DARASI NA 11
Ka Yi Magana da Kuzari
Romawa 12:11
ABIN DA ZA KA YI: Ka ƙarfafa masu sauraronka ta wurin yin magana da himma.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
Ka fahimci batun da kyau. A lokacin da kake shiri, ka yi tunani sosai a kan muhimmancin saƙon. Ka san batun sosai domin ka iya bayyana shi daga zuciyarka.
Ka yi tunani a kan masu sauraronka. Ka yi tunani a kan yadda masu sauraro za su amfana daga abin da za ka karanta ko kuma koyar. Ka yi tunani a kan hanyoyin da za ka gabatar da saƙon da kyau don masu sauraronka su amfana.
Ka sa jawabin ya yi daɗi. Ka yi magana da himma. Motsin hannayenka, da yanayin fuskarka su nuna yadda kake ji game da batun da kake tattaunawa.