TALIFIN NAZARI NA 33
Jehobah Yana Lura da Mutanensa
“Idanun Yahweh suna a kan masu tsoronsa.”—ZAB. 33:18.
WAƘA TA 4 “Jehobah Makiyayina Ne”
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Me ya sa Yesu ya roƙe Jehobah ya lura da mabiyansa?
A DARE na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya roƙe Jehobah wani abu na musamman, wato ya lura da mabiyansa. Hakika tun kafin lokacin, Jehobah yana lura da mutanensa kuma yana kāre su. (Yoh. 17:15, 20) Amma Yesu ya san cewa Shaiɗan zai tsananta wa mabiyansa a hanyar da ba a taɓa gani ba. Yesu ya kuma san cewa za su bukaci taimakon Jehobah kafin su iya yin tsayayya da Shaiɗan.
2. Bisa ga Zabura 33:18-20, me ya sa bai kamata mu ji tsoron matsaloli ba?
2 Duniyar nan da Shaiɗan yake iko da ita tana jawo wa Kiristoci matsaloli sosai. Muna fuskantar matsaloli da za su iya sa mu sanyin gwiwa kuma su jarraba amincinmu. Amma kamar yadda za mu gani, bai kamata mu ji tsoro ba. Jehobah yana lura da mu. Yana ganin matsalolinmu kuma yana a shirye ya taimaka mana mu magance su. Bari mu tattauna misalai biyu daga Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa “idanun Yahweh suna a kan masu tsoronsa.”—Karanta Zabura 33:18-20.
JEHOBAH YANA TAIMAKA MANA SA’AD DA MUKA JI KAMAR MU KAƊAI NE
3. A waɗanne lokuta ne za mu iya ji kamar mu kaɗai ne?
3 Ko da yake muna da ’yan’uwa maza da mata da yawa a cikin ikilisiya, a wasu lokuta za mu iya ji kamar mu kaɗai ne. Alal misali, matasa za su iya ji kamar ba su da mai taimako sa’ad da suke bayyana imaninsu a makaranta ko kuma suka ƙaura zuwa sabuwar ikilisiya. Wasun mu za mu iya baƙin ciki ko sanyin gwiwa har mu ga kamar babu wanda zai iya taimaka mana mu jimre. Za mu iya jinkirin gaya ma wasu yadda muke ji domin a ganin mu ba za su fahimci yadda muke ji ba. A wasu lokuta ma za mu iya ɗauka kamar babu wanda ya damu da mu. Ko da wane dalili ne yake sa mu kaɗaita, kaɗaici zai iya sa mu damu kuma mu ji kamar ba mu da mai taimako. Jehobah ba ya so mu ji hakan. Me ya sa muka faɗi hakan?
4. Me ya sa annabi Iliya ya ce: “Ni ne kaɗai na rage”?
4 Ka yi la’akari da misalin annabi mai amincin nan, wato Iliya. Yezebel ta ɗauki alkawari cewa za ta kashe shi kuma hakan ya sa ya yi fiye da kwanaki 40 yana guduwa. (1 Sar. 19:1-9) Da ya isa wani ƙogo shi kaɗai, sai ya ce wa Jehobah: “Ni ne kaɗai [annabin da ya] rage.” (1 Sar. 19:10) Akwai wasu annabawa a ƙasar. Obadiya ya ɓoye annabawa 100 don kada Yezebel ta kashe su. (1 Sar. 18:7, 13) Amma me ya sa Iliya ya ga kamar shi kaɗai ne ya rage? Shin ya ɗauka cewa annabawan da Obadiya ya ɓoye sun mutu ne? Ko ya ji kamar shi kaɗai ne ya rage da yake wasu Isra’ilawa ba su soma bauta wa Jehobah ba duk da cewa Jehobah ya nuna cewa shi ne Allah na gaskiya a babban Tudun Karmel? Ko dai ya ɗauka kamar ba wanda ya san cewa maƙiyansa suna so su kashe shi, ko kuma babu wanda ya damu da shi? Littafi Mai Tsarki bai gaya mana kome da kome game da yadda Iliya ya ji ba. Amma abin da muka sani shi ne Jehobah ya fahimci yadda Iliya yake ji kuma ya san daidai yadda zai taimaka masa.
5. Ta yaya Jehobah ya tabbatar wa Iliya cewa ba shi kaɗai ba ne ya rage?
5 Jehobah ya taimaka wa Iliya a hanyoyi dabam-dabam. Ya ba Iliya dama ya yi magana. Sau biyu ya tambayi Iliya: “Me kake yi a nan?” (1 Sar. 19:9, 13) Kuma yayin da Iliya yake ba da amsa, Jehobah ya saurari Iliya da kyau. Jehobah ya taimaka wa Iliya ta wajen nuna masa cewa yana tare da shi kuma yana da iko sosai. Ban da haka, ya tabbatar wa Iliya cewa yana da mutane da yawa da suke bauta masa. (1 Sar. 19:11, 12, 18) Babu shakka, hankalin Iliya ya kwanta bayan ya gaya wa Jehobah yadda yake ji kuma ya ji abin da Jehobah ya faɗa. Sai Jehobah ya ba Iliya ayyuka masu muhimmanci. Ya gaya masa ya naɗa Hazayel a matsayin sarkin Suriya, Yehu kuma a matsayin sarkin Isra’ila, sa’an nan ya naɗa Elisha annabi. (1 Sar. 19:15, 16) Ayyukan da Jehobah ya ba shi sun taimaka masa ya mai da hankali ga abubuwan da suka dace. Ƙari ga haka, Jehobah ya ba shi abokin aiki, wato Elisha. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah zai iya taimaka maka idan ka kaɗaita?
6. Me za ka iya yin addu’a a kai idan ka kaɗaita? (Zabura 62:8)
6 Jehobah yana so ka yi addu’a a gare shi. Yana ganin matsalolin da kake ciki, kuma ya tabbatar maka cewa zai saurari addu’o’inka a duk lokacin da ka yi su. (1 Tas. 5:17) Yana jin daɗin saurarar addu’o’in masu bauta masa. (K. Mag. 15:8) Me za ka iya yin addu’a a kai idan ka kaɗaita? Ka gaya wa Jehobah yadda kake ji kamar yadda Iliya ya yi. (Karanta Zabura 62:8.) Ka gaya masa abubuwan da ke damun ka da yadda suke sa ka ji. Ka roƙe shi ya taimaka maka ka san abin da ya kamata ka yi yayin da kake baƙin ciki ko ka kaɗaita. Alal misali, idan ka ji tsoro yayin da aka yi maka tambayoyi game da imaninka a makaranta, ka roƙe Jehobah ya ba ka ƙarfin zuciya don ka bayyana imaninka. Za ka ma iya tambayar sa ya ba ka hikima don ka yi hakan cikin basira. (Luk. 21:14, 15) Idan kana baƙin ciki ko sanyin gwiwa, ka roƙe Jehobah ya taimake ka ka tattauna hakan da wani Kirista da ya manyanta. Za ka iya roƙan Jehobah ya taimaka masa ya saurare ka da kyau kuma ya fahimci yadda kake ji. Ka gaya wa Jehobah abin da ke zuciyarka. Ka lura da yadda yake amsa addu’arka kuma ka amince da taimakon wasu. Hakan zai sa ka rage jin kaɗaici.
7. Me ka koya daga labarin Mauricio?
7 Jehobah ya ba dukanmu aiki mai gamsarwa. Ka tabbata cewa yana lura da dukan ayyukan da kake yi a ikilisiya da kuma yayin da kake wa’azi kuma yana ɗaukan hakan da daraja sosai. (Zab. 110:3) Ta yaya yin waɗannan ayyukan da himma zai taimaka maka sa’ad da kake ji kamar kai kaɗai ka rage? Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai suna Mauricio.b Ba da daɗewa ba bayan Mauricio ya yi baftisma, a hankali wani babban abokinsa ya soma barin Jehobah. Mauricio ya ce: “Ganin yadda yake barin Jehobah a hankali ya sa ni sanyin gwiwa. Na ji tsoro cewa ba zan iya riƙe amincina ga Jehobah ko in ci gaba da kasancewa a ƙungiyarsa ba. Na kaɗaita kuma na ɗauka cewa ba wanda zai fahimci yadda nake ji.” Me ya taimaka wa Mauricio? Ya ce: “Na ƙara himma a yin wa’azi. Hakan ya taimaka min in daina tunani game da kaina da kuma yadda nake ji. Na fara farin ciki kuma na rage jin kaɗaici yayin da nake wa’azi tare da ’yan’uwa.” Hakika, ko da ba za mu iya yin wa’azi da ’yan’uwanmu ido da ido ba, za mu iya samun ƙarfafa daga yin wa’azi ta wurin rubuta wasiƙu da kuma waya. Me kuma ya taimaka wa Mauricio? Ya ƙara da cewa: “Na ƙara himma a ayyukan da nake yi a cikin ikilisiya. Na yi iya ƙoƙarina don in shirya kuma in yi jawabai da aka ba ni da kyau a taro. Yin ayyukan ya taimaka mini in san cewa Jehobah da ’yan’uwa a ikilisiya suna daraja abin da nake yi.”
JEHOBAH ZAI TAIMAKE MU IDAN MUNA SANYIN GWIWA DON MATSALOLI
8. Yaya matsaloli za su iya sa mu ji?
8 Mun san cewa za mu fuskanci matsaloli a waɗannan kwanaki na ƙarshe. (2 Tim. 3:1) Amma akwai wasu irin matsaloli da ba za mu yi zaton cewa za mu shiga ba, ko kuma mu yi mamakin lokacin da suka faɗo mana. Za mu iya talaucewa ko rashin lafiya ya kama mu ko kuma wani da muke ƙauna ya mutu ba tsammani. Idan hakan ya faru, za mu iya baƙin ciki da kuma sanyin gwiwa musamman idan muna fuskantar matsalolin ɗaya bayan ɗaya ko kuma dukan su a lokaci ɗaya. Amma ka tuna cewa Jehobah yana lura da mu kuma da taimakonsa za mu iya fuskantar duk wata matsalar da za ta same mu.
9. Ka bayyana wasu daga cikin jarrabobin da Ayuba ya fuskanta.
9 Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya taimaka wa mutum mai amincin nan, Ayuba. Ya fuskanci manyan matsaloli a cikin ƙanƙanin lokaci. A cikin kwana ɗaya, Ayuba ya ji cewa ya rasa dukan dabbobinsa kuma an kashe bayinsa da yaransa. (Ayu. 1:13-19) Bayan haka, ya kamu da wani rashin lafiya da ya lalata jikinsa duk da cewa yana kan makoki. (Ayu. 2:7) Yanayinsa ya yi muni har ya kai ga Ayuba ya ce: “Ina ƙyamar raina, na gaji da rayuwa.”—Ayu. 7:16.
10. Ta yaya Jehobah ya ba Ayuba abin da yake bukata don ya jimre matsalolinsa? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
10 Jehobah ya kāre Ayuba. Jehobah ya ba Ayuba abubuwan da yake bukata don riƙe amincinsa domin Jehobah yana ƙaunar shi. Jehobah ya yi magana da Ayuba kuma ya tuna masa cewa shi Allah ne mai hikima da babu kamar sa, cewa yana ƙauna da kuma kula da halittunsa. Ya yi magana game da dabbobi masu ban mamaki. (Ayu. 38:1, 2; 39:9, 13, 19, 27; 40:15; 41:1, 2) Ƙari ga haka, Jehobah ya yi amfani da wani saurayi mai aminci mai suna Elihu don ya ƙarfafa Ayuba kuma ya ta’azantar da shi. Elihu ya tabbatar masa cewa Jehobah ba ya fasa ba da lada ga bayinsa da suka jimre. Amma Jehobah ya sa Elihu ya ɗan yi wa Ayuba gargaɗi a hanyar da ta nuna cewa yana ƙaunar Ayuba. Elihu ya taimaka wa Ayuba ya daina tunani game da kansa kuma ya tuna masa cewa ba mu kai kome ba idan aka kwatanta mu da Jehobah, Mahaliccin sama da ƙasa. (Ayu. 37:14) Jehobah ya kuma ba Ayuba aiki. Ya ce masa ya yi addu’a a madadin abokansa guda uku da suka yi zunubi. (Ayu. 42:8-10) A wace hanya ce Jehobah yake taimaka mana a yau yayin da muke fuskantar matsaloli?
11. A wace hanya ce Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana idan muna fuskantar jarrabobi?
11 A yau, Jehobah ba ya magana da mu kamar yadda ya yi da Ayuba, amma yana mana magana ta wurin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. (Rom. 15:4) Yana ƙarfafa mu ta wajen alkawuran da ya yi mana game da nan gaba. Ka yi la’akari da wasu nassosin da za su iya ƙarfafa mu idan muna fuskantar jarrabawa. Jehobah ya ce babu abin da ya isa ya “raba mu da ƙaunar” shi ko da jarrabobi masu tsanani ne. (Rom. 8:38, 39) Ƙari ga haka, yana tabbatar mana cewa yana ‘kurkusa da masu kira gare shi.’ (Zab. 145:18) Jehobah ya gaya mana cewa idan muka dogara gare shi, za mu iya jimre duk matsalar da muke fuskanta har ma mu yi farin ciki ko da muna shan wahala. (1 Kor. 10:13; Yak. 1:2, 12) Kalmar Allah ta tuna mana cewa matsalolinmu sun kusan ƙarewa kuma ba su isa kome ba idan aka gwada su da rai na har abada da Allah zai ba mu a nan gaba. (2 Kor. 4:16-18) Jehobah ya tabbatar mana cewa zai hallaka wanda yake jawo matsalolinmu, wato Shaiɗan Iblis da kuma duka waɗanda suke mugunta kamar shi. (Zab. 37:10) Shin ka haddace wasu nassosi da za su iya ƙarfafa ka idan kana fuskantar matsaloli a nan gaba?
12. Mene ne Jehobah yake so mu yi idan muna so mu amfana sosai daga Kalmarsa?
12 Jehobah yana so mu riƙa keɓe lokaci don nazarin Kalmarsa a kai a kai da kuma yin tunani mai zurfi a kan abin da muka karanta. Idan muka yi abin da muka karanta, bangaskiyarmu za ta daɗa ƙarfi kuma za mu daɗa kusantar Ubanmu na sama. Hakan zai taimaka mana mu jimre jarrabobi. Ƙari ga haka, Jehobah yana ba da ruhunsa mai tsarki ga waɗanda suke dogara ga Kalmarsa. Ruhun zai ba mu “cikakken ikon da ya fi duka” don mu jimre duk wata jarrabawa.—2 Kor. 4:7-10.
13. Ta yaya abubuwan da “bawan nan mai aminci, mai hikima” yake tanadarwa suke taimaka mana mu jimre matsaloli?
13 Da taimakon Jehobah, “bawan nan mai aminci, mai hikima” yana tanadar da abubuwa da yawa kamar talifofi da waƙoƙi da bidiyoyi da za su iya taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma su taimaka mana mu kusaci Jehobah. (Mat. 24:45) Ya kamata mu yi amfani da dukan abubuwan nan da Jehobah yake ba mu. Kwanan nan, wata ’yar’uwa daga Amirka ta nuna godiyarta don abubuwan nan. Ta ce: “A cikin shekaru 40 da na yi ina bauta wa Jehobah, na fuskanci abubuwa da dama da suka jarraba amincina.” Wani direban da ya bugu ya kashe kakanta. Iyayenta sun mutu sanadiyyar wani mummunan rashin lafiya kuma sau biyu ta yi fama da cutar kansa. Me ya taimaka mata ta jimre? Ta ce: “Jehobah bai daina kula da ni ba. Abubuwa da yake tanadar mana ta wajen ‘bawan nan mai aminci, mai hikima’ don mu ƙarfafa bangaskiyarmu suna taimaka min in jimre. Saboda haka, zan iya faɗan abin da Ayuba ya faɗa cewa: ‘Har in mutu, ba zan rabu da amincina ba.’ ”—Ayu. 27:5, New World Translation.
14. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah zai yi amfani da ’yan’uwanmu ya taimake mu sa’ad da muke cikin matsala? (1 Tasalonikawa 4:9)
14 Jehobah ya koya wa mutanensa yadda za su ƙaunace juna kuma su ƙarfafa juna a lokacin wahala. (2 Kor. 1:3, 4; karanta 1 Tasalonikawa 4:9.) Kamar yadda Elihu ya yi, ’yan’uwanmu maza da mata ma suna marmarin taimaka mana mu riƙe amincinmu sa’ad da muke fuskantar matsaloli. (A. M. 14:22) Alal misali, ka yi la’akari da yadda ikilisiyar Diane ta ƙarfafa ta kuma ta taimaka mata ta kusace Jehobah bayan da maigidanta ya yi wani mummunan rashin lafiya. Ta ce: “Abin bai yi min sauƙi ba. Amma mun gan yadda Jehobah ya taimaka mana kuma ya ƙarfafa mu a lokacin da muke cikin matsalar. Ikilisiyarmu ma ta taimaka mana sosai. Sun ziyarce mu, sun kira mu ta waya kuma sun rungume mu, duk don su ƙarfafa mu. Da yake ban iya tuƙi ba, ’yan’uwan sukan tabbata cewa na iya zuwa taro da kuma wa’azi a duk lokacin da na sami damar yin hakan.” Muna farin ciki don muna da ’yan’uwa masu ƙaunar mu sosai a ikilisiyoyinmu!
MUNA GODIYA DON YADDA JEHOBAH YAKE LURA DA MU
15. Me ya sa muka tabbata cewa za mu iya jimre jarrabobi?
15 Kowannenmu zai fuskanci jarrabawa. Amma Jehobah ba zai bar mu mu kaɗai mu fuskanci jarrabawar ba. Kamar yadda uba mai ƙauna yake yi, Jehobah yana lura da mu a kullum. Yana kurkusa da mu, yana a shirye ya ji roƙonmu kuma ya taimake mu. (Isha. 43:2) Mun tabbata cewa za mu iya jimre jarrabobi domin Jehobah ya riga ya ba mu dukan abubuwan da muke bukata don mu jimre. Ya ba mu Kalmarsa, da damar yin addu’a, da ’yan’uwanmu a ikilisiya, da littattafanmu da dai sauransu don su taimaka mana a lokacin da muke da bukata.
16. Me za mu yi idan muna so Jehobah ya ci gaba da ƙaunar mu da kuma kula da mu?
16 Muna godiya domin muna da Uba a sama da yake kula da mu! “A cikinsa zukatanmu suna farin ciki.” (Zab. 33:21) Ta wajen yin amfani da dukan abubuwan da Jehobah ya tanadar mana, za mu nuna masa cewa muna godiya don yadda yake ƙaunar mu da kuma kula da mu. Amma akwai abubuwa da muke bukatar mu yi don Jehobah ya ci gaba da kula da mu. Idan muka ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu mu bi umurninsa kuma muka yi abin da ya dace a gabansa, zai kula da mu har abada!—1 Bit. 3:12.
WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina
a Muna bukatar taimakon Jehobah don mu iya jimre matsalolin da muke fuskanta a yau. Wannan talifin zai tuna mana cewa Jehobah yana lura da mutanensa. Yana ganin matsalolin da kowannenmu yake fuskanta kuma yana taimaka mana mu shawo kansu.
b An canja wasu sunayen.