BABI NA GOMA SHA BIYAR
Bauta da Allah Ya Amince da Ita
Dukan addinai ne suke faranta wa Allah rai?
Ta yaya za mu gane addini na gaskiya?
Su waye suke bauta wa Allah da gaske a yau?
1. Ta yaya za mu amfana idan muka bauta wa Allah a hanyar da ta dace?
JEHOBAH ALLAH yana ƙaunarmu ƙwarai kuma yana so mu amfana daga ja-gorarsa ta ƙauna. Idan muka bauta masa a hanyar da ta dace, za mu zama masu farin ciki kuma za mu guje wa matsalolin rayuwa. Za mu kuwa sami albarka daga wurinsa da kuma taimako. (Ishaya 48:17) Amma, da ɗarurruwan addinai da suke da’awar suna koyar da gaskiya game da Allah. Duk da haka, koyarwarsu game da Allah da kuma abin da yake bukata a gare mu sun bambanta ƙwarai.
2. Ta yaya za mu koyi hanyar da ta dace na bauta wa Jehobah, kuma wane misali ne ya taimake mu mu fahimci haka?
2 Ta yaya za ka san hanyar da ta dace ta bauta wa Jehobah? Ba ka bukatar ka nazarci koyarwa na dukan addinai kuma ka gwada su. Abin da kake bukata shi ne ka koyi abin da Littafi Mai Tsarki ainihi yake koyarwa game da bauta ta gaskiya. Alal misali: A ƙasashe da yawa ana fama da matsalar jabun kuɗi. Idan aka ba ka aikin gano jabun kuɗi, me za ka fara yi? Za ka je ne ka nazarci dukan jabun kuɗi? A’a. Zai fi maka alheri idan ka nazarci kuɗi na gaskiya. Bayan ka fahimci yadda kuɗi na gaskiya suke, za ka iya ka gane jabu. Hakazalika, idan muka san yadda za mu gane addini na gaskiya, za mu iya gane waɗanda suke na ƙarya.
3. Idan muna so mu sami yardar Allah, dole ne mu yi menene in ji Yesu?
3 Yana da muhimmanci mu bauta wa Jehobah a hanyar da ya amince da ita. Mutane da yawa suna tsammanin Allah ya amince da dukan addinai, amma Littafi Mai tsarki bai koyar da haka ba. Muna bukatar fiye da yin da’awar cewa mu Kiristoci ne. Yesu ya ce: “Ba dukan mai-ce mini, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aika nufin Ubana wanda ke cikin sama.” Saboda haka, domin mu sami yardar Allah, dole ne mu koyi abin da Allah yake bukata a gare mu kuma mu yi shi. Yesu ya kira waɗanda ba sa yi abin da Allah yake so “masu-aika mugunta.” (Matta 7:21-23) Kamar jabun kuɗi, addinin ƙarya ba shi da muhimmanci. Fiye ma da haka, irin wannan addinin yana da lahani.
4. Mecece ma’anar kalmomin Yesu game da hanyoyi biyu, kuma ina ne kowace take kai mutane?
4 Jehobah ya ba kowa da ke duniya zarafin samun rai madawwami. Domin mu sami rai madawwami a Aljanna, to, dole ne mu bauta wa Allah yadda ya dace kuma mu yi rayuwa da ya amince da ita. Abin baƙin ciki, mutane da yawa sun ƙi yin haka. Abin da ya sa ke nan Yesu ya ce: “Ku shiga ta wurin ƙunƙuntar ƙofa: gama ƙofa da fāɗi ta ke, hanya kuwa da fāɗi, wadda ta nufa wajen hallaka, mutane dayawa fa suna shiga ta wurinta. Gama ƙofa ƙunƙunta ce, hanya kuwa matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu samunta fa kaɗan ne.” (Matta 7:13, 14) Addinin gaskiya yana sa a sami rai madawwami. Addinin ƙarya yana kai wa ga halaka. Jehobah ba ya so mutane su halaka, abin da ya sa ke nan ya ba mutane a ko’ina zarafi su san shi. (2 Bitrus 3:9) Saboda haka, yadda muke bauta wa Allah zai kai mu ga rai ko kuwa mutuwa.
YADDA ZA A GANE ADDINI NA GASKIYA
5. Ta yaya za mu gane waɗanda suke bin addini na gaskiya?
5 Ta yaya za a sami ‘hanyar rai?’ Yesu ya nuna cewa addini na gaskiya zai bayyana a rayuwar mutane da suke binsa. “Bisa ga ’ya’yansu za ku sansance su,” ya ce. “kowane itacen kirki ya kan fitarda ’ya’yan kirki.” (Matta 7:16, 17) Wato, waɗanda suke bin addini na gaskiya za a gane su ta wajen abin da suka gaskata da kuma ɗabi’arsu. Ko da yake ba kamiltattu ba ne kuma suna yin kuskure, rukunin masu bauta ta gaskiya suna ƙoƙari su yi abin da Allah yake so. Bari mu bincika abubuwa shida da suka nuna waɗanda suke bin addini na gaskiya.
6, 7. Yaya bayin Allah suka ɗauki Littafi Mai Tsarki, kuma yaya Yesu ya kafa misali a wannan?
6 Koyarwar bayin Allah tana da tushe daga cikin Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki kansa ya ce: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: domin mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.” (2 Timothawus 3:16, 17) Ga ’yan’uwansa Kiristoci, manzo Bulus ya rubuta: “Sa’anda kuka karɓi maganar jawabi daga garemu, watau maganar Allah ke nan, kuka karɓe ta, ba kamar maganar mutane ba, amma, yadda ta ke hakika, maganar Allah.” (1 Tassalunikawa 2:13) Saboda haka, abin da aka gaskata da kuma abin da ake yi a addini na gaskiya ba ta samo asali daga ra’ayin mutane ba ko kuma al’adarsu. Sun samo asali ne daga hurarriyar Maganar Allah, Littafi Mai Tsarki.
7 Yesu Kristi ya kafa misali da ya dace wajen koyar da abin da ke cikin Kalmar Allah. A addu’arsa ga Ubansa na samaniya, ya ce: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Yesu ya gaskata Kalmar Allah, kuma dukan abin da ya koyar ya jitu da Nassosi. Sau da yawa Yesu yana cewa: “An kuma rubuta.” (Matta 4:4, 7, 10) Sa’an nan Yesu ya yi ƙaulin nassi. Haka nan, mutanen Allah a yau ba sa koyar da nasu ra’ayi. Sun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce, kuma sun koyar da abin da ya ce.
8. Menene bauta wa Jehobah ta ƙunsa?
8 Waɗanda suke bauta ta gaskiya Jehobah kawai suke bauta wa kuma suna sanar da sunansa. Yesu ya ce: “Ka yi sujjada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta masa.” (Matta 4:10) Saboda haka, bayin Allah ba sa bauta wa wani ban da Jehobah. Wannan bautar ta haɗa da sanar da mutane sunan Allah da kuma yadda yake. Zabura 83:18 ta ce: “Kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Yesu ya kafa misalin taimakon mutane su san Allah, kamar yadda ya ce a cikin addu’arsa: “Na bayana sunanka ga mutane waɗanda ka ba ni daga cikin duniya.” (Yohanna 17:6) Haka nan, masu bauta ta gaskiya a yau suna koyar da mutane sunan Allah, nufe-nufensa, da kuma halayensa.
9, 10. A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci na gaskiya suke ƙaunar juna?
9 Mutanen Allah suna ƙaunar junansu da ƙauna marar son kai. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuma da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Kiristoci na farko suna da irin wannan ƙaunar ga juna. Irin wannan ƙauna ta Allah, ta fi gaban ƙabilanci, da wariya kuma tana jawo mutane ga juna cikin ’yan’uwantaka ta gaskiya. (Kolossiyawa 3:14) Waɗanda suke cikin addinin ƙarya ba su da irin wannan ’yan’uwantaka. Ta yaya muka san wannan? Suna kashe juna domin rashin jituwa ta ƙasa ko kuma ta ƙabila. Kiristoci na gaskiya ba sa ɗaukan makamai su kashe ’yan’uwansu Kiristoci da wasu mutane. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Inda ’ya’yan Allah sun bayyanu ke nan, da ’ya’yan Shaiɗan: dukan wanda ba shi aika adalci ba, ba na Allah ba ne, da wannan kuma wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba . . . Mu yi ƙaunar junanmu: ba kamar Kayinu wanda shi ke na Shaiɗan, ya kashe ɗan’uwansa.”—1 Yohanna 3:10-12; 4:20, 21.
10 Hakika, ƙauna ta gaskiya ta wuce ƙin kashe wasu kawai. Kiristoci na gaskiya suna amfani da lokacinsu, da ƙarfinsu, da dukiyarsu domin su taimaki juna kuma su ƙarfafa juna. (Ibraniyawa 10:24, 25) Suna taimakon juna a lokatan wahala, kuma suna faɗin gaskiya ga wasu. Hakika, suna bin gargaɗin Littafi Mai Tsarki su “aika nagarta zuwa ga dukan mutane.”—Galatiyawa 6:10.
11. Me ya sa yake da muhimmanci a gaskata cewa Allah zai ceci mutane ta Yesu Kristi ne?
11 Kiristoci na gaskiya sun gaskata cewa Allah zai ceci mutane ta hannun Yesu Kristi ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu ceto ga waninsa: gama babu wani suna ƙarƙashin sama, da aka bayar wurin mutane, inda ya isa mu tsira.” (Ayukan Manzanni 4:12) Kamar yadda muka gani a Babi na 5, Yesu ya ba da ransa domin fansar mutane masu biyayya. (Matta 20:28) Bugu da ƙari, Yesu Sarki ne da Allah ya naɗa a Mulkin sama da zai mallaki dukan duniya. Kuma Allah yana bukatar mu yi wa Yesu biyayya kuma mu bi koyarwarsa idan muna son rai madawwami. Abin da ya sa ke nan Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda yana bada gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada; amma wanda ba ya yi biyayya ga Ɗan ba, ba za shi ganin rai ba.”—Yohanna 3:36.
12. Menene kasancewa ba na duniya ba ya ƙunsa?
12 Masu bauta na gaskiya ba na duniya ba ne. Sa’ad da ake yi masa hukunci a gaban Bilatus masarauci na Romawa, Yesu ya ce: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.” (Yohanna 18:36) Ko a wace ƙasa suke da zama, mabiyan Yesu talakawa ne na Mulkin sama kuma saboda haka ba sa saka hannu a sha’anin siyasa na duniya. Ba sa saka hannu kuma a cikin yaƙe-yaƙenta. Amma kuma, babu ruwan masu bauta wa Jehobah idan mutum ya zaɓi ya shiga siyasa, ya tsaya takara, ko kuma ya yi zaɓe. Ko da yake, masu bauta wa Allah da gaske babu ruwansu da siyasa, masu kiyaye doka ne. Me ya sa? Domin Kalmar Allah ta umurce su su yi “biyayya” ga gwamnatoci “masu mulki.” (Romawa 13:1) Amma idan akwai saɓani tsakanin abin da Allah yake bukata da abin da tsarin siyasa yake bukata, masu bauta ta gaskiya suna bin misalin manzani, waɗanda suka ce: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:29; Markus 12:17.
13. Yaya mabiyan Yesu na gaskiya suke ɗaukan Mulkin Allah, kuma wane mataki suka ɗauka?
13 Mabiyan Yesu na gaskiya suna wa’azi cewa Mulkin Allah shi ne kawai zai magance matsalolin mutane. Yesu ya annabta cewa: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14) Mabiyan Yesu Kristi na gaskiya suna shelar Mulkin Allah cewa shi ne kawai zai magance matsalolin mutane maimakon su ƙarfafa mutane su dogara ga shugabanni su magance matsalolinsu. (Zabura 146:3) Yesu ya koya mana mu yi addu’a game da wannan gwamnatin sa’ad da ya ce: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Kalmar Allah ta annabta cewa Mulkin sama “za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Daniel 2:44.
14. Wane rukunin addini ne ka gaskata cewa ya cika dukan bukatu domin bauta ta gaskiya?
14 Bisa ga abin da muka tattauna, ka tambayi kanka: ‘Wane addini ya samo dukan abin da yake koyarwa daga Littafi Mai Tsarki kuma yake sanar da sunan Jehobah? Wane rukuni ne yake nuna ƙauna irin ta Allah, yake ba da gaskiya a Yesu, kuma ba na duniya ba, kuma yake sanar da Mulkin Allah cewa shi ne kawai zai magance matsalolin mutane? A cikin dukan addinai na duniya, wannene ne ya cika dukan waɗannan bukatu?’ Dukan waɗannan sun nuna cewa Shaidun Jehobah ne.—Ishaya 43:10-12.
MENENE ZA KA YI?
15. Menene kuma Allah yake bukata ƙari ga gaskata cewa yana wanzuwa?
15 Ba gaskata wa da Allah ba ne kawai ake bukata domin a faranta masa rai. Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya ce aljanu ma sun gaskata Allah yana wanzuwa. (Yaƙub 2:19) A bayyane yake cewa ba sa yin abin da Allah yake so kuma bai amince musu ba. Domin mu sami amincewarsa dole ne mu gaskata yana wanzuwa kuma dole ne mu yi abin da yake so. Dole ne kuma mu raba gari da addinin ƙarya mu rungumi bauta ta gaskiya.
16. Menene ya kamata a yi game da saka hannu a addini na ƙarya?
16 Manzo Bulus ya nuna cewa dole ne mu guji saka hannu cikin addinin ƙarya. Ya rubuta: “Ku fito daga cikinsu, ku ware, in ji Ubangiji, Kada ku taɓa kowane abu mara-tsarki; Ni ma in karɓe ku.” (2 Korinthiyawa 6:17; Ishaya 52:11) Saboda haka Kiristoci na gaskiya suke guje wa dukan wani abin da zai haɗa su da bauta ta ƙarya.
17, 18. Mecece “Babila Babba,” kuma me ya sa yake da gaggawa a “fito daga cikinta”?
17 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dukan addinai na ƙarya ɓangaren “Babila Babba” ne.a (Ru’ya ta Yohanna 17:5) Wannan sunan yana tuna mana birnin Babila na dā, inda addinin ƙarya ya samo asali bayan Ambaliyar zamanin Nuhu. Abubuwa da yawa da ake koyarwa kuma ake yi a addinin ƙarya sun samo asali ne tun dā daga Babila. Alal misali, Babilawa suna bauta wa allah uku cikin ɗaya. A yau, cibiyar koyarwa ta yawancin addinai allah uku cikin ɗaya ne. Amma Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah ɗaya ne, Jehobah, kuma Yesu Kristi Ɗansa ne. (Yohanna 17:3) Babilawa kuma sun gaskata cewa mutane suna da kurwa da take rayuwa bayan mutum ya mutu kuma za ta wahala a wajen gana azaba. A yau, ana koyar da cewa kurwa za ta wahala a cikin wuta a yawancin addinai.
18 Tun da bauta ta Babilawa na dā ta yaɗu a duniya, Babila Babba ta zamani za a iya ce da ita daular addinan ƙarya ta duniya. Kuma Allah ya ce wannan daular ta addinan ƙarya za ta halaka farat ɗaya ba zato ba tsammani. (Ru’ya ta Yohanna 18:8) Ka ga abin da ya sa yake da muhimmanci ka ware kanka daga Babila Babba? Jehobah Allah yana so ka “fito daga cikinta” da wuri tun da sauran lokaci.—Ru’ya ta Yohanna 18:4.
19. Menene za ka samu domin bauta wa Jehobah?
19 Domin ka yanke shawarar ka daina yin addinin ƙarya, wasu mutane za su zaɓi su daina hurɗa da kai. Amma ta wajen bauta wa Jehobah tare da mutanensa, za ka sami albarka fiye da yadda za ka yi rashi. Kamar almajiran Yesu na farko waɗanda suka ƙyale abubuwa domin su bi shi, za ka sami ’yan’uwa maza da mata na ruhaniya da yawa. Za ka shiga cikin iyali mai girma na miliyoyin Kiristoci na gaskiya na dukan duniya waɗanda suke nuna ƙauna ta gaskiya. Kuma za ka sami bege mai ban sha’awa ta rai madawwami a zamani mai zuwa. (Markus 10:28-30) Wataƙila daga baya, waɗanda suka ƙi ka domin abin da ka gaskata za su bincika abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa su zama masu bauta wa Jehobah.
20. Menene yake zuwa a nan gaba ga waɗanda suke bin addini na gaskiya?
20 Littafi Mai Tsarki yana koyar da cewa ba da daɗewa ba Allah zai kawo ƙarshen wannan mugun zamani zai sake shi da sabuwar duniya mai adalci a ƙarƙashin sarautarsa. (2 Bitrus 3:9, 13) Wannan duniya ce mai ban sha’awa! Kuma a wannan sabon zamani, addini ɗaya ne kawai zai kasance, da kuma hanyar bauta guda ɗaya kawai. Ba hikima ba ce a gare ka ka ɗauki matakai da ake bukata domin ka yi hulɗa da masu bauta ta gaskiya a yanzu?
a Domin ƙarin bayani game da abin da ya sa Babila Babba take wakiltan daular addinin ƙarya ta duniya, dubi Rataye, shafuffuka na 219-220.