DARASI NA 10
Ta Yaya Ne Za Ka Gane Bauta ta Gaskiya?
1. Shin addini na gaskiya guda ɗaya ne tak?
Yesu ya koya wa mabiyansa addini guda ɗaya tak, wato, addini na gaskiya. Yana kama ne da hanyar da take kai ga rai na har abada. Yesu ya ce: “Masu samunta fa kaɗan ne.” (Matta 7:14) Allah yana amincewa ne kawai da bautar da ta jitu da Kalmarsa ta gaskiya. Dukan masu bauta ta gaskiya suna da imani guda.—Karanta Yohanna 4:23, 24; 14:6; Afisawa 4:4, 5.
Ka kalli bidiyon nan Allah Yana Amince da Dukan Addinai Kuwa?
2. Mene ne Yesu ya faɗa game da Kiristoci na ƙarya?
Yesu ya ba da gargaɗi cewa annabawan ƙarya za su ɓata Kiristanci. Suna da’awar cewa su Kiristoci na gaskiya ne. Amma, za ka iya sanin cewa su ba Kiristoci na gaskiya ba ne. Ta yaya? Kiristoci na gaskiya ne kaɗai suke da halaye masu kyau.—Karanta Matta 7:13-23.
3. Ta yaya za ka gane masu bauta ta gaskiya?
Ka yi la’akari da waɗannan alamu guda biyar:
Masu bauta ta gaskiya suna daraja Littafi Mai Tsarki a matsayin Kalmar Allah. Suna rayuwar da ta jitu da mizanansa. Saboda haka, addini na gaskiya ya bambanta da addinin da ke bisa ra’ayin mutane. (Matta 15:7-9) Masu bauta ta gaskiya suna aikata abin da suke wa’azinsa.—Karanta Yohanna 17:17; 2 Timotawus 3:16, 17.
Mabiyan Yesu na gaske suna ɗaukaka sunan Jehobah. Yesu ya ɗaukaka sunan Allah ta wajen sanar da shi. Ya taimaka wa mutane su san Allah kuma ya koya musu su yi addu’a cewa a tsarkake sunan Allah. (Matta 6:9) A inda kake da zama, wane addini ne yake sanar wa mutane sunan Allah?—Karanta Yohanna 17:26; Romawa 10:13, 14.
Kiristoci na gaskiya suna wa’azi game da Mulkin Allah. Allah ya aiko Yesu ya yi wa’azi game da Mulkinsa. Mulkin Allah ne kaɗai zai warware matsalolin ’yan Adam. Yesu ya ci gaba da yin magana game da mulkin har ranar da ya mutu. (Luka 4:43; 8:1; 23:42, 43) Ya gaya wa mabiyansa su yi wa’azi game da Mulkin Allah. Sa’ad da wani ya zo wurin ka domin ya yi maka magana game da Mulkin Allah, kana ganin shi ɗan wane addini ne?—Karanta Matta 24:14.
Mabiyan Yesu ba na wannan muguwar duniyar ba ce. Za ka iya saninsu domin ba sa saka hannu a siyasa ko tarzoma. (Yohanna 17:16; 18:36) Ba sa kuma bin ayyuka da halaye masu lahani na duniyar nan.—Karanta Yaƙub 4:4.
Kiristoci na gaskiya suna nuna ƙauna ta musamman ga juna. Sun koya daga Kalmar Allah cewa ya kamata su riƙa daraja mutanen kowace ƙabila. Ko da yake addinin ƙarya ya goyi bayan yaƙe-yaƙe sau da yawa, amma masu bauta ta gaskiya sun ƙi yin haka. (Mikah 4:1-3) A maimakon haka, Kiristoci na gaskiya suna amfani da lokacinsu da kuma dukiyarsu ba tare da son kai ba don su taimaka wa mutane kuma su ƙarfafa su.—Karanta Yohanna 13:34, 35; 1 Yohanna 4:20.
4. Za ka iya sanin addini na gaskiya kuwa?
Wane addini ne yake gudanar da dukan koyarwarsa daga Kalmar Allah da girmama sunan Allah da kuma yin shela cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolin ’yan Adam? Wane rukuni ne yake nuna ƙauna kuma ba ya goyon bayan yaƙi? Mece ce amsarka?—Karanta 1 Yohanna 3:10-12.