mu ɗaga hannu ko aꞌa? (Ka kuma duba hoton.)
14 Ka yi amfani da basira don ka san lokacin da za ka ɗaga hannunka. Domin idan kana yawan ɗaga hannu, za ka matsa wa mai gudanar da nazarin ya kira ka. Alhali kuwa akwai mutanen da ba su samu damar yin kalami ba ko. Hakan zai iya sa su yi sanyin gwiwa kuma su ƙi ɗaga hannu.—M. Wa. 3:7.
15. (a) Me ya kamata mu yi idan muka ɗaga hannu amma ba a kira mu ba? (b) Ta yaya masu gudanar da nazari za su nuna cewa suna lura da kowa? (Ka kuma duba akwatin nan “Idan Kai Kake Gudanarwa.”)
15 Idan akwai masu shela da yawa da suke so su yi kalami yayin da ake nazari, wataƙila ba za mu samu mu yi kalami yadda muke so ba. Wani lokaci ma mai gudanar da nazarin ba zai kira mu ba. Abin ba sauƙi kam, amma ko da mun ɗaga hannu ba a kira mu ba, kada mu yi fushi.—M. Wa. 7:9.
16. Ta yaya za mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwa da suka yi kalami?
16 Idan ba zai yiwu ka dinga yin kalami yadda kake so ba, kana iya saurara yayin da ꞌyanꞌuwa suke yin kalami, saꞌan nan ka yaba musu bayan taron. Ko da ba ka iya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa ta yin kalami ba, za ka iya ƙarfafa su sosai ta wajen yaba musu. (K. Mag. 10:21) Yaba wa ꞌyanꞌuwanmu wata hanya ce da muke ƙarfafa su.
WASU HANYOYI KUMA DA ZA MU IYA ƘARFAFA JUNA
17. (a) Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su yi kalaman da suka dace? (b) Kamar yadda bidiyon ya nuna, waɗanne abubuwa huɗu ne ya kamata mu yi yayin da muke shirya kalami? (Ka duba ƙarin bayani.)
17 Me kuma za mu iya yi don mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu a taro? Idan kuna da yara, ku taimaka musu su shirya yin kalami da ya yi daidai da shekarunsu. (Mat. 21:16) Mai yiwuwa ba za su samu damar yin kalami sosai ba idan ana tattauna manyan batutuwa kamar matsaloli da ake samu a aure, ko batun ɗabiꞌa. Duk da haka, ba za a rasa sakin layi ɗaya ko biyu da yaro zai iya sa baƙi ba. Ƙari ga haka, ku taimaka wa yaranku su fahimci abin da ya sa wani lokaci ba za a kira su idan suka ɗaga hannu ba. Idan kuka yi musu wannan bayanin, ransu ba zai ɓace ba idan suka ɗaga hannu kuma aka kira wani.—1 Tim. 6:18.d
18. Ta yaya za mu guji yabon kanmu idan muna yin kalami? (Karin Magana 27:2)
18 Dukanmu za mu iya yin shiri don mu yi kalaman da za su sa a yabi Jehobah kuma su ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu. (K. Mag. 25:11) Ko da yake za mu iya ba da labarin abin da ya taɓa faruwa da mu, zai dace mu guji yin magana da yawa game da kanmu. (Karanta Karin Magana 27:2; 2 Kor. 10:18) Maimakon haka, zai fi dacewa mu sa ꞌyanꞌuwa su mai da hankali ga Jehobah, da Kalmarsa da kuma bayinsa gabaki ɗaya. (R. Yar. 4:11) Amma idan tambayar da aka yi tana so mu faɗi abin da ya taɓa faruwa da mu, ko yadda muke ji, zai dace mu yi hakan. Za mu ga misalin wannan a sakin layi na gaba.
19. (a) Me zai faru idan muka mai da hankali ga abin da zai amfani kowa a taronmu? (Romawa 1:11, 12) (b) Me ya fi burge ka game da yin kalami a taro?
19 Babu takamammen doka a kan yadda za a riƙa yin kalami. Amma dukanmu za mu iya yin ƙoƙari mu yi kalaman da za su ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu. Hakan zai iya nufin yin kalami sau da yawa. Ko kuma mu haƙura idan ba za mu iya yin kalami sau da yawa ba, saꞌan nan mu yi farin ciki idan muka ga ꞌyanꞌuwanmu su ma suna yin kalami. Idan muna mai da hankali ga abin da zai amfani waɗansu ba kanmu kaɗai ba, dukanmu za mu ji daɗin “ƙarfafa juna.”—Karanta Romawa 1:11, 12.
WAƘA TA 93 Ka Albarkaci Taronmu
a Mukan ƙarfafa juna idan muna yin kalami a taro. Amma wasu suna jin tsoron yin kalami, wasu kuma suna son yin kalami amma suna ganin ba a yawan kiransu. Ko da yaya yanayinmu, me za mu yi don mu lura da juna, kuma mu ƙarfafa juna? Ta yaya za mu yi kalaman da za su iza ꞌyanꞌuwanmu su nuna ƙauna kuma su yi aikin nagarta? Abin da za a tattauna a talifin nan ke nan.
b Don ka ga wasu shawarwarin kuma, ka karanta Hasumiyar Tsaro ta Janairu 2019, shafuffuka na 8-13, da ta 1 ga Satumba 2003, shafuffuka na 19-22 a Turanci.
c An canja sunan.
d Ka kalli bidiyon nan Ka Zama Abokin Jehobah—Ka Shirya Kalaminka.
f BAYANI A KAN HOTUNA: A wata babbar ikilisiya, wani ɗanꞌuwa da ya riga ya yi kalami ya ƙi ɗaga hannunsa don wasu ma su samu su yi kalami