Ka Koya Daga Kalmar Allah
Ta Yaya Ne Za Ka Gane Bauta ta Gaskiya?
Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Shin Addini na gaskiya guda ɗaya ne tak?
Yesu ya koya wa mabiyansa addini guda ɗaya tak, wato, addini na gaskiya. Yana kama ne da hanyar da take kai ga rai. Game da wannan hanyar, Yesu ya ce: “Masu samunta fa kaɗan ne.” (Matta 7:14) Allah yana amincewa ne kawai da bautar da ta jitu da Kalmarsa ta gaskiya. Dukan masu bauta ta gaskiya suna da bangaskiya guda.—Karanta Yohanna 4:23, 24; 14:6; Afisawa 4:4, 5.
2. Me ya sa addinai dabam-dabam da yawa suke da’awar cewa suna cikin addinin Kirista?
Annabawan ƙarya sun ɓata Kiristanci kuma sun yi amfani da ita don cim ma burinsu. Kamar yadda Yesu ya annabta, suna gabatar da kansu a matsayin “tumakin[sa],” amma suna yin abubuwa ne kamar karnukan daji da ke jin yunwa. (Matta 7:13-15, 21, 23) Kiristanci na ƙarya ya taso ne musamman bayan mutuwar manzannin Yesu.—Karanta Ayyukan Manzanni 20:29, 30.
3. Waɗanne abubuwa ne suke bayyana bauta ta gaskiya?
Masu bauta ta gaskiya sun ɗauki Littafi Mai Tsarki a matsayin Kalmar Allah. Suna ƙoƙartawa su yi rayuwar da ta jitu da mizanansa. Saboda haka, addini na gaskiya ya bambanta da addinin da ke bisa ra’ayin mutane. (Matta 15:7-9) Masu bauta ta gaskiya suna aikata abin da suke wa’azinsa.—Karanta Yohanna 17:17; 2 Timotawus 3:16, 17.
Addini na gaskiya yana ɗaukaka sunan Jehobah. Yesu ya sanar da sunan Allah. Ya taimaka wa mutane su san Allah kuma ya koya musu su yi addu’a cewa a tsarkake sunan Allah. (Matta 6:9) A inda kake da zama, wane addini ne yake yaɗa yin amfani da sunan Allah?—Karanta Yohanna 17:26; Romawa 10:13, 14.
4. Ta yaya za ka gane masu bauta ta gaskiya?
Kiristoci na gaskiya suna wa’azi game da Mulkin Allah. Allah ya aiko Yesu ya yi wa’azi game da Mulkin Allah. Mulkin Allah shi ne kaɗai begen da ’yan Adam suke da shi na warware matsalolinsu. Yesu ya ci gaba da yin magana game da shi har ranar da ya mutu. (Luka 4:43; 8:1; 23:42, 43) Ya gaya wa mabiyansa su yi wa’azi game da Mulkin Allah. Sa’ad da wani ya zo wurin ka domin ya yi maka magana game da Mulkin Allah, daga wane addini ne kake ganin yake?—Karanta Matta 10:7; 24:14.
Mabiyan Yesu ba na wannan muguwar duniyar ba ne. Ba sa saka hannu a siyasa ko tarzoma. (Yohanna 17:16) Ba sa kuma bin ayyuka da halaye masu lahani na duniyar nan.—Karanta Yaƙub 1:27; 4:4.
5. Mece ce alama ta musamman da ta bambanta Kiristanci na gaskiya?
Kiristoci na gaskiya suna nuna ƙauna ta musamman ga juna. Daga Kalmar Allah, sun koyi su daraja mutanen kowace ƙabila. Ko da yake addinin ƙarya ya goyi bayan yaƙe-yaƙe sau da yawa, masu bauta ta gaskiya sun ƙi yin haka. (Mikah 4:1-4) A maimakon haka, waɗanda suke cikin addinin gaskiya suna amfani da lokacinsu da kuma dukiyarsu ba tare da son kai ba don su taimaka wa mutane kuma su ƙarfafa su.—Karanta Yohanna 13:34, 35; 1 Yohanna 4:20, 21.
Wane rukuni ne yake gudanar da dukan koyarwarsa daga Kalmar Allah, wane rukuni ne yake girmama sunan Allah, kuma yake yin shela cewa Mulkin Allah ne kaɗai begen ’yan Adam? Wane rukuni ne yake nuna ƙauna kuma ba ya goyon bayan yaƙi? A gaskiya, Shaidun Jehobah ne.—1 Yohanna 3:10-12.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 15 na wannan littafin Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Hoto a shafi na 16]
“Suna shaida, cewa, sun san Allah; amma ta wurin ayyukansu sun yi musunsa.”—Titus 1:16